Ad Code

Zaane Hausa Novel Complete

Zaane Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

Zaane

_(Zanen Dutse)_

 

 

_Halinsu ne ya zama Maɗaurin Kaddararsu_

*BINTOU

 

 

BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM

 

 

 

*001*

 

*Lagos Nigeria*

1st May

9:10 na safe

 

Ruwane ake tsugawa mai Karfi kamar zai fasa saman kwanukan jama’a ,Gudu yakeyi da iya ƙarfin Sa , Numfashin sa har sarƙewa yakeyi , Hannunsa riƙe da Ledar Magani mai ɗauke da Tambarin Chemist din Ayman Pharmacy,gudu yake sosai a tsakiyar titin da zai kaisadashi da Kangon tsohon Ginin daya kasance tamkar Makwanci su,burinshi ya isa wurin ya Ba ƙanwarsa maganin da ya ƙwato daƙyar, yarone sosai dan Bazai wuce shekara Goma Sha Huɗu ba wahala da rashin Girman jiki yasa zaka fassara shi a jerin Masu shekaru Goma sha ɗaya ko sha biyu.

Yar Senator Hausa Novel Complete

Shin Mu ɗin wane irin halittane da ake gudun Mu haka?, Kodai mu ba Mutane bane? ”

 

Ya faɗi hakan cikin ransa Sai yayi saurin Bama kansa amsa da “munada halitta tamkar na mutane ,muna raye kaman kowa”

 

“Amma meyasa ake wulaƙanta mu? Saboda me? Saboda me wasu mutanen suke wulaƙanta mu?”

 

Ya sake tambayan kansa a karo na babu adadi Ƙwallan da suka cika masa ido suka zubo Saman dakalin Fuskar sa, a daidai lokacin kuma Ruwan da ake tsugawa ya ɗan dakata, sai yayyafin dake saukowa a hankali.

 

“Shin mu muka kaddarowa kanmu wannan rayuwar?, Rayuwar kwararo? Miyasa ake kyarar mu saboda Allah ya jarabe mu da irin wannan kaddarar?”

 

Ya fada a bayyane yana ƙara ƙarfin Gudun da yakeyi.

 

“Tunda Rayuwar ƙunci mukazo yi a duniyar me yasa bamu mutu ba?, Meyasa?, Meyasa Bazamu mutu mu huta ba?”

 

Da Iya ƙarfin Sa yayi maganar jijiyoyin jikinsa na mimmiƙewa kaman wani babba , ƙarfin Gudun sa na Dada ninkuwa akan nasa Ruwan Sama ya jiƙashi sharkaf,Gam ya rike ledar maganin hannunsa kaman Za’a Ƙwace masa dukda kasancewar ba siya yayi ba kwatowa yayi a lokacin da me Chemist yake shirin Miƙama wata mata Batareda yasan ko maganin menene ba, Burinshi Mero Tasha ta samu lafiya.

 

Yana isa Kangon da suke kwanciya ya faɗa da sassarfa, saidai Abinda ya gani yasashi dakatawa yaja da baya agigice Numfashin shi yayi ɗaukewar wucen Gadi, Kafafunsa suka kama rawa gabansa na faɗuwa Tsananin tsoro da fargaba suka shige shi.

 

Ƙattin maza murɗaɗɗu Ƙirar karen Maguzawa ne akan ƙanwarsa suna shirin keta mata haddi su Bakwai Tumɓur Haihuwar Uwarsu , sai kokuwa Sukeyi akanta, Rashin ƙwarin Jikinta yasa basu Wahala bawajen rufe mata baki suka matseta Tamkar zasu fitarda Hanjin cikinta Ta baka.

 

A hankali Numfashin ta ke fita cikin azaba hawaye na cika idonta,Amma kaman babu zuciya a ƙirjinsu

 

“Mero”

Ya furta daker yana jin wani abu na sokar kirjinshi wanda hakan ya fargar da Mutanen ,suka taho sukayi masa Dukan Tsiya Suka wancakalar dashi gefe .

 

A lokacin har Mero ta Miƙe da yar ƙaramar ƙarfin Da take dashi zata gudu ,Babban cikinsu ya farga da ita, Wani irin damƙa ya kaima hannayenta biyu ya jawota da karfi tayi baya,ya buga kanta da gini, ya Riƙe hannayenta waje guda ,yasa Gwiwan ƙafarsa ya Buge ƙafarta Tayi baya Tafaɗi kanta ya bugu da wani ƙaton Dutse ta kwarma wani irin razananniyar Ƙara wanda Ya haddasa tashin Tsuntsayen dake kan bishiyan Dogon Yaro tashi Sama a tsorace Suna Fitarda Wani irin kuka mai Razananarwa.

 

Cikin tarin Azaba da raɗaɗi ta buɗe baki ta kwarma ihu da Ƙoƙarin kwace kanta ƙarƙarfan Riƙon da yayi mata, yasa tafin hannunsa Ya toshe bakinta bai ko damu da Dauɗa da warin dake busowa daga Jikinta ba, ya Fara ƙoƙarin aikata Burin shi akanta.

 

Ta Rintse idanunta Hawaye Suka silalo mata Cikin Yanayi na rashin Imani Ya Haye Kanta batareda Yayi la’akari da kankantar Shekarunta ba ,dan bazata wuce shekara goma sha biyu ba, ya barge rigar dake jikinta suka fizge Suturarta suka jefar da shi can gefe.

 

Sule dake kwance Cikin jini ya  rufe idanunsa wasu irin siraren hawaye na sauko masa ,a yayinda Wani yanayi ya gifta a idanunsa ,wani yanayi na chan baya inda ako wane lokaci ire-iren gardawan nan suke zuwa suyi lalata da Mahaifiyar su a gabansu.

