Ad Code

Sai Naga Bayanki Hausa Novel Complete

Sai Naga Bayanki Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

SAI NAGA BAYANKI

 

*NA SADNAF*

 

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

 

*BISMILLAHI RAHAMANIR RAHIM*

 

*PAGE 1*

 

 

Rasheeqa

 

Kallon tv nake ba wai dan Ina fahimtar ma Mai nake Kallo ba dan hankalina ba a wajen yake ba, Kara daga kaina nayi na kalli agogon dake jikin bango zuwa lokacin raina ya Kai karshe wajen b’aci,wayata da na jefar a gefena na Kara daukowa na Kara Kiran lambarta Wanda Ina ga nafi awa daya Ina kiran ta bata d’auka ba miss call da na mata yafi ashirin,kamar yadda nayi zato har ya karaci ringing bata d’auka ba,girgiza kaina nayi na mik’e ganin goma da rabi tayi yasa na karasa wajen tv na kashe na dauki Yara na biyu Abul da Abla da tun wajen Tara bacci ya d’auke su na dauki Abul na dan bugi kafar yayansu Imrana da shi ma baccin ya Dade da kwashe shi Ina “tashi ka tafi daki ka kwanta”

Dan Tijarar Siriki Hausa Novel Complete

Mikewa yayi Yana mitsitsika ido ya hau sama ni kuma na shiga dakina na Kai Abul na kwantar na dawo na dauki Abla itama na kai ta dakin.

 

Na koma Palo na kulle kofar palon,na koma cikin dakina sai da na watsa ruwa na kwanta duk raina a b’ace har ga Allah kishatu ta fara Kai ni bango bazan zauna na zuba mata ido tana abinda ranta ke so ba,kiran mijina daya shigo wayata ya katse min tunanin da nake kamar bazan dauka ba dan duk ranar da ba nice da girki ba da haushinsa nake kwana dan gani nake yadda yake rawar kafa a kaina haka yake yi akan bakar matarsa,ban kuwa daga ba sai da ya sake kirana,na d’auka nayi shiru ya fara magana yana “Gimbiya ko har kin fara bacci ne”?

 

Kamar Yana gabana sai da na gama hararar wayar nace “Ban yi ba sai yanzu kaga damar kirana sai yanzu aka bar ka ka kirani kenan”?

 

“Gimbiyata kenan kema Kinsan duk abinda nake wallahi kina raina yau lissafi muka tayi sai yanzu na baro shago ko gidan ma ban kai ga karasa wa ba”

 

“Hmm na d’auka ai hana ka tayi ka kirani”

 

“Wane mutum yanzu ma idan kikace ba acan zan kwana ba kinsan tahowa ta zanyi nan dan ni akan dole nake nisa dake”

 

Sai a lokacin na dan ji sanyi a zuciyata bacin ran kishatu ya dan sakeni

 

Na saki murmurshi Ina “ai shikenan yanzu dai ka karasa gida sai da safe”

 

“Ina Su Abul ne banji motsinsu ba ko su ma sunyi bacci “?

 

“Sun Dade da bacci ni kadai ce banyi bacci ba”

 

“Kishatu ma tayi bacci kenan”?

 

Shiru nayi Ina Jin bacin rai na taso min da na daga kaina na ga Sha daya ta wuce har da minti goma

 

Sai na daure Ina “Tayi bacci itama tundazu”

 

“Allah sarki gimbiyata na d’auka fa zata na debe Miki kewa idan bana nan akan me za tayi bacci da wuri ko dai nazo na tayaki kwana”?

 

Har ga Allah da zai zo din Dadi zanji kuma Ina ce yazo din zuwa zai yi amma bana so ya gano kishatu bata gida hakane yasa nace “Aaa ba sai kazo ba ka wuce gida kawai nima na fara jin baccin kwanciya zanyi”

 

“Ba wani matsala dai ko ba wani Abun da kuke bukata”

 

“Babu komai Alhaji”

 

“Tom shikenan bari na karasa idan na isa zan kiraki idan kuma baki dauka ba nasan kinyi bacci gobe da asuba zan zo”

 

“Tom shikenan Ina Jira sai da safe”

 

Daga haka na katse wayar dan Allah Allah nake na kashe wayar na Kara Kiran kishatu a waya.

 

Sai dai Koda na sake kiranta haka yayi ta ringing bata d’auka ba.

 

Jefar da wayar nayi na kwanta zuciyata fal bacin rai har ga Allah bazan tab’a daukar wanan iskancin ba ya zama dole nayi kararta,toh wajen wa zan Kai kararta ma,Aunty Ama ce zata iya daukar mataki ita kuma munyi fada da ita,naja dogon tsaki da na tuna abinda ya hadani da ita nayi na Allah nayi na Annabi idan har Kishatu bazata shiga hankalin ta ba wallahi korarta zanyi bazan iya da wanan iskancin ba.

