Da Ciwo A Zuciyata Hausa Novel Complete
DA CIWO A ZUCIYATA*
_MALLAKIN_
*SAJIDA NIJAR*
*FREE BOOK NE* 1️⃣
LITATAFAN MARUBUCIYAR
Duk karyar kada
Yar mahaukaciya
Neman na kaina
Bani da zabi
Bak’a ce
Kutkale
Makauniya ce
Mage
Duk nisan jifa
Idan ka raina inda kake
Dutse
Alkalamin kadarata
Bani da zabi
Dakika Biyar
Now
*Da CIWO A ZUCIYATA*
*Tallah, tallah, tallah*
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_
Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicé
Lait de nuit
Parfums désodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*WaÉ—annan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al’ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes
Tukuicin Gata Hausa Novel Complete
*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata
Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan number 97 82 44 94
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata💃💃💃💃💃
Tunda suka yi sallar asubahi suka yi aduo’insu kamar yadda suka saba ita ta koma ta dan kwontar da hakarkarinta, domin dama ta cika dare ne sosai tana bitar karatun jarabawar da zata gabatar a yau din a makaranta wace daga ita in sha Allah kuma sai ta karshe wace sunna yi zasu samu damar fara zuwa asibiti dan kula da mararsa lafiya ko nace koyon aikin jinya kafin su rike makamin kula da marar lafiya………, Yan uwanta kuwa su biyun watau RUKAYA da AISHA sai suka shiga hana habarsu kamar yadda ya zame masu jiki kama daga gurje tafin kafa, wanka da wuri dan gyara fuska da dai sauransu a matsayinsu da matasan yan mata masu ji da kansu da tsarin kyau daidai nasu da kuma iya wanka dan samun cikar burinsu watau birge wanda suka san sunna iya birgewa a hanyarsu ta zuwa ko ta dawowa daga makarantar summa
Sai da karfe bakwai ta yi mahaifiyarsu ta dage labule sanye cikin zumbulelen hijabinta wanda ke yi kamar zai tadeta ta fadi ama kuma baya tadetan dan damatsunnan hannayenta ke dauke shi da zarar ta motsa ta fan leka kanta tana kallonsu da dan murmushi ta sake amsa gaisuwarsu sannan ta ce” Oh Allah, ana nan ana fama da hodar ? Ina ita dayar take ban ji motsinta ba bayan tace jarabawa ne da ita yau din?”
Firgigit ta farka a barcin da take yi, mundul taundula daga saman shamakakiyar katifarta wace kwonciyar da ta yi a sama ta sake matse katifar sosai ya zamto ta takure sosai katifar dan dama ba wani auki ne da katifar ba gashi kuma ta hayeta ba ko dan juyawan nan
Hularta ta laluba ta warto ta kabeta ta dora saman gashinta da bai fi kamu biyu ba dan bata da tsayin gashi sai cika sosai a kanta sannan ta kama ta mike daga zaunen da ta yi da abin magagin barci ta kalli Aisha ta ce” Karfe nawa ne Aishe?”
Aisha ta duba yar karamar wayarta ta sanar mata bakwai ta yi, ta dora da fadin” Bamu tasheki ba dan ko takwas saura kika farka ba lati kike yi ba tunda wankan kawai ne kike yi”
Ita dai da sauri cikin yannayin halitarta wace kana iya tunanin idan har ta motsa to fa da shasheka zata yi motsin, sai dai abin mamaki jikinta da ya fi shekarunta bai hanna mata motsawa da kaza kaza ba ta yi bayi tana hangen Mamanta na batse mata bokicin da ta ajiye dan jan ruwa a rijiyar gidansu ta duba sabulunta yana nan dan haka da gudu ta fito ta kinkimi ruwan ta yi bayin da shi ta ajiye abinta sannan ta shiga tubewa dan yin wankan
A wajen wankan ne kawai ta dan dauki lokaci, dan akoyta kale kalen jiki irin na tsaftar jiki, koda yake sai ta yi anfani da lemun tsami ta darji hamatarta da du wanu lungu na jikinta wanda ke iya daukan gumi har ya bada wani wari daban irin na jikin dan adam bale ita mai tsoka a jiki masha Allah, kafin take yin wankan ta fito cikin sauri ta yi dakinsu ta warci uniforme dinta dake saman kujera ta kabe ta shiga zurawa bayan ta saka rigar mamanta da kafcecen pant dinta sannan ta zumbula hijabinta ta sake tsalake yan uwanta da har yanzun basu gama nasu shirin ba tana murmushi ta daga masu hannu da fadin” By sisters, sai mun hade”
