Ad Code

Furar Danko Hausa Novel Complete

Furar Danko Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..

 

 

𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 1️⃣

 

 

 

*_UK (LONDON)_*

 

……..Kwance yake rai-rai a madaidaicin gadon nasa da mutanen Nigeria ke kira da 6-by-6. Sai dai wannan yaji katifa mai shegen laushi da bedsheet fari tas shima mai laushin gaske da ko’a ido ka kalla zaka shaida hakan. Yanda yake ɗan furzar da numfashi sama-sama da huttai ga zufa da tai ma jikinsa jagab zai tabbatar maka da ga training ya fito. Dan wandone na jc ƙarami da ya tsaya masa a fin rabin cinya da rigarsa. Sai takalma da aka san ƴan ƙwallo da su a ƙafarsa. Jikinsa ne a saman gadon ƙafafun zube a ƙasa. Iska mai nauyi ya sake furzarwa tare da buɗe idanunsa da launinsu ke a surke. Sam babu fara’a a tare da shi, dan fuskar nan ɗam take fiye da yanda kowa ya sanshi da rashin walwala acan baya….

Cikin kuzari da ke nuna cikakkiyar lafiyar gangar jiki ya tashi zaune da ƙyau, ƙaramin tsaki ya ja tare da yamutse fuska ya fara saɓule takalman ƙafar tasa. Anan ya zubesu tare da miƙewa gaba ɗayansa ya kama rigar jikinsa ya cire cikin kamar yanayin jin haushi ya jefar da rigar ƙasa. Dogon glass ɗin da ya kasance kamar bango guda a haɗaɗɗen bedroom ɗin nasa ya nufa. Ya kai hannu ya danna wani ɗan maɓalli green. A hankali glass ɗin ya shiga raba kansa biyu har ya bada ƙofa. Shiga yay nan ma kamar a ɗan fusace, lafiyayyen toilet ne ya bayyana da ni kaina na zama baƙauya a kallo, kai tsaye ƙarƙashin shower ya nufa ya sakarma kansa ruwa yana mai jan wata nannauyar ajiyar zuciya…