 

Cikin ƙanƙanin lokaci ya keta mata haddi ,Ba mutum daya yayi ba, ba biyu ba, ba uku ba, ba hudu ba, haka suka jera su Bakwai suka yi mata yadda suke so Batareda sunyi la’akari da yarintarta ba, budurwa Wacce bata san komai ba , wacce bata wuce Goma Sha Biyu ba.

 

Suna ida biyan buƙatar su suka fita suka barsu kwance Yaron na nishin Wahala, Yayinda Mero ke kwance kamar tsumma babu alamar Rai a Jikinta,Abun ka da ɗan uwa suna fita Sule ya yi karfin halin rarafawa ya isa inda yagaggiyar Rigarta yake ya dauki rigar da hannun shi da yakeji kaman A ɓalle yake Dan ba ƙaramin dua yasha a hannunsuba kuka yakeyi sosai harda majina ya daura mata ya suturta mata jikinta ya fara taɓa Fuskarta a hankali yana Kiran sunanta da In inar dake wahalar dashi matuƙa wajen Magana.

 

“Mm…mm…Mero”

 

“Mm…kkkk…ki..Tashi”

 

Amma ina Kaman ta Mutu, zubewa yayi jikinta a sume saboda jirin da ya jashi.

 

 

Yaran Sun taso basu san kowa ba sai mahaifiyarsu wacce Allah ya daurawa Lalurar taɓin hankali Sun shaƙu da juna ainun, ta yanda ya kasance dayan jigon rayuwar dayansu ne hakan yasa ya kasance ƙaunar tasu abin Burgewa saidai Rayuwar tasu cike take da tausayi, kunci da damuwa a duk lokacin da mugayen Aljanun Kan Mahaifiyar su suka motsa, basua tantance ƴaƴanta da akasin su jibgansu takeyi kaman Ta samu jakkai ,amma dukda haka Babu abinda ke raguwa na daga cikin Ƙaunar da ƴaƴan Sukema uwar tasu Saima Dada ninkuwa da Ƙaunarta keyi a cikin ransu, dukda kankantar shekarunsu Sunsan ita din Uwa ce kuma basuda kamanta Duba da yanda mutan gari ke ƙyamatarsu basu son matsowa kusa dasu basu san haɗa hanya dasu, kowa kallon Ƙyama yake binsu dashi, suna ganin kowa cikin Sutura gata lafiya da sanin ya kamata, Su kam basuda Mafadi basuda abokin Tarayya, Ganin Kansu suke kaman su ɗin ba Jinsin Bil’adama bane, gani suke kaman Su ɗin wasu datti ne daga Cikin Jikin Bil’adama marasa Amfani.

 

 

Daidai lokacin da motar baka wuluk kirar Mercedes BENZ C-Class ta sulmiyo ta shigo layin kamar walƙiya ,Yau ma kamar kullum ya fito yana takun nan nasa a hankali, cikin baƙar danyen Suit Mai dan nauyi sai karewa Unguwar kallo yake cikin yamutse fuska

 

Journal James IBRAHIM Alaxender kenan shahararren Matashin ɗan jaridan ZTA channel 5 LAGOS wanda ya Shahara wajen Yaɗa labarai na Ban Al’ajabi wanda su ya fito nema a daidai wannan lokacin

 

 

Idanunsa ya sake watsawa yana kallon Unguwar yana nazarin taya Bil’adama ke rayuwa a irin wannnan Kazantar, ba Dole cututtuka su yaɗu ba? Girgiza kansa kawai ya yi ba tare da ya ce uffan ba, ya dawo da kallonsa ga motarsa bayan ya fito ji yake kaman ya koma , ya Tsayar da wani Mai pure water ya siya ɗaya sannan ya shige cikin Kangon dake fuskantar Inda ya Parka motarsa yana neman inda ya kamata ya yi fitsarin.

 

 

 

Wurin ya ɓaci da yawa Saboda ruwan da ba’a jima da tsagaitawa ba, da kuma rashin Kyawun wurin, irin Kauyen nan ne dake dauke da Ƙananun gidaje da wadatuwar Kangunaye da rashin kyan hanya Haɗida yalwatuwar Bola ta ko ina ,irin yanayin ƙauyen Askamaye na Lagos, don haka ya dinga jin Kyama ya kasa ajiye Kafafunsa yadda ya kamata, yanda yake jin fitsarin baya jin zai iya komawa.

 

Wuri ya samu ya zaga ya shige, sannan ya biya buƙatar ya ciro Tissue paper yayi tsarki dashi, sannan ya ɓula ledar pure water da yasiyo ya wanke hannunshi ya kuma gyara gefen takalminsa da ya ɗan bata da fitsari , ya mike hannunsa riƙe da ragowar Ruwan pure wata yana shirin fita yaji . Numfarfashin da yakeji sama-sama yasa yaji gabansa ya faɗi yayi saurin maida Dubansa wajen yana faɗin

 

“Blood Of Jesus, Blooood of Jesus….jesus”

 

Jin Numfashin na daɗa ƙaruwa ne yasa Tsananin tsoro ya shige shi. Don haka ya yi tsalle gefe guda yana zare idanu, ƙafafunsa suka hau rawa, bakinsa bai bar furta kalmar Blood Of Jesus ba ya leƙa inda yakejin saukar numfarfashin,Burinsa ya samo Rahoton da zai wallafa a shafinsa na sada zumunta Ji ya yi kamar Kafafun sun gaza daukarsa, tsoro ya dabaibaye shi a daidai lokacin da Idanunsa sukayi masa Arba da ƙyakkyawan fusjarta .