 

Ranar kishi bai hanani bacci ba bacin ran kishatu ne ya Hanani bacci sai bacci barawone ya sace ni.

 

Bugun da naji ana yiwa kofar shigowa palona da k’arfi ya Saka na bude idona sai da na wartsake na kalli agogo naga karfe 12:30 daidai wayata da na ragewa volume sai ringing yake ko da duba wayar kishatu ce take kirana.

 

Kamar wacce aka mitsina haka na mik’e zumbur nayi waje Ina Jin zuciyata na tafasa.

 

Har lokacin buga gidan take,yanzu da Alhaji a wajena yake haka zata zo ta zubar min da mutunci,yace kanwarta Yar iska ce bata gari bace.

 

A fusace na Bud’e k’ofar ta kuwa ja baya da sauri ta tsaya nesa dani,yadda nake jina ji nake kamar na jawota na hau bugunta,sai zare ido take ta matse cikin riga da skirt da ya fito mata da rabin nononta waje,dakyar ma take numfashi.

 

 

Cikin tsananin bacin rai na fara magana Ina “daga Ina kike kishatu”

 

Inina ta fara yi tana “Asmau na raka dinner Aunty wallahi bansan dare yayi ba ban kuma ga Kiran ki ba dan wayata na cikin jaka sai da muka taho naga ashe kin kirani”

 

A tsawace na fara magana Ina “Kishatu kina da hankali kuwa zawarci hauka ne,ni Zaki cewa wata banza kika raka dinner dududu yaushe kika dawo kasar nan da har kika san mutane,yau kika fara fita ki Kai dare?kusan kullum sai kin fita kin dawo da tsakar dare,?ni zaki zo ki zubar wa mutunci a wajen mijina ya d’auka bamu da kamun kai har macen arziki ce zata fita ta dawo daddare har ni zaki raina wa hankali ki fita barikin ki kizo kina cemin Kawa kika raka tom wallahi bari kiji na fada miki kinyi na farko kinyi na karshe bazan dauki wanan yawon iskancin naki kizo ki zubar min da mutunci a wajen mijina ba na taimaka miki ki zauna a gidana ne dan ke din jinina ce Ammi bata da burin daya wuce taga kanmu a hade kafin ta mutu haka tayi ta rokonmu mu rike ki hannu biyu,idan kina ganin gatan da zan miki na ki zauna a gidana har ki Kara samun wani mijin bai miki ba bariki kike so kiyi wallahi korarki zanyi bazaki zo ki zubar min da mutunci ba nayi iya yina har ga Allah nidai daga yau kika Kara fita wallahi baki Isa dawowa gidanan ba gwara ki tattara ki koma wajen Aunty Ama tunda bata da Aure ballantana ace zaki zubar mata da mutunci wajen mijinta ni kuwa da aurena bazaki zo ki jawomin ba yanzu idan Alhaji na nan yaga a yanzu kika dawo gidan wane Kallo kike so ya Miki ko ya.min ace kanwata ta fita tun yamma sai wajen dayan dare ta dawo hauka ake yi wallahi wallahi Kishatu daga yau kika kara fita karki soma doso gidanan kisan nayi”

 

Daga haka naja dogon tsaki na bar ta a tsaye tana Zare ido na shige dakina tare da Saka key,wallahi mugun haushin ta nake ji a madadin ta nutsu tunda Allah ya Mata baiwar kyau har Allah ya kawo mata wani shegen Mai kudin tunda na lura mazan nan suna da San fara ba dadewa za tayi tana zawarci ba amma shine ta nemi tayi amfani da kyan da Allah ya Mata ta ringa tsulla tsiyarta.

 

Naja tsaki tare da Jan bargo Saman kaina,Ina Jin lokacin da take kulle kofa wata hudu kenan da zuwanta Nigeria dan mijinta na sakinta ta taho Nigeria wai har tayi budewar idon da zata San mutane tazo tana zuba min bariki,na Kara jan dogon tsaki,Ina Shan alwashin in dai ta Kara fita ta Kai dare wallahi bazan duba uwar mu daya ba korarta zanyi tunda ba yarinya bace ita duk lalacewa dai ta Kai ashirin da shidda tana da Yara biyu idan bin Maza take so tayi sai ta je ta karata ba dai a gidana ba ta jawo min magana a wajen Alhaji.