Halak Dina Hausa Novel Complete

*_Aliyu Mika’il Idris Mawashi_* kenan da ke amsa sunan _Smart Mawashi_ a duniyar ƙwallon ƙafa. Duk da dai kwata-kwata watanninsa uku kenan da dawowa ƙasar ta UK a London yay signing a club ɗin Queen City. Du da kasancewar ƙaramin club ne muna fatan ya zame masa wani tsanin kaiwa inda ba’ai zato ba. A yanzu Smart da muka sani na baya mai shiru-shiru da rashin sakewa da jama’a ya sake zarce hakan. Dan yanzu ba shiru-shiru ba, har miskilanci ma ya koyo. Hakan kuma ta faru ne a sakamakon faruwar shuɗaɗɗun abubuwan da suka faru a cikin watanni ukun nan da suka wuce. A gaɓar da tafi kowace gaɓa muhimmanci a tarihin rayuwarsa. A lokacin da ya gama shiryawa da tsarawa kansa gina rayuwa mai ban sha’awa da birgewa tare da matarsa. A lokacin da yay shirin ɗaukar dukkan yarda da amanar kansa data rayuwarsa domin damƙa mata. Sai labarin ya canja da ga yanda ya rubuta shi a zuciya zuwa rubutun ƙaddara.. Matarsa ta kufce masa a yayinda da burinsa na zama ɗaya da ga cikin ƴan ƙwallo a wata ƙasa ya cika. A hankali komai ya dinga dawo masa a zuciya dalla-dalla tamkar a yanzu ne yake faruwa. _(Bayan fitarsa gida a waccan ranar ya nufi gidansu cike da damuwar halin da ya jefa Lulu a ciki. Ya samu Asma’u taje aikan da Ammah tai mata gidan Aunty Bilkisu. Sai Maryam kawai da Ammah. Ko zaman kirki baiyi ba a daddafe suka gaisa da mahaifiyar tasa ya sanar mata yazo ɗaukar ɗaya daga cikin su Maryam ne dan Mawaddat babu lafiya. Hankalin Ammah ya tashi, ko neman Abba bata tsaya yi ba tace ya ɗauki Maryam suje idan Abban ya dawo zata sanar masa, dan ita a nata zaton ko ciki Lulun ta samu. Cikin sauri Maryam ta kimtsa tare da ɗibar kunun gyaɗar da sukayi domin tafiya da shi can su karya dan itama ko karyawar basu yi ba. Cikin ƙanƙanin lokaci suka iso kasancewar safiya ce babu yawan go slow a hanya. Sai dai me tun a yanayin da sukaga ƙofar falon a buɗe da littafin da ya gani ɗazu a saman gadon Lulu yashe a ƙofar shiga falon alamar an yarda bisa kuskure gabansa ya faɗi. Amma sai ya dake cikin ƙarfin hali suka shiga, a falo Maryam ta zauna shi kuma ya nufi bedroom ɗinsa yana faɗa mata taje ɗakin Lulun yana zuwa. Maryam ta amsa masa da to, yayinda shi kuma ya nufi ɗakin nasa. Bai wani jima ba sai gashi ya fito. Ɗan turus ya tsaya ganin Maryam kamar a ruɗe tana kai kawo. “K lafiya? Ba canai ki shigaba ina zuwa”. Da sauri Maryam ta juyo gareshi tana bashi amsa da “Yaya ai Auntyn bata nan ciki fa. Har toilet na leƙa babu kowa a ciki, hakama kitchen, sai dai duk an harmutsa wadrobe ɗinta an ɗiba kaya harma da akwati guda da aka bari kamar sauri ya hana a ɗauka”. Wani irin duka ƙirjinsa ya dinga yi, sai kuma ya nufi ɗakin da sauri shima. Kamar yanda Maryam ɗin ta sanar masa haka ya gani, sai dai shi nashi idon ya ƙara masa ganin duk wani abu mai amfani a ɗakin ma babu shi. Ƙafafunsa ne suka fara rawa, sai dai cikin dakewa ya cigaba da ƙarfafa kansa. Takardar da idonsa ya sauka kanta a bisa gado ya ƙarasa ya ɗauka. *_Na tsaneka Aliyu, bana son sake ganinka a rayuwata, amma kaje na barka da ALLAH azzalumi. Ashe wa’azin naka duk na yaudara ne kaima baka aiki da shi. Ka manta da ni har abada, dan ko’a hanya nai maka tazara irin ta sama da ƙasa, gabas da yamma. Idan ka wahal da kanka a nemana kai ka so, dan babu wanda ya isa sakani sake zama da kai koda Uncle Yousuf ne._* jiyay jiri na nan ɗibarsa yay saurin kaiwa zaune yana ambaton sunan ALLAH. Ya jima a wajen zaune kansa na yamutsa masa har Maryam ta gaji da jira ta shigo ɗakin. Hankalinta ya tashi da ganin yanda Yayan nasu ya birkice cikin ƙanƙanin lokaci. Kansa tai tana ƙwala masa kira amma sai ya ɗaga mata hannu da ƴar tsawa-tsawa yace ta fita ta bashi waje. Ta tsorata dan