 

A hankali yake jiyo sautin Sule yana faɗin

 

“Mero na….mamana… Mahaukaciya… Kina ina….ki tttaimakke mmmu, zan mutu zan Mutu”

 

 

Karasa shiga yayi, wannan karon yayi matuƙar ƙoƙari wajen rike tsoron da yakeji ya ɗago yaron dukda dauɗar jikinsa bai damu ba ,gani yake abinda zai samu a kansa yafi mahimmanci, ya tabbata Abinda yaran ke dauke dashi zaiyi matuƙar janhankalin al’umma idan ya wallafa abinda ke faruwa dasu a shafinsa na YouTube Tiktok Instagram zai zama gaba cikin jerin masu trending ta ko ina.

 

Yarinyar kwance take cikin jini ko ba’a fada masa ba yasan fyade aka nata, aka kuma zane yaron ,Saidi ya rasa taimakon da ya kamata ya fara basu, Duk yadda ya so ya yi Karfin hali ya kasa, tashi yayi da sauri ya ja da baya da baya ya fice daga Kangon yana Ambaton

 

“Blooood Of jeeesus…!”

 

Wata mata ya hango ta ɗauko yaranta biyu daga Lesson Tana Riƙe da hannunsu su biyu daga ita sai Half gown da bai ida rufe cinyoyinta ba, sai uban sauri take rafkawa ya sha gabanta da faɗin please Babu inda zai sami manya ne a wajen nan?, Wata yarinya yagani a yashe anyi mata fyaɗe.

 

 

Da Yarbanci yayi maganar dan ya lura shine Yaren da mafi yawancin Ƴan unguwar suke Ji, ta kalleshi cikin yatsine fuska tace

 

“And so….?, Abege comot for my front, You wan help Wèré?, Ebe like say na were breast You suck for your mama’s chest ”

(Sai me…..?, Dalla matsa min Na wuce , yar mahaukaciyar kake son ka taimaka?, Da alama kaima Mahaukaciya ce ta shayar dakai)

 

 

Ya tare mutane sunfi biyar amma babu mai taimakawa, Wanda dama a bayyane yake a wannan zamanin Abu ne me matuƙar wuya kaga Mahaukaciya na neman taimako an taimaka mata wasu Mutanen gani suke kaman taimakon su asara ce.

 

A haka Ya dauki Yarinyar kaman gawa yasata a mota sannan ya dawo ya dauƙi Sule dake ta Faman sumbatu cikin fitar hayyaci yasa shi a mota ya harba Motar sa izuwa wani Private Hospital mafi kusa already ya kira wani abokin shi ɗan sanda ya sanar dashi , Cikin ƙanƙanin lokaci aka karɓe ta aka fara fara bata taimakon gaggawa Tareda Gudanar da Bincike akan abubuwan da suka shiga Jikinta.

 

Cikin Awa ɗaya Sukayi nasarar Dawoda bugun Numfashin ta, saidai abin mamaki sai ganin Mahaukaciyar akayi tana sintiri a Harabar Asibitin  tana surutai Ita kadai a Harabar Asibitin, abinda yabama kowa mamaki, sai korarta ake tana dawowa.

 

Sai Ƙarfe uku da rabi na rana aka basu Umurnin Ganinta a lokacin Sule ya jima da Farfaɗowa har an mishi wanka an bashi abinci ƙarƙashin kulawar James wanda tuni ya rafkawa abokin Aikinsa Bukhar Kira a waya yayi masa kwatancen wurin nan da nan Yazo dukda dan Tazarar dake tsakanin Asibitin da makwancinsu, a tare suka shiga Dakin da aka chanza mata mahaukaciyar na biye dasu tana ta Faman Surutai, Hannunta riƙe da na ɗanta sule wanda ya bayyana masu cewan Mahaifiyarsu ce.

 

Har yanzu Yarinyar bata farka ba, tana Kwance Fuskar nan tayi fayau alamar Babu jini a Jikinta, wuyanta ya miƙe Samɓal kaman Karan Fulani.

 

Mahaukaciya tayo kanta da gudu, ta cire drip dinda aka daura mata da ƙarfi tayi wurgi da shi ,sannan Ta ɗauke ta chak zata goya ,Sule yayi saurin Tare hanya Hawaye na bin Fuskarsa, cikin Maganarsa da ba fita yakeyi ba yace

 

“Mmm….mm.ma..haukaciya Ddd dan Allah kkki ssssauke ta kinga batada lafiya Karki jin mmmm…”

 

Bai ida maganar ba ta ɗauke shi da mari ,cikin tsawa tace

“Uwarka ce?….ko zaka haifeta ne?, Hahahaha suke ciki kake dashi ko?, Kana naƙuda ne?”

 

Saii ta kwashe da dariya

 

“Hege yarona me ciki yazo naƙuda”

 

Duk abinda ke faruwa James na ɗaukar komai da wayan hannunshi ƙirar Infinix hot 30, hakan ya zama tamkar al’ada a wajen wasu yan jaridun basuda burin da ya wuce Su kasance Na gaba wajen yaɗa labaran da zai jawo hankalin jama’a batareda Sun damu da illan Da yin hakan zai iya jawowa ba , Bukhar ya dube nurse yace

 

“Zuwa yaushe Zata iya farfaɗowa?”

 

“Maganin bacci mukayi mata wanda zai iya daukanta nan da akalla Awanni Uku”

 

Nurse ta faɗa tana gyara mata rufa bayan Ta samu Mahaukaciyar ta sauke ta da ƙyar, tay tsaye tana ƙare mata kallo cikeda tausayi.