 

 

Bansan ya akayi bacci ya daukeni ba,sai da naji tashin muryar Su Imrana daga Palo na Bud’e idona naga ashe gari ya ma waye nasan dole na makara duk da indai ta fanin tashi da wuri ne dan nayi sallah Allah yamin nauyin jiki.

 

Bandaki na shige sai da nayi brush na daura alwala nazo nayi sallah Ina daga daki Ina Jiyo kamshin dankalin da nasan kishatu ce take soyawa tunda tazo gidanan ta sangarta ni da aikin gidan kafin na farka zanga ta share ko Ina ta kuma dora abincin karyawa ta shirya yaran ma ta fanin nan dai kam ta siyeni wanan yawon da take yine kawai ya bata min rai,dan Ina da dan San jiki,indai ta ni ne Yara zasu iya makara ma,dan bani da saurin aiki,na kuma ki yarda na dauki Yar aiki Sam,dan Allah ya zuba min kishi.

 

Ina cire hijabin na gyara hulan kaina da na tusa gashina da ya barbazu dan asalin mu buzaye ne Allah ya mana baiwar gashi Mai yalwa da fari.

 

 

Ina Bud’e k’ofa nayi ido biyu da Alhaji Yana ta wasa dasu Abul, fitowa ta yasa ya dago yana “Gimbiya kin tashi kenan”?

 

“Yaushe kazo Alhaji”?

 

Bana ce miki ana asuba zan zo ba daga massallaci nayo nan da naga bacci kike na shige dakin yarana dan bana so na katse miki bacci”

 

Ya karashe da murmurshi a fuskarsa,wani irin farinciki na tsinci kaina a ciki,yadda Alhaji ke nuna min kauna har mantawa nake Ina da wata kishiya.

 

Cikin shagwaba da nasan Ina Kara rikita shi na fara bubbuga kafa Ina “Shine baka tasheni ba na fa dauka wasa kake bazaka zo ba”

 

“Tab abinda ko bacci ban yi ba mai zai hana ni zuwa,yanzu dai ki karaso ki shirya Yan biyu na Mika su makaranta”

 

“Ai na dauka driver ne zai Kai su sai Ka Kai Yan uwan nasu makaranta”

 

Take naga ya hade rai Yana “Mallama ki shirya min su ni zan Kai su makaranta da kaina”

 

Toh kawai nace nayi hanyar kitchen dan Ina ta Jin motsin Kishatu a ciki.

 

Ko da na shiga ta bani baya tana tsaye a gaban gas,tana sanye da sleeping dress Mai hannun shimi daya wuce gwiwarta kadan,indai mazaunai ne Allah ya bawa kishatu dan daga ni har Aunty Ama ta fimu baya har yau idan Ina kallonta sai nayita mamakin abinda yasa mijinta har ya saketa, wanda wasu da yawa sunce uwar gidan ce ta masa asiri ya saketa ya kuma hanata daukar yayanta,ko ni da nake mace shagala nayi da kallon ta tuna Alhaji na palo yasa nayi saurin rufe kofar kitchen din dan kar ya hangota,dan nasan Alhaji akwai kalle kalle ba laifi duk da Yana iya k’ok’arinsa wajen gudun bacin raina amma nasan Yana da wanan halin.

 

Motsina da taji na rufe kofa Yasa ta juyo da sauri tana “Aunty Ashe kin tashi Ina kwana”

 

Wajenta na karasa fuska a hade ina “Kishatu ya kika fito haka tsirara bayan kinsan mijina na iya ganinki”?

 

“Aaa Ina sallah na fito kitchen a lokacin bai zo ba”?

 

“Toh daya kwankwasa waye yaje ya bude k’ofar”?

 

“Ina ga da mukulli ya bude dan Ina daga nan kawai naji tashin muryar sa”

 

“Tom naji bari na je na dauko Miki dogon hijabi ki Saka daga yau karki sake ganganci fitowa haka tunda kinsan Alhaji na iya ganin ki kuma hakan ba tsari da baya garine ma da sauki amma da ya shigo ya ganki a haka tsirara gashin naki ma a Bude kamar dai kina gidan Maude”

 

 

Bata ce komai ba ni kuwa na juya na fito daga kitchen din na tafi dakin da na sauketa na dauko zungureren hijabin ta na Kai Mata ta saka,muka shirya abincin su Imrana a lunch box dinsu ta taimaka min muka futo dashi,lokacin Alhaji na zaune Yana latsa wayarsa Yana kurbar shayin da na fara Kai musu.

 

Kishatu dakin ta shige su Imrana suka karya bayan sun gama Alhaji ya rike hannun Abul da Abla suka yi waje Imrana na binsu abaya.