haka ta fita da sauri. Kamar an saita batafi minti ɗaya da fita falo cikin ɗaurewar kai ba sai ga kiran Ahmad ya shigo mata. Da sauri ta ɗaya ta kai kunneta. Ko gaisawar kirki bata tsaya sunyi ba ta shiga faɗa masa abinda ke faruwa. Gaban Ahmad ya shiga faɗuwa shima da ga can, cikin ƙanƙanin lokaci sai gashi a gidan. Tambayar duniya Smart yaƙi cemasa komai har sai da ya nuna fusata sanan a taƙaice ya ce masa, “Tabar gidan”. Duk da abin ya daki zuciyar Ahmad ɗin. Sai ya shiga kwantar masa da hankali akan yana zuwa ya tabbatar bazata wuce gida ta tafi ba. Wayar Uncle Yousuf yay kira, da ƙyar ya samu ta shiga. Bayan ya gaishesa bai wani tsaya kwana-kwana ba ya sanar masa halin da ake ciki. Hakan ya ɗan ɗimauta Uncle Yousuf ɗin shima amma sai ya yanke kiran yace yana zuwa. Gidansa ya fara kira Aunty Saliha dake tsaye itama cikin tashin hankali ta ɗaga wayar da sauri. Dan dama nemansa take tun ɗazun ta gagara samunsa. Kafin ma yay mata tasa tambayar ita ta jeho masa abinda ke bakinta. “Abban Ra’is wlhy akwai matsala babba. Yanzu nan Khadijah tai kirana akan na shirya naje gidan Mawaddat babu lafiya na lallasheta da kwantar mata da hankali, banyi ƙasa a gwiwa ba nai shiri dan na shiga tashin hankalin bayanin Khadijahn. Sai dai muna kan hanya sai ga text massege ɗin ta ya shigo wai karmu nemeta, dan tayi nesa damu, na faɗa maka a kira Aliyu ya bata sakinta ta arziƙi inba haka ba zata sashi ya bada ta wuya. Duk da saƙon ya bani mamaki nacema driver yay sauri mu tafi gidan nata. lokacin da muke shiga street ɗin mun haɗu da wata baƙar mota mai tinted glass suka wuce muka wuce. Mun samu gidan buɗe da wani makwafcinsu tsaye a bakin gate ɗin, driver na ƙoƙarin shiga ya dakatar da mu cewar aiko baijin gidan nan da kowa. Dan yanzu yaga wata mata ta rirriƙo matar gidan tana kuka sun shiga mota sannan a loda akwatina a Hilux ma, shima ganin sun bar gidan buɗe ne ya sashi fahimtar babu lafiya, shine fa naketa nemanka ka kira Aliyu koka turo min Number sa amma na kasa smaunka”. “Innalillahi wa-inna ilaihiraji’un” Uncle Yousuf ya shiga maimaitawa. Nan ɗin ma baice komai ba ya yanke kiran. Mommy ya kira, itama bai tsaya sun gaisa da ƙyau ba ya jeho mata tambayar ko Lulu taje gidan. Da mamaki tace bata zo ba gaskiya, kuma batajin zatazo ɗin, dan yau tanada Shari’a. Jin haka Uncle Yousuf ya ɗan samu nutsuwa ya yanke kiran. Ahmad yay kira yace su maza court dan tana can zai turo Aunty Saliha yanzu su riƙeta. Da sauri Ahmad ya miƙe, shima Smart sai ya miƙe. Har Maryam basu bariba suka kulle gidan. Sai dai me koda suka isa can ɗin ma babu Lulu, an kuma basu tabbacin bata zo ba. Sosai yanzu kuma hankalinsu ya fara tashi, dan kowa yasan duk rintsi fa Lulu akaran kanta bazatai sakaci da aikinta ba, musamman idan akai la’akari da yanda take matuƙar son al’amarin. Sai dai yanda aka ɗibi kaya yayin barinta gidan na hargitsa ma kowa lissafi. Gidan ƴan uwa da duk aka san zata iya nufa aka fara bubbuga waya, gidan Alhaji Garko ne farko, amma sai cikin tashin hankali Dada tace batazo ba, ba cikin Kano ba har wajen Kano amma dai amsa ɗaya ce Lulu fa bataje ba. Tun kowa na ɗaukar al’amarin wasa harya fara shan hankali, zuwa yamma dole aka shigar da report police station. ALLAH sarki Smart, yini guda baici komai ba sai ruwa, dolene a kallo ɗaya ya baka tausayi, sai da Coach ya tsaresa bayan sallar magrib yasha shayi, yana gamawa kuma sai amai, sai zazzaɓi mai zafi. Dole ranar Ahmad da Abdull na gidansu sai anan suka kwana, dan suma dai tuni sun san mike faruwa Ammah duk kawaicinta a ranar sai da ta taka gidan Smart da ga ita har Abbah. Umma kam wani shegen daɗi takeji, dan a ganin ta in har wani abu ya samu Lulu iyayenta sai sun ɗaure Smart na tsawon rayuwa.