 

Har bayan Asr Bata farka ba, Zuwa lokacin an kawo results ɗin maniyyin da aka ɗauki sample ɗin shi a Jikinta ,Dr Bilaal ya kira Su ya shaida masu sakamakon Gwajin cewa cikin wanda sukayi Amfani da ita akwai wanda ke ɗauke da cuta mai karya garkuwar Jiki Wato HIV wnda hakan ke nuna lallai ta kamu da cutar itama, Cikin Firgici James da Bukhar suka ƙwallo ido a tare suka furta “WHAT….!”

 

Dr ya gyada kai cikin bada tabbaci yace

 

“Tabbas haka Gwajin da muka gudanar ya nuna mana,gaskiya rashin Imanin nan yayi yawa Ya kamata a bi mata haƙƙinta ya kamata a samu mai tsaya mata a ƙwatar mata yancinta”

 

James ya Harareshi cikin Harshen Yarbanci yace

 

“Kai ka tsaya mata mana?”

 

Bukhar ya ɗan bugi kafaɗarshi

 

“Jame Zy ya kamata ka duba lamarin nan , rashin Imanin nan yayi yawa”

 

James ya dubeshi yace

 

“Zaka taimaka mata?”

 

Bukhar ya sauke kai cikin rauni , James yace

 

“You see, no body is willing to help ,wadannan mutanen Su kansu basuda hope a rayuwar da Sukeyi, Suna rayuwa ne kawai dan Su ɗaukaka mu , idan Sun mutu babu wanda zai damu dasu ,suna raye ne a dalilin Mu dan haka ya zama dole muyi amfani dasu wajen Ɗaukaka Matsayin Mu”

 

Cewar James

 

“Innalillahi Wainnailayhirraji’un”

 

Dr ya furta a daidai lokacin da wasu hawaye suka ja burki a kwanan Idanunsa , mutanen mu basuda imani basuda tausayi, ya kamata ya aikata abinda suke gudu zai taimaketa ya kuma zama dole a hukunta Koma waye ya aikata mata wannan ɗanyen aikin, ya zama wajibi a gurfanar dasu ta yanda hakan zai zama izina ga masu niyyar aikata Wannan mummuar aikin sunyi amfani da Rashin Gatanta sun Wulaƙanta t ta faɗa hannun marasa imanin yan jaridu Wadanda basuda burin da ya wuce yaɗa Labaran Su dan sunga batada gata, batada mai kareta daga aukuwan hakan.

 

yaɗa labarai na da matuƙar tasiri wajen kama masu laifi, Amma bayyana fuskar wacce akaci zarafinta Yafi laifin da aka aikatawa mutum muni Domin dalili kenan da ke hana iyaye bayyanawa hukuma Tozarcin da ake yiwa yaransu, Babu wance zataso yar ta ta fito ana nuna ta ana faɗin Kaddarar da ta faɗa mata.

 

Wani sashe daga cikin zuciyar Dakta nason gano wanda ya aikata lamarin, amma baisan ya ZAI fara ba, amma yazama dole ya karfafawa Jami’an tsaro su shigo lamarin Sosai dukda kasancewar ta ba kowa ba , ya sawa ransa zai tsaya mata.

 

 

Tsananin Tausayinta ya bayyana ƙarara a fuskar Journal Bukhar, Amma bayajin Zai iya bata lokacinsa wajen taimaka mata, haka ba ƙaramin Girgiza James IBRAHIM Alexander yayi ba a lokacin da likita ke sanar masa da cewar Cikin wadanda suka sadu da ita akwai mai ɗauke da Cuta mai karya garkuwar Jiki wato HIV, ya kuma Tsorata da Lamarin duniyar nan, saidai kuma a ransa da ya tuna cewa Musulma ce kuma wanda ya aikata mata hakan Musulmi ne sai ya taɓe baki a fili ya furta

 

“It’s their family matter”

 

Ɗaga nan hankalinsa ya koma kan Rahoton da yake ɗauka, Mahaukaciyar da ɗanta Duk sunyi laushi, ta ɗora kan Sule a cinyarta tana Shafawa a hankali, ta kurawa fuskar Mero Ido tana kallo kaika rantse Hankalinta ne ya dawo , Bukhar ya sake fita ya siyo masu Abinci Sule ya tashi ya karba zai fara ci Mahaukaciyar ta kwace Robar a hannunsa tayi Wurgi dashi sai ta fashe da kuka, shima sulen kuka ya fashe dashi Ya rungumeta yana faɗin

 

“Mmmm… Mahaukaciya Ddd dan Allah kki daina Zzzubarwa Yyy…yunwa nake ji, kinga tun jiya banci abinci ba”

 

Hawaye suka sake zubo masa yasa bayan hannu ya share yace

 

“Kema kina jin Yunwa ko? ,Dan Allah mmmm… Mahaukaciya ki ddd…Daina zubarda abinci kinsan muna shan wahala kafin a bamu”

 

Ya rufe maganar cikin fashewa da kuka , Mahaukaciyar Bata ce komai ba sai ta zuba masa Idanu kaman Mai shirin Yin magana amma babu wata kalmar da ta fito daga bakinta, yaron ya Lumshe idanunsa hawaye suka sake zubo Masa, ta daga Hannunhagunta tana shafo hawayen daKe zuba Daga kurmin idanunsa, sai kuma kaman an tsikareta ta Sauke hannunta tana motsa baki a hankali ta kai dubanta kan Abincin da ta zubar shinkafa da miya ce Gabaki ɗaya Miyan ya ɓata farar Tiles din ɗakin ,Tasa hannayenta biyu ta kwaso Abincin takai bakinshi ya bude baki Murmushi haɗida yar guntun ƙwalla ya kwace masa saida takai Hannun daidai bakinta ta ɓarar da Abincin ta ware Yatsunta biyar babu zato yaji saukar mari a kuncinsa, ta kuma daga hannu zata wanke shi da mari nurses din Suka Riketa

 

“Yunwa nakeji”

 

Yaron ya ambata cikin yar karamar Muryarsa cikin Shessheƙar kuka yana dafe cikinsa batareda ya damu da Zafin marin da tayi masa ba dan da alama ya saba shan Irinta.