 

Yace min idan ya dawo anan zaiyi wanka kafin ya tafi kasuwa.

 

A dawo lafiya na masa bayan sun tafi.

 

Na kwashe kwanukan na kai kitchen na koma daki,nayi wanka nazo na tsantsara ado da wani shaddata da na karbo daga dinki kwana uku da suka wuce wajen dubu Dari biyu da hamsin shaddar take,aikin dubu hamsin,sosai Alhaji ka kashe min kudi, bana saka Karamin kaya,bani da burin daya wuce na mallake shi gabayansa duk da a yanzu ma kamar na mallake shin ne.

 

Ina cikin turare jikina da turare naji wayata na ringing ko da na duba sai naga Aunty Ama ke kirana.

 

Tsaki nayi na Maida wayar na ajiye daga shekaranjiya zuwa yau tamin miscall ya Kai dari har ga Allah na fara gajiya bazan iya ba.

 

Kira kawai take ni kuwa naki d’auka.

 

Bayan na tabbatarwa kaina na gama haduwa na fito Palo na zauna Ina Jiran zuwan Alhaji.

 

Fitarsa da minti ashirin sai gashi ya dawo.

 

Nima nasan kwalliyar da nayi na tsokana ne sai da ya goge min kwalliyar nan tsaf muka yi wanka a tare ya shirya Yana “Kasuwa fa ya dau zafi yanzu idan kika ga ban kira ba aiki ne ya kacame min,kafin na wuce can zanzo daddare anan zanci abincin dare ayi min sakwara da miyan Agushi nasan akwai komai na bukata,idan ma babu ki tura Bala ya siyo”

 

Wal nayi da ido Ina Jin ba Macen da ta Kai ni saa a rayuwa kar yaga kamar na so kaina da yawa yasa na wayance da “Ai kasan dai gobe zan karbi girki maman mujaheed ita ya kamata kace ta Maka girki ni kar ka zo ka jawo min bakin jini ma wallahi a gurinta.

 

Wani irin tsaki yaja fuska a hade yana “Ki dai yi abinda na Saka ki Babu ruwanki da wata maman mujaheed”

 

 

Ban kara magana ba yayi gaba na raka shi har wajen motarsa sai da naga fitarsa na dawo ciki na koma daki na Kara canza shigana zuwa less baki da golden daya matukar haska ni saboda Ina da haske na jera zobunan gwal dina guda uku da kudinsu ya kai ya siyi Karamin gida, a rayuwata Ina so naga Ina ado da gwall kyau nake yiwa kaina Ina Kara ganin sai mace ta Kai zata tadoni a saa.

 

Palo na fito yau Yan hirar basa Kaina da na kira kishatu tazo ta zauna mun Sha hira,amma dai bari na dubata na dawo Palo nayi zamana.

 

 

Ina kokarin tura k’ofar naji tana waya kasa kasa da “Wallahi yau hakuri zamuyi bazamu hadu ba Aunty ta min gargadi indai na sake fita wallahi korata za tayi”

 

Murmurshi na saki Ina Jin Dadi a zuciyata banza banza dai taji magana ta ko wane dan iska ne ma ya manne mata yake neman lalata ta,Ina tura k’ofar tayi saurin cire wayar daga kunnenta ta danna wayar a kasan pillow.

 

Ban nuna nasan mai tayi ba dan nasan shakkata take yi ta kuma tsorata tunda taji nace zan koreta duk danginmu bana jin akwai wanda zata je gurinsa ta sakata ta wala haka kamar gidana har ta samu Jin dadi irin wanan dole ma taji magana ta.

 

“Kin karya”?

 

“A aunty na karya”

 

“Tom zan hau sama zan zauna a palon Alhaji wajen Sha biyu ki shiga kitchen ki dora mana abincin rana.

 

Idan uku tayi zan sauko ki tayani muyi wa Alhaji girki

 

Kai ta gyada min na juya na bar dakin.

 

Ina Jin kaina a sama.

 

Sama na haye na kunna Kallo,ta karfin tuwo.na saka wayata a silent dan Aunty Ama kam bata fasa kirana ba na rasa wanan naci.

 

Naja dogon tsaki.

 

Wajen karfe goma sha daya da rabi naji an bugo k’ofar palon da k’arfi har sai da na tsorata cikin mamaki dan kishatu ma batasan ya palon Saman yake ba yarana ne kawai suke hawa sama.

 

 

Aunty Ama ce ta bugo k’ofar tana tsaye a bakin kofa tana hucci.

 

Duk da sai da naji gabana ya fadi haka na daure ban nuna tsoranta ba na zuba mata ido kamar yadda ta zubo min ido.