Al’amarin kamar wasa tuni ƙaramar magana ta zama babba, dan kwana ɗai-ɗai har uku babu labarin Lulu Daddy da Uncle Yousuf tuni sun wancalakar da ayyukan gabansu sun dawo Nigeria. Hakama su twins duk suna Kano. Smart yay wata irin zabgewa, bawan ALLAHn ko murmushi baka gani a fuskarsa, ya duƙufa kawai gayama UBANGIJI, dama Abba ya kai islamiyya da masallatai a taya addu’a, hakama ƴan sanda nata faman kai kawo da bincike. A cikon kwana na biyar ne fa Addu’a bata faɗuwa ƙasa a banza sai ga binciken ƴan sanda ya fara maida akalarsa kan Dada, ba komai ya kawo hakan ba kuwa sai dalilin ganin sanda aka fita da Lulu da maƙwaftansu yayi, dan ƴan sanda basu barshi ya hutaba shima. Yana ganin Dada yace ma ƴan sanda “A’a to ai wannan Maman ce na gani da yarinyar a waccan ranar, tare da wani saurayi haka mai ɗan kammani da su”. A take kowa ya dubi Dada da duk ta daburce, sai kuma ta hau borin kunya. Ran kowa a wajen sai da ya ɓaci idan ka cire Alh. Sulaiman da Tajuddeen da suka san komai. Smart kam wani irin kallo yakema Dada kawai, ji yake yau da ace bata da alaƙa da Lulu wlhy duk da tsufanta sai ya koyama matarnan hankali, dan sai ta tabbatar da ainahin Aliyu Hydar. Daddy ma dai da duk ya zabge a tsaye harda ciwo akan ɓatan Lulun a wani irin rikice yake kallon Dada da Alh. Sulaiman a karo na farko, shikam dama ya zargi Alh. Sulaiman, sai dai Uncle Yousuf ya kwaɓesa akan hakan. ALLAH sarki Uncle Yousuf sarkin dattako, da ya fahimci faɗan na cikin gidane sai ya sallami ƴan sandan kawai, da ƙyar suka tafi dan sun ce dolene Dada ta fuskanci shari’a. To abinka da manyan mutane, a take akai kiran cp ya basu umarnin tafiya. Bayan wucewarsu ne fa gida ya hargitse, dan Dada tace bazata taɓa faɗar ina Lulu take ba sai Smart ya saketa. Karan farko da tun faruwar al’amarin ya saki wani shegen murmushi mai ƙona zuciya a baɗini mai kuma hasala abokin gaba a zahiri……..✍️