 

James ya dubeshi yace

“Kanajin yunwa?”

 

Yaron ya gyada kai ,James yace

“Kana so In sake siyo maka irin wannan abincin?”

 

Da sauri ya kuma da ga kai, Bukhar yace

 

“Idan Kanason Abinci ya zama dole ka bamu Amsar duk wani tambayan da Zamuyi maka, kaji”

 

Ya sake gyada kai, James yace

 

“Yaushe Rabonka da kayi wanka?”

 

“Wanka…?”

 

Yaron ya maimaita kalmar Cikin Rashin sanin Amsar da zai bashi , James ya girgiza kai cikin Taɓe baki ya samu wuri yA zauna yana kallon yaron a ƙyamace, burinshi ya naɗe rahoto su fice daga Asibitin Zuciyarsa har tashi yakeyi kasancewar sa mutum wanda ya tsani Ƙazanta duk kankantar sa , ya zauna kusa dashi bayan ya Saita na’urar dake naɗe magana wato recorder, Bukhar ya Saita camera

 

James yafara da faɗin

 

“Sunana James Alexander, inaso duk abinda na tambayeka ka cire tsoro ka bani amsa kaji”

 

Yaron ya daga masa kai

 

“Ya Sunanka?”

 

“Sunana…?”

 

Ya maimaita cikin karamar Muryarsa mai ɗauke da inina ,James ya Gyada masa kai shuru yayi na wani lokaci sannan yace……

 

 

 

 

 

 

 

 

Am back Again…..!

 

 

 

Bintou ce

 

1st May

Nayi Gabas

Z* *A* *A* *N* *E*

 

 

 

*_002_*

 

“Ada Banida suna, wata rana na haɗu da wani mutumi a Abakin Titi lokacin naje kallon yan Ƙwallo sai Naji ya kirani da Sule wai nayi masa Kamada wani Sule ɗan abokinsa”

 

james ya Gyada kai alamun gamsuwa sannan ya ɗora da tambayanshi shekarunshi nawa , Sule ya kauda kai

 

“Ka daina Min irin wannnan tambayan, Kasan banida Amsarsu”

 

Shuru james yayi yana Dubansa da mamaki ,Batareda sule ya sake dubansa bayace

 

“Eh Ban san shekaru na ba, Bamuda kowa Bamuda gida, bamuda me kirga mana shekaru, A ginin makarantar Boko muke kwana ko kasan gada ko kango , so ttt….tari mmmm..munfiye kwana a Cikin Bola, Mu kadai muke rayuwa Mutane basu son mu basu son su Bamu Abinci Sun gummace su Bama kare akan su bamu, Yara masu shekaruna suna tsoron mu, suna jifan mu, Malam dan Allah akwai mutane irin mu a duniyar nan?, Dan Allah idan akwai irin mu ka kaini wajensu ina so muyi wasa tare, muyi dariya tare mu shiga Bola tare mu hana masu kuɗi irinku aikata mana irin abinda akayi ma Mero, Mahaukaciya ma anshayi mata hakan a gabanmu”

 

Sai ya dakata yana kai Dubansa kan Mero da ke kwance tana sauke numfashi a hankali, Mahaukaciyar ta ɗora kanta a kafaɗarta tana bacci ,shuru ya Ratsa wajen na wasu yan sakanni Bukhar na ƙoƙarin hana Tausayin Bayin Allahn Tasiri a zuciyarsa yayinda ,zuciyar James ta daɗa ƙosawa da zaman shi a Asibitin Burinshi ya Naɗi rahoto ya ƙara gaba ,kukan da yaron ya Kara kecewa dashi ne ya dawo dashi hayyacinsa,ya dubeshi

 

“Kukan me kakeyi?”

 

Sule ya girgiza kai Hawaye na daɗa Zubo masa, James ya sauke ajiyan Zuciya

 

“Ya Sunan Yar Uwarka?”

 

“Mero ”

 

“ITA kuma taya akayi ta samo wannan sunan?”

 

 

“Ni na sa mata sunan saboda Ina ssson Sunan, Sunan wata ce me siyarda hura a jikin Kangon da muke kwana, ta kan kai talla in ta dawo sai ta rago mana Shine kawai Nasa mata Ss…Sunanta”

 

_yaron ya cika in ina_

 

Bukhar Ya furta a ransa sannan ya mika masa hannunsa yana kara Saita Cameran sa a Jikin hannun da yayi gaja Gaja da Kuraje, sai ya nade hannayensa ya matsa baya yana Zare manyan Idanuwan sa , wasu hawayen har sun fara sauko masa, wani zafi ma yake jin zuciyarshi na masa saboda yawan tambayan akan Rayuwar su da yake.

 

“Ina mahaifin ku?”

 

Ya tsinci Muryar Bukhar, bayan Ya Gyara zamansa, da mamaki Sule yace

 

“Dama Muma Munada Mahaifi?”

Bukhar ya daga masa kai sannan yace

 

“Ina yake?”

