Na Maka Nisa Hausa Novel Complete
*NA MAKA NISA*
Story & writing
By
*Zara Muhammad sunusi
(Ummu HEEBBAT)*
Bismillah…….
Pg 1&2
*Barno State*
————— plsss mom ke daya ce zaki taimake ni cikin wanna halin dana ke ciki, wallahi bazan iya rayuwa idan ban same ta ba ! Abdulhakeem ke nan cikakken namiji kuma matashi wayayye mai isa da kyau da a sali da arziÆ™i!
Dogon namiji ne mai haiba fari mai dogon hanci fararan idonsa kaÉ—ai abin kallo ne baya da jiki sosai sannan bai da rashin jiki haka dai yake tsaka-tsaki.
Juyowa mum tayi ta dube shi ”My son dan Allah sai yaushe zaka dawo nutsuwar ka ne ! Abdul Hakim dan Allah me sa kake neman jazamin ne,
Idan daddy yaji wannan maganar kasan makomar zancen amma bazaka dai na faÉ—a ba .”
Bahaushiya Hausa Novel Complete
”Mommy wallahi Ina cikin tashin hankali ban san ya zanyi da soyyayyar nan ba, ban san sanda hakan take faruwa dani ba ina ma ace zan manta komai da na huta, Amma kashh! Sai dai na kasa kullum cikin Æ™unci na ke bacci na kasa samun nutsuwa daga lokacin zuwa yanzu,. Amma dan Allah mommy ki tayani addu’a akan wanna lamarin.”
”Abdulhakim taya zan taya ka addu’a akan wanna lamarin naka bayan kuwa baya da gurbi ko a Addini ! ”
”Dan Allah mommy ki ta yani domin bakinsa me Allah ya boye ba .”
”Shikenan tashi kaje ka yi wanka ka karya zan taya ka.”
“Na gode sosai mommy, ya faÉ—a yana miÆ™ewa gaba daya bashi da kwarin guiwa.
Bayan shigar sa mommy tayi shiru tana nazarin lamarin sa ita fa da abdulhakim ba ita ta haife shi ba zata ce baya da cikakken hankali, Domin abinda yake ya sabawa hankali kuma baya fahimtar lamarin ba gaskiya ciki.
Nasmat! Nasmat! ” Na’am honey gani nan zuwa yanzu .
Ko da ta fito hannunta rike da jakar zuwa ofishin aiki ta kalle shi cikin farin ciki ta mika mishi ”My Honey Allah yasa dai yau ka samu ka gama komai da wuri dan bana son jima warka sosai wallahi gidan baya min daÉ—i idan baka nan, gashi su azeeza basa nan suna gidan hajiya.”
Kallon ta yake har cikin ransa yake alfaharin samunta macen auren sa!
”Humm babyna na fiki san zama dake wallahi domin kedin ta daban ce amma dole na fita domin hakan shine cikar na miji ”
”Haka ne Mijina Allah ya dawo min da kai lafiya”
Ameeen ya ce tare da rungumar ta cikin jikinsa yabata wani hoot kiss a kumatu ya juya ya fita cikin falon ta na binsa bakin mota domin ta ga tafiyar sa, bayan fitar sa ne ta dawo falo ta fara nazari kan halin da take fuskanta gurin dan uwanta!
Nasmat mace ce wacce ake kira karshe cikin mata wanda dukkan namijin da ya same ta tom ya gode wa Allah, domin yayi dacen mace ta kowanne fanni oll hakan kuwa shine ya ke kara rura wutar matsalar da take ciki.
Bayan kwana biyu nasmat ta shirya domin zuwa gida wato men hause ɗin su na family wanda yake dauke da dukkan kakanni su na uba da kuma iyayen su har ma da wasu daga cikin ƙanne mahaifin ta.
Shigar ta ke nan ta tarar da mommy bata nan dan haka ta shiga dakin ta domin ta duba ko ta na ciki, cibuss tayi da mutum tana shiga yana rufe mata ƙofar dakin .
Cikin haÉ—e fuska ta dube shi ! ”Malam me ye haka ka bude min kofa na fita me yakawo ka ma dakin uwata .”
”Abin da ya kawo ki shi ya kawo Ni yafaÉ—a cikin murmushi ya dube ta yana kashe mata ido cikin kwanciyar hankali.
”Humm dan Allah habbity sai yaushe zaki gane gaskiyar maganar da nake faÉ—a miki ! Sau nawa zan sanar miki cewa nine mijin ki tun farkon rayuwar ki ba wancen ban zan ba! Amma kin tsaya bata wa kanki lokaci”
Wani irin a bune ya daki zuciyar nasmat domin kuwa koya ta ke dakai kar ka zagi mijinta a nan zaka ga É“acib ranta.
”Karka sake saka mijina a cikin jahilci irin na ka domin shidin ba irin ka bane yana da hankali kuma yasan me yake dan haka kafita harka ta abdulhakim wallahi abinka ya fara isata!!”