 

 

_Alhamdullah barkanmu da sake dawowa a book 2. Yanda muka fara a Sa’a ALLAH yasa mu kammala da nasarori. Ina godiya da jirana da kukayi tare da fatan alkairi

 

 

 

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

 

*KINSAN SUNAN LABARAN?,…..GASU KAMAR HAKA*

 

FURAR DANKO

Billyn Abdul

 

-ZAFIN KAI

Mamuhgee

 

-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma

 

-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo

 

Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400

 

Pay at👇

 

1487616276

Access Bank

Bilkisa Ibrahim Musa

Sai katura shedar biyanka anan👇

 

09032345899

 

Idan katin waya ne kuma saika tura anan

09033181070

 

 

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

 

*THANKS FOR CHOOSING US*

 

Zafafa🫶🔥

 

 

 

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu

 

 

 

 

 

🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

 

 

 

 

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️

 

 

 

……..Iyayensa ya kalla cikin nutsuwar data ratsashi a yanzu najin tabbacin ina matar tasa yake, cike da girmamawa ya ce, “Abba ku tashi muje gida kawai”. Abba da tausayin ɗan nasa ya ƙara mamaye masa zuciya ya ce, “Aliy ba tafiya gida ne masalaha ba, ka bari dai a sasanta muji miye dalilin aikata hakan”. “Abba bata da wani dalili face na son zuciya. Ina son cigaba da ganin girmanta a matsayinta na uwa kamar yanda kuka tarbiyantar dani girmama kowace irin furfura, tun farko ma ita ya kamata na zarga, amma banyi hakan ba saboda shi zargi bashi da amfani. Sai dai amsa ɗaya zan bada a yanzu har gaban Abada *_BAZAN SAKI MAWADDAT BA_*. Sai dai ayi ɗayan biyu. Ko na MUTU tamun TAKABA, ko ni na mata wanka na sallaceta zuwa kabarinta. Wannan dalilan guda biyu ne kawai zasu iya raba wannan auren da izinin ALLAH!!”. Ba su Dada ba hatta Abbah da Ammah sai da Smart ya girgizasu, dan magana yake a dake, a fusace, a kuma kausashe, hatta da Ahmad dake a matsayin aboki zai iya rantsewa bai taɓa sanin Smart ɗin yanada irin wannan zafin ba. Harara Dada ta watsa masa da faɗin, “Oh burinka kenan dama ta mutu kaci gadon dukiya. Sheɗani to ALLAH ya fika, sakin Mawaddat kuwa idan bakai ta arziƙi ba zakayi ta wuya dan bazamu taɓa haɗa zuria da jinin tsiya jinin talauci ba. dama koda ka aureta ai asiri kai ma iyayen nata matsiyaci”. Murmushi Smart ya saki da taɓe bakinsa cikin halin ko’in kula da zancen Dada. Sai ma ƙoƙarin barin falon da yake yi batare da ya bata amsa ba . Alh. Sulaiman da ya kai maƙura a kan Smart ɗinne ya miƙe a fusace yana nunashi da yatsa. Sai dai kafin ma yace wani abu Smart ya nunashi shima cikin gargaɗi, “Kai! Karka kuskura shiga ramin da zai bizne rayuwarka ta har abada ya barka da gangar jiki kawai da idanun kallo. Sunanka ƙanin uwa ne ba uba ko ƙanin uba ba. Ni da kake gani na nan Sulaiman na fika fiye da abinda ka iya wlhy. Idan kace zaka saka ƙafar wasa da ni sai na gigita rayuwarka ta yanda kai a karan kanka bazaka taɓa morarta ba balle waninka. Magana ake ta mutane ba irinku riɓɓaɓu ba okay…” da ga haka Smart ya sa kai yay ficewarsa kafin ma Alh. Sulaiman da jikinsa ke rawar ɓacin rai dana firgita ya