 

“Ban sani ba, Ni ai na Aza mu Uku ne a duniyar mu ,malam dan Allah Ina zamuje Mu ganshi? ,A Ina Zamu Samoshi?, Inason Zama dashi ”

 

 

Yayi Maganar cikeda yarinta da rashin Sani, yanda yake maganar cikin Natsuwa bazakace kananun shekaru gareshi ba, james ya kauda kai daga dubanshi Dan duk Rashin Imanin shi wannan karon Saida yaji tausayin yaran da mahaifiyar su ya darsu a Zuciyarsa ,Bukhar ma gwiwan sa Dada sanyi Yayi, James ya kamo hannun Sule cikin hannunsa ɗaya, ya ƙara matso da abin Maganar daidai Saitin bakinshi cikeda Salon jan Hankali da neman Suna ya ce

 

“Share Hawayen ka ƙanina kaji, kaima mutum ne kaman Kowa, kuma zaka iya zama babban mutum irina, da yardar Allah zaka samu ɗaukaka Samada Nawa Mahaifiyar ka sai ta samu Lafiya itama Mero Allah ya Bata lafiya”

 

Sule ya gyada kai Murmushin da ya Mance Rabonda yayi irinshi ya Ƙwace masa, Dauɗaɗɗun haƙoransa suka bayyana, James yayi Saurin Kauda kai a ransa yana faɗin

 

“God forbid bad thing”

 

Bukhar ya cigaba da cewa

 

“Daga yau Sunanka ba Sule ba, sunaka Sulaiman”

 

Yaron yayi murmushi dan tun tasowarsa babu ɗan gayun da ya taba rike hannunsa yayi masa magana cikin Tausasawa kamar haka, kowa ƙyamar su yake, dukda a wasu lokutan akan nuna masu tausayi amma ba’a cika kusanto su ba, kasancewar haukar Mahaifiyarsu ya haɗa da duka da jefe jefe

 

“Sulaiman”

 

Ya maimaita sunan cikin washe baki ,James ya shafa kan Yaron don yaron ya burgeshi matuƙa

 

“Ita kuma Mero ka dinga Ce mata Maryam ko mary”

 

yaron ya kada kai da murmushi a fuskarsa, ” to” ya amsa da sauri, Bukhar ya cigaba da faɗin

 

“Dakyau Abokina Zaka iya Tuna abinda ya faru ɗazu?”

 

“Wane abu kenan?”

 

“Abinda ya faru da ƙanwarka mana”

 

“Auho Eh zan iya tunawa, Maryam batada lafiya , shine na fita don nema mana abinci da magani ina dawowa naga Wasu katun katun maza babu Kaya suna…….”

 

Tiryan Tiryan Ya bashi labarin Komai, James ya sake Jefo masa wata tambayar

 

“A lokacin Mahaukaciyar tana ina?”

 

Ya James kirata Mahaukaciya ne don yaji haka yaron yake kiranta

 

“Bansan inda taje ba, so tari Idan Gari ya waye takan kewaya bayan Kangon da muke kwana tayi wasanta Rashin Lafiyan Mary ne yasa Bamu bita ba dan Dama Tare muke zuwa”

 

“Zaka iya gane fuskokin Wadanda kaga sun aikata mata Wannan abin?”

 

Ya gyada kai

“Eh fuskar Babban cikinsu na nan a idanuna saidai sauran in na gansu zan iya ganesu”

 

“Siffanta min Fuskarsa”

 

“Dogone Akalla tsawonsa bazai wuce naka ba ,kafadarsa tsukakke ne amma ba sosai ba, ka fishi fadin kafada, sannan Fuskarsa a daure take , yanada tattararren Goshi baƙine amma ba ƙirin ba idanunsa kaman na Mamana Hancinsa dogone Amma yanada fadi kadan yanayin fasalin fuskarsa irin na abokin nan naka”.

 

 

Ya faɗa yana nuna James dake riƙe da abin magana ,Cikeda natsuwa ya siffanta kamannin Mutumin kaman dama ya taɓa Ganinshi.

 

 

_Yaron nada Wayau sosai, What a wasted talent_

 

Bukhar furta a ransa sannan ya Sake jefo mashi wata tambayar, bai ɓoye masu komai ba, Journal Bukhar da James sun jima kafin su Gama yi masa tambayoyin, babu inda Basu Taɓo ba a Ɓangaren Rayuwarsu ,Har saida suka sa shi kuka, Ba abu ne mai daɗi ba a taɓo wani ɓangare na rayuwarka, Ɓangaren da kai kanka baka so ka tuna, ba abu ne me sauƙi ba kayi bayani akan irin ciwon da Rayuwa tajin maka ba, irin ciwon da Bakada halin Ramawa, irin ciwon dake da wuyar warkewa, a iya shekarunsu akwai Raunuka da dama a zuciyoyinsu, Tabbas akwai masu Rayuwa da damuwa tun suna Jarirai Bamu sansu bane don bamu Rayuwa dasu, Muna rayuwa ne da mutane Irin mu masu cikakken yanci masu dariya, masu farin ciki kullum dan Allah ko sau ɗaya ne ki kwatanta tare ƙaramin Almajiri a hanya ki tambayeshi yanda yakeji a duk lokacin da Ya fita yayi Bara be samu ba, Amsar da zai baki kadai ya isa yasa ki godewa Allah akan tarin Ni’imar da Allah yayi miki na kasancewa mai cikakken yanci a Gidan namiji either Mahaifinki ko mijinki. ….

 

A zantawan da sukayi dasu sun fahimci cewa wannan bashine karo na farko da aka fara kaiwa Maryam hari ba ,ansha Kawo Mata hari so da dama Mahaukaciyar ke Haukace masu take fin karfinsu dan babu karya akwai karfi a tattare da Ita ,itama Mahaukaciyar basu barta ba ansha yi mata fyaɗen a gaban yaran nata, wanda hakan ke nuna ansha fin ƙarfinta aci galaba akanta, Amma Sun kasa fin ƙarfinta suci galaba akan yarta , Bayan sun gama samun abinda suke so a take sujaji Zuciyar su tayi Fiffike tayiwa Gidan Talabijin Zarian Television Authority Lagos channel 5 tsinke Bayan sun ajiyewa Sule Dubu biyu da cewan zasu shiga kasuwa su dawo, Abinda bai sani ba, Sunyi Amfani dashi Sun Samu abinda suke so sukeso sun ƙara gaba abinsu.

