Yan Ubanci Hausa Novel Complete
Ƴ’AN UBANCI
NA
MAMAN AFRAH
FCW
RENEW
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM.
Godiya da ya yabo sun tabbata ga Allah madaukaki, tsira da aminci su tabbata ga Annabin rahma (S. A. W).
page 1️⃣
Malam Buba mai almajirai malami ne da yake koyar da almajirai a k’auyen kukayasku dake Maigatari L.G a Jihar Jigawa, Malami ne da ya yi suna ya shahara sosai a cikin Æ™auyen na Kukayasku da ma wasu k’auyukan da ke mak’otaka da kukayasku, kai har ma da rugage da ke kusa da nesa kai har ma daga kauyukan Niger irinsu garin isa,Dogo dogo, Shakunu da dai sauransu. Duk da cewa su ma k’auyukan na da mayan malamai amma shahara da kuma tsayuwa tsayin daka na malam Buba ya sa su ke kai masa yara almajirci. Malam Buba yana da matan aure guda biyu uwar gidansa itace Ishalle sai kuma amarya mai suna Alawiyya, y’arsa d’aya a duniya mai suna Nana y’ar gidan Ishalle ce dan ita amaryar Allah bai ba ta haihuwa ba. Suna zaune lafiya da iyalansa kuma yana kula da su kamar yadda ya kamata. A kwana a tashi sai matarsa amaryar ta nemi ya sawwak’e mata sabo da tana so ta je wani wurin ta yi aure ko Allah zai bata rabon haihuwar, haka Malam Buba ya saki Alawiyya ba dan ransa ya so ba sai dan kar ya shiga hak’k’inta domin idan bai amince ba kamar ya tauyeta ne tun da tana ganin kamar rashin haihuwar daga gareshi ne , dan tun da ya haifi y’a d’aya , shiru ka ke ji. Yanzu yarinyar zata kai shekara takwas. Duk da ya nu na mata duk a in da ta ke sai Allah ya nufe ta da samun haihuwar tukunna zata haihu amma haka ta matsa ya sawwak’e mata ta je ta yi wani auren. Bayan shekara d’aya Malam ya sake auro wata matar mai suna Kande, bazaware ce aurenta uku amma bata tab’a haihuwa ba.Kande wata masifaffiyar mata ce wacce tsabar fad’anta ya sa mazan ke sakinta, Malam Buba bai yi wani bincike ba akan ta sabo da ta nuna masa ita mace ce mai ladabi da sanin ya kamata, wanda a zahiri kuma ba haka bane kawai buge ne.
Yan Mata Return Hausa Novel Complete
Bayan Kanden ta tare da farko zama kamar abin arzik’i, sai daga baya ta fito da halinta na asali daman an ce mai hali baya canjawa.Rashin mutunci kala-kala Kande ta tsiro da shi wanda hakan ya matuk’ar sanya Ishalle a damuwa domin kullum ba su da zama lafiya kai hatta da Malam da almajiransa basu tsira ba daga rashin mutuncin Kande. Haka zaman ya cigaba da kasancewa babu dad’i babu dad’ad’awa, sam Malam Buba ya gaji da fitinun Kande gashi ba yadda son ya sake ta gudun kada mutane su d’aukeshi mutum mai auri saki. A kwana a tashi haka rayuwa ta kasance gaba d’aya gidan ta zamewa Ishalle kamar wani kurkuku gashi ko Nana bata son zama a gidan sai dai ta je mak’otansi, har abin ya kai Ishalle ta daina zama a tsakar gida sai dai a d’aki in ba wani Abu za ta yi ta bata ko k’aunar fitowa tsakar gidan da sunan ta zauna tasha iska. Malam ma sabo da masifar Kande sai da zaman gidan ya zame masa kamar kufai.