Rukaya ta dago ta fara zuba idannuwanta a takalman da yar uwar tata ta saka takalma ne yan soso plat sun shamuge abinsu , bayan tana da takalma taki biyu bayansu ama dan yau tana jarabawa abin ya karra kwabewa takalmin kirkima ba zata tsaya ta saka ba haka zata tafi
Kai kawai ta girgiza domin ta san ba sauraronta zata yi ba in dai ta wannan fannin ne , ita a nata tsarin rayuwar tun da ta gama fahimtar rayuwarta ta gane me take ciki ta yi waje ta ajiye abubuwan nan gefe , ta riga ta sani ne bata lokaci ne a gareta ita, dan haka ta fi dauko fannin da zai gyarata wanda zata iya birge kanta da kanta da kuma Wa’inda ke tare da ita, shine karatunta da kuma nema cikin tarin rashin gajiyawa da rashin son jikin da Allah ya yi mata a cikin irin nata ni’imomin itama
Dari biyu yau aka bata, hakan ya sa take tafe tana sakin murmushi da irin tafiyar nan ta gagawa dan a hasashenta in sha Allah minti ashirin da uku zai sadata da ajinta hakan zai yi mata sauran minti goma sha takwas kafin a shiga aji kennan zata karya abinta kafin ta shige, wanda makarantar ke dan nesa da gidansu kadan ama kuma baya mata nisa dan ita a kafa take tafiyarta ta kuma dawo abinta, yan uwanta ne ke bata mamaki, tasu makarantar ta fi kusa da gida fiye da tata , ama idan ka ga sun yi tafiyar kafa ranar tai masu daren kure ba gaba ba baya sai gyaran ubangiji kawai
Cikin saurinta ta karasa wajen aunty mai dambu ta zaro dari biyunta ta mika mata ta sanar mata dambu na saba’in zata maka mata tana ta sakin murmushi tana bin hannun Aunty mai Dambu dake zuba mata da kallo, ta sani ne yau zata kile abinta dan kuwa mai cin na arba’in ya kara talatin ai zai more iya morewa
Zama ta yi nan ta wanke hannu ta maida hankali ta ci dambun nan sannan ta sayi ruwa daya ta shanye tasss kafin ta mike tana sauke ajiyar zuciya hadi da sakin murmushi domin hankalinta ya kwonta bata da matsala da cikinta takarda kuwa a je a gabza cen dama ba matsalarta bace , watau karatu
Kasancewar ranar jarabawa ce, wa’indama basu cika zuwa makarantar ba, da masu zuwa a lati du sun iso tun kafin a shiga, hakan ya sa makarantar ta cika da wuri inda hankalin daliban du ya kakasu gida gida, domin karara zaka ga halaya uku a tare da daliban mabambanta,
Wasu zaka ga hankalinsu Kwonce yake dan sun sani sun dauka sun kuma yi iya kokarinsu sun riga sun sani idan sun shiga ajin nan da izinin Allah ba zasu fito a tutar babu ba, watau ko yayane zasu dauki na dauka ko su cinye baki daya
Wasun zaka ga sunna ta fama da bude litafi sunna ta bitar abinda ba zai zauna masu a kai ba, saima ya zubar da dan wanda suka cika dare sunna dauka domin dama basu cika leka litafin ba sai irin wannan dama ta samu ta jarabawa, sai ko daidaikun da zaka ga wayarsu ce a hannunsu hankalinsu kwonce, yawanci ya’yan baba da rai ne da suke tunanin tunda babansu ya tara to fa basu da matsala da damun kansu da yin karatu ko faman fafutukar samun takarda , wannan din ba shine a gabansu ba, gidansu an tara a yi sama a yi kasa su kam sun san ko abokin baba ne zai basu aiki a wajen da ya dace da su, shi yasa basu da damuwa a abinda zasu tarar na jarabawar su ci ko su ki ci matsalar wanda ya daurawa kansa matsalar ne, kai hasalima sun zo makarantar ne dan kar a yi masu fada a gida dan iyayensu ne ke so su yi karatun ba wai su ba!