Murmushi yayi ya fara tunkaro inda take matsawa take baya amma binta yake ” Kana da hankali kuwa abdulhakim! Fa É—a min za ka yi wa…… Bata Æ™ara sa ba taji ya kai hannu sa kan kafadar ta, ya sanya dayan zuwa bayanta yana shirin rungume ta.
Ido ta zaro ta dube shi ”Anya kana da hankali kuwa ta faÉ—a tana ban gaje shi amma bai cika ta ba .
Sunkuyar da kansa yayi ya É—ago ya dube ta ”Nasmattttt dan Allah me kika gani cikin idona ?”
”Ban saniba abdulhakim wallahi zan yimaka ihu kowa yazo Allah kuwa ”
Dariya sosai yake yi ”Au ihu ko? Bari na Miki abinda zaki yi ihun idan yaso sai a zo domin daman hakan nake so ya faÉ—a yana kai bakin sa saitin nata.
Daga bakin kofar ya ji ance wallahi kana mata wani abu sai na maka rashin mutunci agidanan ! Abdulhakim
Chak ya tsaya bai cika ta ba kuma bai bar gun ba .
Wani ajjiyar zuciya nasmat ta sauke Tura kofar mommy tayi ta ji shiru ”Wallahi abdulhakim idan baka bude kofar nan ba zan É“ata maka rai.”
Jin muryar mommy tuni jikin sa ya fara rawa ya cika ta ya koma gefe ya na sauke numfashi. Nasmat na ganin ya koma gefe ta nufi kofar ta bude ta faÉ—a jikin mommy ta fashe da kuka .
”Yi hakuri auntyn yara zan sabar masa, Ummy ba ta nan tafita amma yanzu zata dawo ina sama naga zuwan ki kuma na tambaya ina abdulhakim yake aka ce yana nan part É—in shiyasa na zo domin nasan sai ya Miki wani abu ! Ashe kuwa hakan ya ke, kiyi hakuri muje ki gaida kaka kai kuma wallahi zaka dawo ka same ni .
Ta faÉ—a ta na hararsa.
Da haka suka wuce É—akin kaka nan suka tarar da ummy ta dawo
”Mommyn nasmat keda diyarki ne yaushe tazo gidan?” inji kaka ta faÉ—a tana hararar nasmat na wasa .
”Wallahi kuwa yaayin ni da ita ne yanzu ta shigo ta na duba uwar abdulhakim ne bata ganta ba .
Sai sannan ummy ta juyo ta dube su ”Gata ga ke mezan mata nikuma .
”Humm shike nan kuma baza’a gaida kiba?”
”Murmushi tayi ta kalle su ta maida kanta gefe bata sake cewa komai ba .
Nasmat kuwa gurin kaka ta wuce ta zauna ”Kakka na bari na ja miki kafar ta ware tunda ke kullum baki da aiki sai zama.”
”Kyasan ta ai idan ban zauna ba me zanyi kuma bayan ba komai na ke ba agidan iyayen ki sun gama min komai. ”Hakane kakka amma ai sai kina motsa jiki zaifi”
”Sannu! likita yaron chan ma dan iyayi ya barni wai shi É—an gayu harda wani kakka ya kamata kina hawa mahin ko me ne ne É—in sa dai ohhho”
Dariya dukkan su su ke yi banda nasmat da ta ji sunan ma sai da ranta ya É“aci, kakka ta dube ta
“nasmit me yake tsaka ninki da yaron nan?Kullum da ance yayyan yara sai ki yi ta faman hada rai”
Sake bata rai tayi ”kakka babu komai nikam yaushe ma muka hadu dazan bata rai a kan sa.”
”Shike nan ai ku kuka sani ”
Tana rufe baki sai ga abdulhakim ya shigo ya samu guri ya zauna.
”Kakkana hutawa ki ke yi?”
”Ehh fa yayya a she kana gida .
”Wallahi fa ya faÉ—a yana kallon nasmat da ke zaune, duk abinda suke kakka na kallon su, nasmat ta ta shi ta ce “Bari na je na huta a part É—inki ko kina da aiki ne mommy.”
”A’a auntyn yara bani da, kihuta abin ki zainab ma yanzu zata dawo ”
”Ok Tom tafada tana ficewa a falon .
Shikuwa abdulhakim saukowa yayi kasa kusa da ummy ya zauna yana daura kansa bisa cinyar ta .
”Ummy na tun dazun na ke neman ki a she kinzo gurin tsohuwa”
Wallahi gani na zo gaida kakka ne daga anguwa na dawo tafada tana shafa kansa .
Mommy ta kalle shi ta galla masa harara.
Kakka ta kalle shi ”Ni kuwa yayya mai kayi wa mommy da nasmit ne .”
Dariya sosai yake yi har da kusan Æ™wa ruwar sa ya ce ”Yanzu kaka kullum bazaki iya cewa nasmat ba sai nasmit… ”
”Ehh haka na iya bazan ce ba É—in dan haka bani waje ina neman maka sulhu ka na min tsiya .”
”Yauwa daman haka nake so ya faÉ—a yana miÆ™ewa tsaye ummy tashi mutafi part É—inki daman ke nake son muyi magana .”
”Tom yayya muje damn yanzu Nima nake shirin koma wa.”