iya furta komai, da gaskiyar Lulu idanun Smart sun cancanci kowane irin suna, musamman a yau da ransa ke a ɓace dan Alh Sulaiman idanun Smart na ɗaya da ga cikin abinda ya razana shi. Fitar Smart ɗin ta saka falon zama tsit, yayinda Alh. Sulaiman ke nuna ƙofa cikin rawar baki data hannu. Daddy ya sauke wata irin gajiyayyar ajiyar zuciya a karo na farko, sai kawai yaji hawaye sun cika masa ido, dan tunda Smart ya fara magana yake kallonsa harya fice. Uncle Yousuf ne ya tashi yabi bayan Smart, haka ma Ammah da Abbah. A gate suka sami Smart yana waya da Coach, dan a gobe ya kamata ya wuce dama, sai dai da yayi aniyar haƙura dan bazai iya tafiya wata ƙasa batare da anga Lulu ba. Amma a yanzu ya gama yanke shawarar wucewa babu fashi. Uncle Yousuf da ke kallonsa da murmushi yay masa nuni ya shiga mota inda Abba da Ammah suke, bai musa ba ya shiga. Har gida Uncle Yousuf ya kaisu, inda ya samu zama na musamman da Abba da Ammah. Shi ya lallashesu akan su kwantar da hankalinsu dan ALLAH a zubama su Dada ido aga gudun ruwansu, dan ya tabbatar sun aikata haka ne dan Alhaji Garko baya nan. Sosai Abbah ya gamsu da bayanin Uncle Yousuf ɗari bisa ɗari tare da ganin shawarar itace dai-dai. Bayan wucewar Uncle Yousuf Abba da Ammah suka sake zaunar da Smart sukai masa nasihar ya cigaba da shirinsa na tafiya kawai kamar yanda Uncle Yousuf ya faɗa da masa faɗan abinda yay ma Alh. Sulaiman da Dada. Haƙuri ya basu da alƙawarin bazai sake ba. Wannan shine sanadin tattara al’amarin Lulu ya haɗa kayansa a washe gari shi da Uncle Yousuf da Coach suka nufo ƙasar UK a London. Inda yay signing da wani ƙaramin team Queen City. Su Uncle Yousuf sun sake masa nasiha akan ya kwantar da hankalinsa kan al’amarin da kanta zata bijirema su Dada. Shi dai cikin dauriya da dakiya yake amsa musu da to kawai. Amma a cikin ransa shi kaɗai yasan irin ƙunar da yake ji da matuƙar kewar matarsa. Sai dai ƴan mazan sun ɗauki aniyar da jarumtar a wannan karon na sai ya tabbatar ma family ɗin Lulu gaba ɗaya da ita kanta shi ɗan halak ne, sannan talauci ba hauka bane ba. Duk da dai yanayin yaso taɓa shi da son maidashi sanyi-sanyi a watanni ukun daya samu kansa, sannan sam yanzu baka ganin fara’a a fuskar Smart, ya sake zama shiru-shiru a yanzu ma harda miskilanci zamu iya cewa ya ƙaro. Dan bai shiga sabgar kowa, abinda ya kawosa kawai yake yi sai bautar ALLAH. Baya zuwa ko ina da ga gida sai idan yana buƙatar sayen wani abu ya ɗan fita ya sayo ya dawo sai wajen training ɗinsu. Burinsa shine ya manta da komai kamar yanda Uncle Yousuf a koda yaushe ke bashi shawara, dan har yanzu Dada taƙi faɗin inda ta kai Lulu. Duk da yanda aka so yin ɓatacciya tsakanin Daddy da Alh. Sulaiman, dan Daddy yana ragama Dada kodan darajar sunan uwa, amma tunda ya fahimci da haɗin bakin Alh. Sulaiman akai komai sai hankalinsa yay masifar tashi, yasa a nemo masa Smart, Uncle Yousuf da ke nuna shi al’amarin bai damesa ba a zahirin dan yana son Daddy ya maganantu a wannan karon yace masa ai baya ƙasar. Zancen ya girgiza Daddy duk da bai san ina Smart ɗin yaje ba ko abinda ya tafi yi. Da ga baya ma sai Dada ta tattara ta bar ƙasar itama zuwa jiyyar mijinta….)