 

Cikin wani irin murya tace “Rasheeqa baki ga kirana bane”?

 

“Nagani Aunty Ama idan na daga bansan mai zance miki bane dan abinda kike nema bazaki samu ba”

 

 

“Wato kina ganin kirana dagawa ne ba za ki yi ba har ni zaki kalli kwayar idona kice kina ganin kirana d’auka ne ba zaki yi ba Rasheeqa”?

 

Tace tana wani irin hucci

 

Bance komai ba dan so nake na iya bakina dan bana so na zake da yawa taga rashin kunyata dan tazarar dake tsakanin mu da yawa tunda ta bani kusan shekara Ashirin.

 

 

“Rasheeqa karya kikeyi nafi karfin ki wulakanta ni na rantse da Allah koda kuwa giyar wake kika sha har nayi wanan lalacewar a wajenki da zaki ga kirana ki k’i dauka sanan nace miki Ina bukatar Abu kice bazan samu ba”?

 

Mik’ew nayi dan fa naga alama idan ban murzawa idona kwallin rashin kunya ba Aunty Ama haka zata cigaba da juyani san ranta

 

 

“Aunty maganar gaskiya nayi miki iya k’ok’arina nabi ki sau da kafa a cikin shekara shidda na bauta Miki yadda ya kamata a yanzu kuma na gaji dan Allah ki barni haka na samu nutsuwa a gidan mijina ki barni haka kafin ki jawo min bakin jini a wajen mijina a gaskiya daga yau bazaki Kara samun komai a wajena ba ki sarara min haka”

 

 

Na karashe Ina juyar da kaina dan idanunta kadawa yayi yayi jajjur har Ina iya hango yadda jikinta ke rawa ta nuna kirjinta tana “Rasheeqa ni kike fadawa maganganun nan”?….

SAI NAGA BAYAN KI

 

*NA SADNAF*

 

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

 

 

*PAGE 2*

 

Ban kalleta ba na tsaya da kyau dan bazan Kara bari ta cigaba da juya ni ba

 

Ta tako cikin palon ta tsaya a gabana jikinta na wani irin rawa da jajjayen idanun ta ta fara magana cikin kaushin murya tana “Rasheeqa nice yau kike wa rashin kunya har kina na barki ki samu nutsuwa a gidan mijinki ni Amabuwa kike fadawa magana”?

 

Jarumtaka na aro na juyo na kalli cikin idanunta dan idan ban kawo karshen wanan juya nin da take ba zan wayi gari ba ni da komai na fara magana Ina “Ba rashin kunya nake miki ba Aunty Ama gajiya nayi da yadda ki ka sa kani a gaba ki ka mai dani bankin ki,bayan kinsan ni ba aiki nake ba,duk kudin da na ke baki daga wajen Alhaji nake karba kudi kuma ba kanannu ba yau da gobe dole na gaji Aunty,tun Alhaji na bani kudi watarana dole shi ma yaga na ishe shi da karbar kudi,shekara shidda ba’a wata baki amshi kudi a hannuna ba ni kaina baki barni na samu ko dan kudin na tara ba kinci iya rabon ki ki barni nima naci rabona Aunty shine kawai ba batun rashin kunya”

 

 

Ja da baya tayi dama idan ranta ya b’aci jikinta rawa yake ta kasa tsayawa ni kuwa na koma na zauna ta hau zagaye palon sai da ta gaji ta tsaya a gabana tana “Ni zaki yiwa butulci Rasheeqa Yau bani na zama silar da kika taka wanan matsayin ba?bani na nemo miki Alhajin kika aura ba?

 

“Ko baki Nemo min shi na Aura ba mijina ne kuma ai ban roke ki ki nemo min mijin Aure ba,kuma ai baki fada min kina da manufar daya Saka kika jajirce wajen tsayawa na auri Alhaji ba Aunty Ama kefa yayata ce ba haifata kika yi ba da zaki ce lailai sai na Miki biyayya kin tsara min yadda zanyi da rayuwata,idan ma taimakon da kike ganin kinyi min zan biya ki ai na dade da biyan ki daga aurena da Alhaji zuwa yanzu ke kan ki ba za ki iya lissafa kudin da na ba ki ba,ko ta silarki ko bata silarki ba Allah yayi Alhaji mijina ne tunda gamu da Yara uku Abu kadan sai ki hau yimin gori toh a gaskiya na gaji ki barni na sha iska sisi bazan Kara badawa ba,mijina ba a kasa yake tsinko kudin ko bai San zafin kudinsa ba da zaki ringa saka ni karbar kudi Ina baki ,har kyautar gida da mota ya miki ni na baki kudi bazan iya lissafa wa ba idan ma kadara zaki yi ta siya kudaden da nayi ta ba ki ya isa ya siya Miki kaddara da yawa na gaji bazan Kara bada ko biyar dina ba”