 

Kaman yanda James ya Tsara, Ya posta video din yaran a kafafensa na facebook Instagram, Tiktok garda YouTube , Kuma burinshi ya cika ya samu Abinda yakeso cikin Awannin da bazasu wuce uku ba ya samu more than 800k viewers ya Kuma samu followers Fiyeda ƙima, Dama So tari ire iren labaran nan Nada matukar ɗaukar hankalin jama’a cikin kankanin lokaci aka fara reposting kafin Wani lokaci Hotunan Mero kwance cikin jini dama wasu videos nata marasa Kyan gani sun yaɗu a Yanar gizo da kuma Result ɗin da likita ya tabbatar da Cikin wadanda sukayi mata fyaɗe akwai Mai cutar HIV, hirar da sukayi da Sule Kuma an kai Sashen tace rahotanni na gidan talabijin ZTA inda suke aiki aikai Zuwa Monday Zasu sakeshi a Shirin su na musamman…..

 

 

Zaria Kaduna

*Nigeria*

 

Sanye take cikin Uniform Na masu bautan ƙasa (NYSC) kayan yayi mata yawa sosai wuyar Rigar yayi mata fadi dayawa Har yana saukowa kafaɗarta, haka wandon Sai jan ƙasa yake, kafafun nan Sunyi butu butu, Hular PCap Uniform din juye a Kanta , kayan sunyi Wani uban dauɗa ,Farar Rigar ta rine ta Koma baƙin ƙirin tsabar dauɗa har wani yauƙi yauƙi sukeyi , Yanda kayan ke tattareda ɗauda haka Baƙar fatarta ke walwali yana Ƙyallin ranar dake gasata ,ta nuna sosaidan har ta fara fashewa ita kanta ba ƙaramin Juriya takeyi ba wajen shaƙar Ƙarnin dake tashi a cikin Jikinta.

 

Hannunta riƙe da mangoro tanasha har tana kada kai, Wanda ta ƙwato a hannun wani ƙaramin yaro da mamanshi ta bashi ya tafi makaranta, haka Takeyi da zarar taga Abu a hannun yaro taji tana marmarin Abin sai ta ƙwace ta kuma lakadawa yaron Dan banzan duka, wannan karon bintou tayi matuƙar sa’an mangoron da ta ƙwato ƙato ne sosai bata fiye son Mangoro Mai Karfi ba shiyasa ta tsaya jikin Wata gini tayita bubbugashi da bango har yayi ruwa, tanasha Ruwan na tsiyaya saman hannunta yana bin sahun hannun har cikin Rigarta, Gabaki ɗaya Ruwan Mangoron ya ɓata Mata kaya dama gasu nandanƙare da dauɗa, ji take kaman Ta cinye har ƙwallon Mangoron saboda tsabar daɗi,

.

 

Ruwan sai gangarowa yake yana bin hannunta har izuwa cikin Jikinta, ƙudaje sai Binta suke, amma bata damu ba sai Faman tauna Ɓawon take tana zazzare ido, ga zafin ranar dake gasata Fuskarta na fitarda wani irin maiƙo tana sheƙi, kallo daya zakayi mata ka ji gaban ka ya faɗi sai kayi tunanin Daga Duniyar Aljannu aka wullota tayi ɓadda kama.

 

Ta gaban shagon Bala me provision ta wuce Saida ta galla masu harara ɗaya bayan ɗaya ganin Irin kallon da suke Binta dashi Sannan ta wuce tana jan tsaki still mangwaron na hannunta tana tsotsan Kwallonshi.

 

“Bala anya babu gaskiya a maganganun Mutane ? Da sukace Bintou yar Aljanu ne?, Jitafa babu wani Kamannin da ya nuna ita din macece kuma bil’adama”

 

 

 

Cewar Iliya dake tsaye jikin Shagon, Bala ya taɓe baki yace

 

“Aini koda naji ance yar Aljanu ce ban Musa ba, domin kuwa Uwarta Makauniya ce, da Alama taka ɗansu tayi Suka kamata suka ɗirka mata ciki, ta haifo wannnan Rabi mutum rabi Aljan ɗin”

 

Gaba ɗayansu suka sa dariya, sai kuma lokaci Guda dariyar tasu ya ɗauke ɗiff kaman An tsaida ruwan Sama sakamakon Arba da Ita da sukayi a gabansu ta zura masu Idanu har yanzu ƙwallon Mangoron nan na hannunta sai Faman Lashewa takeyi, yayi fari tas ya fidda gashi kudaje sai Binta suke, tsawa Bala ya daka mata

 

“Ke menene Kin wani tsaya kin zura mana ido Lafiya?”.

 

Iliya yace

“Mayya Mayya Kazamar banza Mai siffar Aljanu”

 

“Ni ba Mayya bace saidai In Uwarku ce Mayya kuma Ni ba Aljana ta haifeni ba Lantai da Hansai masu tallar Hura a bakin Kasuwa sune Aljanu”

 

Ta ambaci sunan iyayensu kai tsaye sannan Ta ware Tafukan hannayenta biyar ta jefa masu,tayi Wucewarta tana tafe tana Surfa masu duk zagin Da yazo bakinta har ta kai gida ,A bakin Ƙofar gidan nasu taga wani almajiri wanda bazai wuce sa’arta ba tsaye yana Bara, yana ganinta yabar ƙofar gidan, da hannu tayafitoshi da yazo, Jikinshi na rawa dan kaf unguwar babu wanda baisan bintou ba, tauraruwa mai wutsiya ganinki ba alheri ba, Almajirin yazo ya tsaya a gabanta, ta dunƙule hannu ta kaimai Rankwashi hae biyu a tsakiyan kansa da yasha kolon molo, sannan Ta kama kunnen shi ta murɗa Sosai har saida yaronyayi ƙara tace