”Kufu ruwa gudu daman ban ne me ka ba .”
Ummy dai bata ce komai ba tayi murmushi ta mike suka fita .
Watsewa suka yi a falon kakka, suka bar mommy ita da kakka, sai dai sam hira tsakanin su ba ta yiwuwa idan ba Ummu.
Nasmat zaune falon mommy tana chattyn da mijinta
Sai ga zainab ta shigo ”Aunty oyoyyo ta faÉ—a tana fadawa kan cinyar ta.”
”Washhh Allah na zeee zaki karya Ni ina kika je ne haka tun dazun”
”Aunty naje gidan su bintu ne muyi assignment yayyaa yace ba zai min ba da na san zaki zo da ban je ba ma.”
Ayya rashin sani ne ai ba damuwa yanzu dai kije kitchen kiyi min abinda na fiso kikawo min.”
”Kai aunty ke dai kina son kunun aya wallhi nima ki ko yamin shan sa mana.”
“Karki damu zeee zan koya miki bayan zuba . Ta fada tana maida hankalin ta kan waya domin tasan zee da hira ba tashi zatayi ba idan ta biye mata .
Ganin haka ne yasa itama zee ta wuce kitchen É—in .
Abdulhakim ya dubi ummy yayi kamar zayyi magana kuma ya fa sa.
”Mana be yi kenan yarona kasanar da Ni mana kasan dai nice zan baka shawara duk gidan nan ko.”
ÆŠagowa yayi ya dube ta ya sunkuyar da kansa ya ce ” Ummyyy naaaa wallahi ina cikin damuwa ne sosai wacce har ta kai na fara kasa jurewa.”
”Subhanallah amma kuma baka sanar min ba yanzu me yake damun ka? Sanar dani maza dawuri.”
Shuru yayi domin kuwa wallahi da kunya ya ce mata ga halin da ya ke ciki, duk da bai dau abin wata babbar matsala ba amma yana jin kunyar sanar da ita duk da kuwa cewa baya jin kunyar ta koda yau she .
Dan haka ka wai ya daure ya ce,
”Ummy na wallahi tunda na dawo daga Ingila nake fama da tashin hankali kan wata yarinya da nake so, amma kuma ita bata sona ban san ya zanyi ba ta soni.”
Cike da alhini Ummu ta dube shi ta ce,
”Wayyo yarona karka damu in sha Allahu wataran zata soka na sani kabata lokaci kadan kuma ka cigaba da nuna mata so. Nikuma zan taya ka addu’a in sha Allahu.”
”Tom ummy na na gode zanyi yadda kika ce din .”
Koda abdulhakim ya koma part É—in mommyn sa bai kula nasmat ba domin kuwa ta na zaune falo ita da zee bata dago kai ta kalle shi ba zee ce ta masa sannu ya wuce É—akin sa da ke cikin babban falon mommy .
Sai wajen biyar na yamma nasmat tayi musu sallama a kan cewa zata tafi gida domin abban su kaltum bazai samu damar daukar ta ba, amma kuma sai Kakka ta ce abdulhakim ya kai ta gida kar ta hau nafef tunda ba kowa gidan, Jin maganar da kakkaka tayi ya san ya gaban nasmat faduwa, domin kuwa ta san a binda zai faru, kuma idan tayi magana zasu fahimci wani abu, ita kuma bata son É“a ta tsakanin iyayen su domin tun suna yara kowa yake dakin uwar dan uwansa saboda amana irin ta iyayen su.
Haka ita ma mommy bata so ba amma idan tayi magana abin ba zai bada ma’a na ba dan haka shikuwa abdulhakim daga jin haka yaji wani sanyi domin wata dama ce yasamu sai dai bai nuna ba sai bata rai da yayi yace wa Kakka ”Kuma shi ke nan dan ta rai nani nine zan kaita gida ina shi mijin nata ”
Kakka ta dube shi ” Sannu sarkin san girma sai ka kaita É—in wuce kishiga ya kaiki .
Haka nasmat ta shiga badan ta soba ya shiga ya É—aga glass É—in motar dake É“aki ne ya kalle ta yayi murmushi ya kashe mata ido ” Gaki ga masoyin ki amma kina bata rai?”
Dauke kanta tayi gefe ta hade rai
Ta ce masa,
” Idan bazaka kaini ba na sauka na fada mata.”
”Rufa min asiri taya zan ki kai masoyiyar ta wa gida bayan kinsa bani da kamar ki nan duniya ! Kedai É—an saki fuskaar mana baby .
Bata ce da shi komai ba ya kama hanya suka fita ya kunna sautin kida na waÆ™ar salim smart da yake cewa “Allah ya ji Æ™aina idan har ba ke, wa’adin rayuwata ya zo Æ™arshe.” domin shine wakar da yafi ji .
Suna tafiya yana kallon ta yana murmushi yayin da ita kuma bata ko kallon sa domin tasan rashin mutun cin sa zuciyar ta fal fargaba, bata yi tsammani ba ta ga ya chan ja hanya, cikin tashin hankali ta ke kallonsa amma ko gezau bai fasa ba…….by Ummu HEEBBAT