 

 

Nace Ina hucci

 

Aunty Ama da na kasheta da mamaki taja baya ta fara tafi tana “Ba shaka Rasheeqa wuyan ki ya isa yanka dole ki fada min maganganu kin manta ba dan na dauko ki a kauye ba da kina can kina haifar yayan shegu kina bin Yan talla suna dirka miki ciki,kin manta da yadda na dauko ki na kawo na raine ki na tsaya tsayin daka ko Yar dana haifa a cikina ban mata abinda na miki ba,saboda ki kawo matsayin nan ni nasan kudin da na kashe da wahalar da na sha akan ki kin manta kalar rufin asirin da na miki,saboda ke na shiga daji sai da na samu kwana uku nayi kazamar rayuwar da ko makiyina bana masa fatan yayi,na shiga na fita kika kawo matsayin nan sakayyar da zaki min shine ki butulce min,kimin rashin kunya akan kudaden dana san basu taka karya sun karya ba kike wulakanta ni,kudin da ba’a Aljihunki zai fito ba a Aljihun mijinki zai fito Wanda ni nasan kamar naira goma yake a wajensa shine zaki wulakantani Rasheeqa”?

 

A fusace na fara magana Ina “Na gaji Aunty Ama da anyi abu kadan sai ki hau yimin gori naga ni da ace nasan badan Allah duk kika min abinda kika min ba wallahi bazan yarda ma ki dauko ni daga can ba daidai da allura da kika siya min kimin gori kin siya min,idan ma biyanki kike so nayi a cikin shekara shidda ai na biyaki har da riba wallahi dan haka Dan Allah ki rabu dani tunda ba haifata kika yi ba kije ki samu kubura ki cigaba da juyata ni dai kam wallahi sisi bazan Kara badawa ba kinci rabonki haka Ina dalili zaki matsamin da takura da gori,kuma ko baki nemo Alhaji ya aureni ba kema Kinsan zan samu Mai kudi da zai Aureni”

 

“Haka kika ce Rasheeqa,Yau Alhaji da kika samu a tafin hannunki ya zama bai San kowa ba sai iya ke da yaranki ko kinsan nice sila?

 

Ko kinsan nice nan na shiga na fita yaji duk duniya ba wacce ya tsana sama da uwar yayansa na Sha wahala wajen ganin baya ganin kowace mace a gabansa sai ke.

 

Kinsan irin rayuwar.kunci da wahala da uwargidansa ke ciki ita da yaranta Rasheeqa kinsan kalar wahalar da na sha kafin kizo matsayin da kike ciki yanzu har wuyan ki yayi kaurin da Zaki kalli kwayar idona ki fada min maganganu”?

 

“Ban roke ki ba Aunty Ama duk abinda ki ka yi ke kika Saka kanki kuma na dauka dan Yaya tayi wa kanwarta abu ba wani Abu bane bansan ke kina da manufa akan taimakon da kika min ba, bansan cewar ba Dan Allah kika taimaka min ba duk abinda ki ka yi ke kadai ki ka je kika yi ba Abunda ya dameni na kuma fada miki na gaji idan ma wahala kika ce kin. Sha ai na biyaki har da Kari ma dan haka ki sarara min haka ehe”

 

“Rasheeqa ni Amabuwa da kinsan zan iya haifarki kike gaya wa magana ni Amabuwa da nake yayar ki da kafin ke Akwai Nura Saeed Faruq Bala kafin ke ni kika tsaya a gabana kike fadawa duk maganar da tazo bakin ki yau da Babu ni da baki Isa ma Jiyo kamshin inda kike ba yau,saboda kin samu duniyar da nice silar samun sa Zaki kalli kwayar idona kin manta a yadda na dauko ki Rasheeqa nice wulakantaciya a wajenki?

 

Tsaki nayi nace “Ke kika wulakanta kanki kika nuna zallama da kwadayinki ni da Auren Alhaji ke da juyani san ranki ki barni na zauna Lafiya a gidana ki rabu dani”

 

Wani irin girgiza kai tayi ta share hawayen da ya zubo mata zan iya cewa tunda nake ban tab’a ganin ta cikin b’acin rai haka ba balle har na ga hawayenta dan ko lokacin da Ammi ta rasu banga tayi kuka ba,har ga Allah ta isheni tun Ina Mata Al kunya sai da ta kaini bango.