 

“Ba na hana ka Bara a ƙofar Gidan Mu ba?, dan ubanka Bara aka turoka kayi a Zaria ko Karatu?, Tsabar Mugunta kunzo kuna neman Tsotse mana arzikin Da Allah ya bamu, Tho Allah yafiku bi izinillahi Yanda kake Bara haka Zaka ƙare Rayuwarka zaka ɓace min da gani Ko saina tsaga kan nan naka gida biyu tukunna? ”

 

Ta faɗa tana sakin Kunnensa, ya shafa kunnen yana kallonta kasa kasa, Almajirinn da yakejin kansa kaman ya fita fasali ta ko ina yayi gaba yana kallonta, Rabonshi da yin wanka tun Jumma’ar da ta gabata, sati ɗaya kenan, amma zai iya rantsuwa yace Bintou tafi wata ɗaya rabon da Jikinta yaga ruwa, kayan dake sanye a Jikinta kuwa har yayi wani jirwaye Sai zarnin fitsari take wani bauri mai ƙarfi na busowa daga cikin Jikinta.

 

Ya toshe hancinsa ya wuce yana ja Mata Allah ya isa, itama kallonShi take ko a Jikinta sai ma Surfa Masa zagi da takeyi a masifance.

 

“Bintou…..!”

 

Muryar yayanta ya daki Kunnenta daga bayanta, a gigice bintou ta ɗago cikin tashin Hankali ta amsa a tsorace

 

“Na’am yaya”

 

Yana tsaye a bakin Ƙofa fuskarsa a jike da alama Masallaci zashi kallonta yake fuska a yamutse wanda hakan Ya sake haifar da Tashin Hankali a wajenta, Saidai Dukda hakan bata cire ƙwallon Mangoron da take ta Faman tauna daga bakinta ba, kudaje nabin Sahun bakinta wanda duk Ruwan Mangoron ya ɓata Mata gaban farar Rigarta da ta koma baki tsabar dauɗa.

 

“wani dan ajin mu ne ya bani”

 

Wannan karon kam ya gama amincewa da bintou dai ɗiyar Aljannu ce , ba mutum yayi cikinta ba

 

“Jefarda kwallon nan”

 

Bintou ta sake cusa Ƙwallon Mangoron a bakinta tana magana ciki ciki.

 

“kawai sai mutum yazo ya sa min ido kaman tsohon Maye?, Dama mutane sunce Umman mu tayi Mu’amala da Aljanu ada, ga manyan idanunsa da yake zarewa kaman na Mayu, waya sani ma koso Yaƙe ya lashe Ni? Tho wallahi kurwata tafi ƙarfin ka”

 

a gidan nan kai kadai ke sa min ido kana kyararta kaman ba ciki ɗaya muka fito ba Mugunta da tsongwama iri iri babu wanda baya nuna min tho Allah ya isa tsakani na dakai, Allah zai biya min hakkina”

 

yanzu idanunta a cikin nashi, kallonta yake yana Yamutse fuska dan Gabaki ɗaya ƙyama take bashi, kallon yanda ta zuba mishi ido yayi tana tauna Ƙudaje sai kai kawo suke a Jikinta, Idanunta na ƙara girma kaman tsohuwar Mayya yayi saurin daka mata tsawa

 

“Ki Jefar nace kuma ki shige ciki kiyi wanka”

 

Bakinta dake Kumbure ta sake tana Dubansa, ƙudaje na cigaba da bin Jikinta, badan ya riƙe ƙofa ba da bai isa ya tsaya a gabanta yana auna mata wadannan muggan kalaman ba

 

Ya fara magana cikin fushi

 

“Wawiya ƙazama, yadda fuskarki take baƙa haka halayyanki yake bakin ƙirin babu abinda kika iya sai Ƙazanta tsiwa da shegen kwaɗayin Tsiya”

 

Daidai nan yaga ta Zaro Ƙwallon Mangoron daga bakinta, ta zuro harahenta waje tana Wani sambe Ƙwallon, zagin da yayi mata ko a jikinta

 

“Shegiya mummuna kawai marabanki da Mahaukaciya tantance kwaɗayi dan ke a rayuwarki iya abinda kike iya tantancewa cekann”

 

“Ɓace min da gani ƴar iska”

 

Ya faɗa yana ficewa ya bata dama Ta shige ciki da gudu tana cewa

 

“Ɗadin Abin ba Ni kadai iska ya haifa ba, harda kai a ciki ,wanka kuma baza’a yi ba saidai ka kashe Ni, dama ka saba duka na ba yau na fara sanin BAKADA IMANI BA”

 

 

 

 

….

 

 

 

Labarin yazo da Wani sabon Salo, sabbin abubuwa masu ban mamaki, akwai al’adu daban daban da kuma Banbancin addinai da kuma Irin ƙalubalen Rayuwa , Ƙalubalen da Hausawa ke fuskanta a kudu.

 

Tabbas akwai Damuwa a littafin nan, kuka da bakin ciki

 

Saidai kuma za’a kyakyata, Akwai Tsananin Soyayya Mai narkar da zuciya .

 

 

 

We’re still in free pages Littafi nan na kuɗi ne, a koda yaushe zan iya datse free pages daga yanzu har page 10 free ne, Amma datsewan Zata iya zuwa a lokaci ɗaya babu daga ƙafa.

 

Salon na musamman ne biya 500 ta Wannan acct ɗin 0478418742 Zakiyyah Ishaq GT Bank. Shaidar biya. 08110243438 .

Close Menu