 

Wannan shine abinda ya faru kafin tahowar Smart England.

 

Ɗaure da guntun towel ya fito a ƙugu, sai ƙarami yana tsane jikinsa da sumarsa da ya jiƙe da ruwa. Mai ya shafa sama-sama tare da shiryawa ciki ƙaramin wando da riga armless. Gadon nasa ya sake hayewa yay kwanciyarsa dan barci yake ji sosai. Sai dai kafin barcin ya ɗaukesa tunani ya jasa tsahon lokaci….

 

Wannan kenan.

 

 

*_CANADA_*

 

Amai take sosai cikin galabaita da fitar hayyaci, a kallo ɗaya zaka fahimci yanda duk jikinta ya saki sai huttai take da ƙyar. Cikin tausayawa mai aikin da suka taho tare tun daga Nigeria ta ke jera mata sannu. Bayan ta gama aman ruwa ta sakarma kanta daga inda take zaune tana hawaye. Haka take tun can da ma bata da juriyar ciwo, a yanzu kuma da take jin ciwon tamkar ya bambanta da duk wanda ta sabayi ne ke sake galabaitar da ita da raunana mata zuciya, har tana jin anya bazata bijirema kakar tata ba ta bayyana kanta kota koma gida Nigeria. Tsahon watanni uku kenan da barowarta gida Nigeria bisa taimakon kakarta Dada. _(Dan a waccan ranar bayan fitar Smart da ga gidan ta fito toilet da taje yin fitsari, duk da tai masa kurarin barin gidan ba’a ranar tai niyyar hakan ba, sannan batai niyyar sanarma wani nata abinda yay matan ba kamar yanda aunty Khadijah ta bata shawara. Saman gado ta koma ta ɗauki book nata da take adana muhimman sirrikanta ta fara rubutu tana hawaye, bata kai ƙarshe ba ya cika dan haka ta buɗe sabo ta cigaba. Tana tsaka da rubutun ne taji sallamar Dada a bazata, kafin ma ta farga har ta shigo bedroom ɗin nata kai tsaye. Hawayen da Dada ta gani a fuskarta ya sata nuna tashin hankali da fara jera mata tambaya, sai taji zuciyarta ta ƙara karaya ta sakarma Dadan kuka kawai. Komai Dada bata tsaya tambayarta ba ta hau haɗa mata kaya, bayan ta kammala drivern da ya kawota ya shigo har ciki ya dinga kwasar kayan, yana kammalawa ita kuma ta ce Lulu ta tashi suje, da farko Lulu taso tirjewa akan ta bari Aliyu ya dawo, amma Dada ta balbale ta da masifa. Dole badan taso ba tabi umarninta ta sako. Sai dai tanayin taku biyu uku Dada ta rabga uban salati da antayo ashariya mai kawuna bakwai ta dire. Balbale Lulu tai da masifa irin wadda bata taɓa mata ba, tare da tambayoyi masu tsaurin gaske da suka saka Lulun ɗan jin nauyi harta gagara cewa komai. Sai da taga ta takura mata tace faɗuwa tayi. Hakan ya ƙara harzuƙa Dada ta fisgeta suka fita, sai dai zafin da take ɗan ji ya sata tirjewa dole Dada ta kamata suka fita cikin lallaɓawa. Anan ne makwafcinsu ya gansu, sai dai ita Lulu bama tasan maƙwafcin nasu bane ba. Lulu ta roƙi Dada suje Court akan case ɗin yarinyar nan da take so a ƙarƙare a yau, inda suka samu alƙali suka juye masa kuɗaɗe akan ya cigaba da riƙe mata mutumin a gidan yari zata bar ƙasar dan bata da lafiya. Da ga court hanyar airport suka ɗauka, suna isa basufi minti arba’in da biyar ba jirgin zuwa Abuja ya shirya tashi, dama Dada tasa a tanada mata ticket tun barowarsu gida. Ita kaɗai ta wuce Abuja Dada ta koma gida. Maimakon gidan Uncle ɗinta Khamil wata mata ce tazo ta tareta, tasan matar tare da Dada da daɗewa, suna kiranta Hajiya Shuwa. A ranar gaba ɗaya ta yini kwance ne da zazzaɓi a gidan Hajiya Shuwa, hakama washe gari dai duk gata nan ne dai babu isashen lafiya tare da ita. A kwana na uku Dada tai kiranta a waya ta tsara mata zance cewar ai Aliyu na nan nata zaginta da cewar wai ta tafi yawon banza ne, dan haka sun saka ƴan sanda sun kamashi a yanzu haka ma kotu zasu kaisa ya bata takardar sakinta. Ran Lulu ya ɓaci matuƙa dajin wai Smart na zaginta har da dangantata da karuwa, dan haka tacema Dada tana son ƴan sandan nan su ƙara wajiga rayuwasa kuma ya saketa. Kwana biyu bayannan da ke zama biyar da barowarta Dada ta kirata nan ma ta sanar mata Aliyu wai ya saketa. Duk da abinda take fata ke nan sai taji wani iri, daga ƙarshe ma ranar yini tai babu lafiya zuciyarta a cunkushe. A ranar ta sanarma Dada tana so tabar Nigeria zuwa America, amma sai Dadan ta bata shawarar taje gidanta na Canada tunda babu wanda yasan da shi, dan Uncle Yousuf yay ikirarin ɗaukarta da kansa ya maida gidan Aliyu ko tana suma tana mutuwa ne. Ran Lulu ya sake ɓaci, ta kuma sake jin ƙwarin gwiwar nisantar ahalinta baki ɗaya. Wannan shine dalilin tahowarta Canada tare da mai aikin da aka haɗota da ita mai suna Ummita. Sai dai tunda sukazo zuciyarta taƙi nutsuwa waje ɗaya, abubuwa da yawa tsakaninta da Smart a ɗan zamansu sun zame mata barazana a barci da ido biyu, wannan ya sata sake buɗe babin shaye-shayen ta sosai-sosai. Ko abinci bai dameta ba da ga shaye-shaye sai barci. A kwanakin da bazasu wuce sati biyun nan ba ne abubuwa suka fara canjawa, idan tasha kayan shaye-shayen ta tana kammalawa zatai amansu, tun tana ɗaukar al’amarin wasa har takai bata son warin kowane irin ƙwayar magani, amma cikin ƙarfin hali take daurewa ta sake gwada sha, ta kuma sake aman nasu. Wannan dalilin ya sata ɗaga ƙafa kwana biyu, sai kuma hankalinta ya fara dawowa jikinta har salla da lokaci yayi kamar wadda aka zabura sai ta tashi tayi. Kwana uku da suka wuce kuma sai zazzaɓi ciwon kai da kasala, ga yawan mafarkin Aliyu kamar wani magic a gareta. Sai duk randa tai mafarkin nashi takan tashi da ɓacin rai har taji buƙatar shan kayanta ko zata manta da shi. Sai kuma dai ta daure taƙi sha dan ko tunawa tai da su sai taji amai. Yau kuwa wayar gari tai cikin wata irin damuwa da kewar wani abu data kasa canka a ranta, sai zuciyarta daketa faman ƙuntata, cikin son kauda yanayin ne ta samu ƙwaya tasha amma ta rantse bata zama a cikinta shine take amayar da ita a yanzu).

 

Wannan kenan.

Close Menu