 

Sai da ta gama share hawayen ta,ta daga hannun ta sama tana “wallahi wallahi kinyi da Yar Halak Rasheeqa yadda kika butulce min kika sakani zubar hawaye kika tusa min bakin ciki wallahi wallahi sai na Miki fiye da abinda kika min wallahi indai Ina Rayye sai naga bayan ki indai Ina rayye sai kin wulakanta ko da zanyi yawo tsirara Rasheeqa sai naga kin fito daga wanan matsayin daya saka kike ganin kin Kai ki kalli idona kimin rashin kunya sai kinyi bara a titi kin rasa mai taimakon ki”

 

 

“Bakin ki ya sari danyen Kashi Aunty Ama baki Isa kimin abinda Allah bai yi min ba ba abinda Zaki iya min wahalar banza zaki sha kuma ko ciwon Kai nayi wallahi wallahi sai na saka an kulleki tunda naga alamar ke jahila ce nayi Aure ki hanani zaman lafiya a baya ma da na ringa binki bana Jin a hayyacina nake amma yanzu na dawo hayyacina sisina ba za ki kuma ci ba kuma bara da kike cewa zanyi ke zaki yi bara Bayana da kike cewa Zaki gani sai dai naga naki dalla fitar min a gida”

 

Nace a tsawace Ina hucci

 

Kallona kawai take tana hucci kamar yadda nake yi tana girgiza kai ni kuwa na Kara fada a haukace Ina “kifita nace”

 

Juyawa tayi ta nufi kofa ta juyo tana “Ni Amabuwa kike kora Rasheeqa wallahi sai naga bayanki ko da kuwa zan shiga wuta,kuma wanan sirrin naki da baki so kowa yasani sai na bankada wallahi sai mijinki yasan irin raywuar da kika yi a baya”

 

“Idan kin cika Yar Halak ki bi shi kasuwa ki fada masa yanzu kema ai kallonki nake nasan boyayyen sirrinki da kalar rayuwar da kika yi a baya daidai nake dake duk ta inda kika bullomin kuwa ki tona nawa sirrin kema na tona ki da kike tunanin ba Wanda yasani kinga sai ki shirya kisan yadda zaki yiwa yayanki bayani”

 

 

Cak ta tsaya tana kallona kamar yadda nake kallonta Ina Jin tsanarta tabbas da zamuyi kokawa zan iya caka Mata wuka banyi nadama ba, girgiza kanta tayi ta fice Ina Jin saukarta da sauri.

 

Na bi bayanta na tsaya daga sama Ina kallonta har ta sauka batare da ta ko Kalli kishatu dake tsaye a bakin kofa dana san hayaniyar mu, ya fito da ita daga daki.

 

Naja tsaki dana ga ta fice na zube a kujera na kwanta Aunty Ama yayata ce uwar mu daya uban mu daya itace babba a gidanmu daga ita sai Maza hudu sai ni,Ina karama mahaifinmu ya rasu mahaifiyata sai da ta shekara bakwai tana zawarci kafin ta auri mahaifin kishatu da tun kafin ta haifi kishatu shi ma ya rasu daga nan mahaifiyata ta hakura da Aure.

 

Tun banida wayo Aunty Ama tayi aure aka kawo ta Nigeria dan anan Niger muke asalinmu buzaye ne daga Jin haka kunsan indai kyau ne sai dai wannan ta Fi wanan amma duk a cikin mu kishatu tafi kyau dan mahaifinta dan Ethiopia ne shi yasa bata kama da mu kamanin ta daban.

 

Aunty Ama ba laifi tana da zumunci da san nata ba tayi karya ba da taimakon ta na kawo matsayin nan amma bazan iya jure halinta ba na gaji tabbas ta taimakeni a lokacin da nake cikin halaka nake rayuwa cikin duhu,da bansan yancin kaina ba amma ba hakan shi zai saka ta ringa juyani kamar waina a tanda ba.

 

Wayata dake ringing ya katse min tunanin da nake

 

Ganin Alhaji ke kirana yasa na d’auka Ina dagawa yace “Kun dora abincin ranan ne?

 

“Aaa yanzu nake so na sauka na Saka kishatu ta dora mana ko jollof ne”

 

“Tom ki bari ba sai an dora ba idan na dauko yaran sai mu shirya mu fita na hutashe ki ko”?

 

Murmurshi na saki Ina “Tom shikenan Alhajina sai ka karaso”

 

Sai da ya kashe wayar maganar da Aunty Ama tayi ya fadomin,na wai ita tasaka Alhaji ya tsani matarsa ya zama baya ganin kowa sai ni,har ga Allah bansan itace ta asirce Alhaji ba,na dauka tsabar san da yake min yasa baya daraja matarsa Wanda kasan zuciyata gani nake ba daidai bane amma San zuciya da san Kai yasa nake Jin dadin yadda yake mata,idan alhakine ma ita zai kama bani ba.