Bayan shekara d’aya matan na Malam dukansu Allah ya azurta su da samun ciki, Malam ya yi murna sosai dama samun wannan k’aruwa duk da hali irin masu Kande amma hakan bai sa ya ji ba dad’i a ransa ba damuwa samun cikin Kanden sai addu, a da yake Allah sauke su lafiya. Kande kam ta yi matuk’ar bak’inciki ciki da Ishalle ta samu ciki domin so take ta samu ita kad’ai dan ta yi ta haihuwa sabo da gadon dan Malam Buba akwai gonaki da shanaye d’a sauran Dabobi wannan dalilin ne ya sa mazan Kande ta amince da aurensa ba wai dan kasancewarsa Malam ba ita wannan ba damuwarta bace. Tun da cikin na su ya tsufa Kande ta dinga bin malamai da bokaye tana so ta salwantar da abin da ke cikin Ishalle, dama tun yana k’arami take ta son a zubawa Ishalle amma hakan ya gagara.cikin yawon Malaman nata ne ta had’u d’a wani boka wanda ya yi mata wani asiri ta biyashi mak’udan kudad’e dan ya gaya mata mai zai faru, haka ta dawo gida da farinciki.A haka har ita Kanden ta haifi d’iyarta mace duk da ta so haihuwa namijin domin gadonsa ya fi yawa, ranar suna aka sanyawa yarinya Ikilima. Bayan sati uku da haihuwarta itama Ishalle ta fara nak’uda, tun tana yi d’auke k’arfinta har dai ta galabaita, ita kuma kande tana d’akinta tana dariyar k’eta.Malam Buba kuma yana d’akinsa ya hau buzu yana ta addu, a Allah sauketa lafiya. Gozomar da zata karb’i haihuwar ce take ta mata sannu a haka har dai haihuwar ta zo gadan -gadan, amma me dai -dai fitowar kan d’a me gozoma zata gani wani k’atoton kan miciji ne ya kawo kai, Dan sauri Gozomar ta ja da baya tana salati ita kuma Ishalle wahala ta isheta bata ma san meke faruwa ba. Kafin me miciji yana fitowa zilululu tsayinsa ya kasa k’arewa ai da gudu Gozomar ta fito daga d’akin ta nufi turakar Malam Buba hankali a mugun tashe, haka ta kira Malam Buba ya fito da sauri ya nufi d’akin Ishalle hankali a tashe dan ya d’auka ma Ishallen ta mutu ne dan gozomar d’akin kawai ta ke nunawa ta kasa masa bayani tsabagen rud’ewar da ta yi. Malam Buba na shiga d’akin idanunsa ya sauka akan wani dank’areran bak’in maciji a gaban Ishalle da take a mugun tsorace ta takure a wuri d’aya sai ruwan hawaye ke zuba kamar famfo.
[08/06, 3:12 pm] +234 903 028 3375: YAN UBANCINA
MAMAN AFARAH
🅿️3️⃣⏩4️⃣
K’arasowa Malam Buba ya yi tsakiyar d’akin bakinsa d’auke da addu, a, yana kallon micijin da yake kaiwa tsakiyar d’akin wani irin mugu mugun Sara na ban mamaki, so yake ya fita ya d’akko wani ruwan addu, a a d’akinsa domin zai yi amfani dashi amma kuma zuciyarsa ba ta so ya tafi ya bar Ishalle da macijin a d’akin Dan gudun kar ya sareta domin girman miciji ya wuce misali tabbas zai cutar da ita dan da ganin macijin kasan cewa ba na lafiya bane. Ganin micijin ya tunkaro inda ya ke yasa yake ja da baya domin hatta idon macijin jajawur ya ke kamar garwashin wuta,Malam Buba nan take ya shiga karanta addu, o, i dan tunda yake bai tab’a ganin maciji mai girma da suffa irin tarbiyar wannan babban, dan har wani irin gashi ne a jikinsa fari tass kamar furfura, Kande tana tsaye a jikin labule tana hango Malam ta windon d’akin Ishalle ya wani rabe a jikin bango bakin nan sai motsi ya ke alamar ana janyo addu, a sosai ta ke dariya marar sauti har da hawaye dan dama boka ya fad’a mata cewa miciji Ishalle zata haifa domin ya dad’e da sanya aljannu sun narkar da jinjirin d’a ke cikin Ishallen sun ajiye k’aton maciji.
Malam Buba so ya ke ya d’akko ruwan addu, a a d’akinsa wanda zai yi amfani dashi shi wajen yiwa macijin addu, a amma kuma ba dama, nan take ya shiga k’walawa Kande kira domin ta d’akko ruwan a d’akinsa amma Kanden ta k’yaleshi ga macijin ya gama zuwa dab dance shi neman saransa ya ke, da ya gaji da kiran Kanden sai ya shiga kiran gozomar, gozoma tana wajen zaure a tsaye kamar ka ce kulle ta ce cass dan ma tana tausayin Ishalle sabo da macece mai hak’uri da dattako ga sanin ya kamata amma da wata ce zata haifi maciji da tuni ta tsufa a gidanta. Haka ta zo ta tsaya daga bakin kofa Malam Buba ya fad’a mata ta d’akko masa wata gora a rataye a jikin bango a d’akinsa haka ta d’akko ta zo tana d’ari – d’ari ta mik’a masa ta window.Malam karb’a ya yi ya fara k’ok’arin bud’ewa ,yana gama bud’ewa ya tsiyayo ruwan a hannunsa ya yi bismilla ya watsawa micijin nan take micijin ya yi wani irin k’ara mai ban tsoro, sake tsiyayo ruwan ya yi ya karanta ayatul kursiyyu ya k’ara watsawa micijin sai kawai Malam Buba ya ga idanun macijin sun koma koraye yana wani mirginawa a tsakar d’akin da Malam ya watsa masa a karo na uku sai kawai ya fara hayak’i ya ke zama kamar toka,a take tokar ta ke bin kofar d’aki har sai da ya zamana babu ko d’igon sauranta. Gozoma da ke wajen zaure a tsaye tana ganin ikon Allah bare Kande da take jin kamar ta je ta shak’e Malam Buba domin so ta yi micijin ya kashe Ishalle da Malam d’in in ya so sai ta ci gadon ita kad’ai dan ita bata MA zancen Nana dan har mantawa take da ita Dan bata fiya zaman gidan ba kullum tana mak’ota