 

 

Karfe daya da rabi naji dawowarsu bana Jin Ina bukatar na canza kaya sai dai na Kara murza hoda su Imrana kawai zan shirya.

 

Saman suka hawo gabadaya suka sameni.

 

Sai da na rungume Abul da Abla da suka kasance Yan biyu ba inda suka dauko Alhaji fari da kyau duk nawa yarana suka d’auko dan Alhaji bakine ba Karamin ji dasu yake ba,musamman yake yawo dasu ma wai Dadi yake ji ace wadanan fararen yayan nasa ne.

 

Idan yace haka nakan yi murmurshi dan na taba ganin matarsa sau daya baka ce tunda shi ma bakine nasan dole yaransa duk bakakke ne.

 

Cikin minti goma Sha biyar na shirya yarana cikin kaya masu tsada na tura Imrana wajen kishatu akan yace mata ta shirya zamu fita cin abincin.

 

Alhaji ma sai da ya sake wanka ya canza kaya muka sauko kasa gabadaya na fara kwallawa kishatu kira.

 

Ta amsa daga daki akan gata nan.

 

Mayafina na Kara gyarawa a kafadata Alhaji ya rike hannun Abul da Abla da na raba Mata gashin ta biyu

 

Yana ta wasa dasu,karar Bude kofar dakin kishatu yasa muka Kalli k’ofar sai gata ta fito cikin shigar atamfa riga da skirt ya matseta ta saki gashinta har gadon baya bata daura dankwalin ba sai bulbula kamshi take,wani irin Kallo na mata take naji nama raina kaina, dan ba Karamin kyau tayi ba karyane ta wuce baka kalleta ba.

 

Alhaji kuwa na saci kallonsa sai naga ba ita yake Kallo ba Abla ma ya d’auka yayi gaba “Yana mu tafi ko”

 

Suna yin gaba nacewa kishatu “Kiyi zamanki ba sai kinje ba zamu yo Miki take away bai dace ma Abar gidan ba kowa ba”

 

“Dan Allah Aunty ki barni na biku zaman gidan ba Dadi wallahi”

 

“Wallahi ba inda zaki je ki zauna kawai”

 

Nace cikin hade rai nayi waje ban ko Kara kallonta ba”

 

 

Ina zuwa na Bud’e motar na shige Ina “mu tafi ko”

 

“Ina kishatun”?

 

“Nace ta zauna ma yi Mata take away”

 

Ido ya zuba min na hade rai bai ce komai ba ya tada motar muka tafi.

 

A hankali Alhaji ya ringa tuki,yana ta hira dasu Imrana ni kuwa fadan da nayi da Aunty Ama ne ya ringa dawo min.

 

Sai da muka tsaya a danger na dawo daga tunanin da nake kafin a bamu hannu na hango wasu Yara su hudu Maza biyu mata biyu sun nufo ta wajen da Alhaji yake.suna sanye da kayan makaranta ido na zuba musu Ina mamakin Mai yasa suka nufo wajen motar,da alama Alhaji Sam bai lura dasu ba,har sai da Matan suka karaso mazan na daga dan baya naji karamar tace “Abba”

 

Alhaji juyawa yayi ya kalleta yace “Ummi dama baku koma gida ba har yanzu”?

 

“Eee Abba da kafa muka taso yau Umma bata da kudi bata bamu na mota ba”

 

Mamaki da Alajabi ne ya kasheni a zaune idan dai zan gane Mai ke faruwa wadanan yaran yayan kishiyata ne suka Sha bakar Rana suna zuba gumi,Alhaji kudi naga ya dauko daga Aljihunsa Ya mikawa wacce yake cewa Ummi “Maza ku samu abun hawa ku tafi gida”

 

Yarinyar sai taki karba tana “Abba ka kaimu gida a motarka”

 

Alhaji na k’ok’arin magana wani da naga suna kama zaiyi shekara goma Sha hudu ya zo ya rike hannun yarinyar Yana “Kizo mu tafi sai na goya ki”

 

Bai ko Kalli Alhaji ba ya sunkuya ya dauki yarinya suka fara tafiya Alhaji ya Maida kudinsa a Aljihu ya fara k’ok’arin Jan motar ni kuwa na kasa hakuri sai da nace “Alhaji wanan yaran ba Yayanka bane”?….

 

 

Paid book 500 via 0078986629 sterling bank nafisa nuhu or recharge card Tru this 08068484400 evidence of payment Tru this 08033719070

Close Menu