Hankali Kwonce ta nufo hanyar ajin nasu, inda yawancin daliban suke, tana tafe tana dan gaisawa da kusan du wanda ta hadu da shi faran faran da murmushinta domin ita dai ba gwali takeda na son birge wani ba, bata kuma zo makaranta dan ta birge wane ko ta bata da wane ba, wannan shiriritar ba da ita ba, to ita batama ga anfanin hakan ba sam, ana ta kai wa yake ta kafa in ba shirmen wasu daliban bama……………..
“Abokina, ga fa mutuniyar cen tafe, ka ga kamarma sidar hannu ake ko me aka samu da safiyar nan?” Kamal ya fada yana dan murmushin shakiyanci yana kallonta da irin tafiyar da take yi ba abinda ya dadata da kasa , bata da damuwar komai sai ta abinda yake gabanta, wanda hakan abin mamaki ne a wajen samari da yan matan yanzu, duba da irin yadda kowa ke rike da nasa akidar na kin raini, da É—orawa kai abinda ya fi karfin kai dai da sauransu………..
Fuska ya dan gimshe ya kalli inda take zuwan sannan ya maida dubansa kansa fuskarsa a dan gimshe ya ce” Ka fa san bana son haka ko? Na sha fada maka ka mutuntata ko ka shafa mata lafiya, kowa ya yi ta kansa ko?”
Zai bashi amsa ta karaso inda suke tsaye fuskarta dauke da madaukakin murmushin gannin ya ji maganarta har ya zo din kamar yadda ta masa maganar jiya da yama da suka rabu daga wajen exercice cewar ya tabata ya zo aji a kan lokaci ya kuma yi exam din nan a cike kar ya saki ya ki zuwa fa?
Tsayawa ta yi dan daf da shi ta ce” Bani abin kunnen bawan Allah?”
Murmushi ya yi yana fan shafa bayan kansa ya cire abinda ke cikin kunnensa ya mika mata da wayarsa kirar iPhone 11 pr ita kuwa ta kashe ta bude jakarta inda ta san ba zata fashe ba ta saka masa a ciki sannan ta rufe ta sake dubansa ta ce” Ka dauki shafukan fa na fada maka jiyan kuwa?”
Shnayayun idannuwansa ya dan bude kamar wani mai shan abin maye bayan babu abinda yake sha haka yannayin idannuwansa suke ya dan kalleta kadan ya kuma gyada kai, shi fa du ba wannam bane a gabansa, abinda yake gabansa aikin da Mahaifinsa ya saka shi yace kuma karfe takwas da rabi ya zamto yana bakin shagonsu na wajen sabon gari dan a sauke kaya a gabansa ya kuma daidaita komai , yau dai wunnin yau sam bashi da wani lokaci gaskiya, shi yasa ya yi safiya ya zo dan baya so su raba hali saboda jarabawar nan, idan dai ta ga ya zo ai ba zata ji haushi ba ko ta yi fadan bai zo ba yana wasa da karatu
Da jin dadi ta yi gaba dan duba sunnanta ta barsu ko ci kanka bata cewa Kamal ba, haka shima da ido ya rakata kafin ya dauke kai yana girgiza kansa yana tunanin ta yiwu tun fadan da aka yi ne bata masa magana take masa gaba, bai sani ba cewar ita ba maganar gaba a cikin tsarin rayuwarta ,idan har ta kula cewar zamanta da kai akoy wani abu mai kama da wulakanci ko cin zarafi ne zata janye jikinta cikin salama ba tare da ta yi naci ko ta dorawa kanta abinda zai dameta ba,
Hasalima abokin nasu da suke takama da shi shine ya yi mata nacin son kasancewa aboki a wajenta itama, daga wannan bata tunanin akoy wani abu da zai sa ta zamto abokiyar gabarsu, ko fadan da aka yi budurwarsa ce take tunanin meye tsakaninsu haka? Kamal din wajen fada mata bafa soyaya sai ya yi aiki da munanan kalamai da suka sa ta daina gannin kimarsa….., Lalle ita talaka ce, ama a cikinsu ai talakawan da yawa,haka kuma yannayin jikinta ita baya damunta dan ta san Allah ya haliceta haka , haka kuma yake son ganninta, bata tunanin wani bawa zai iya tsayawa ya zageta a duniya dan kawai ita din tana da jiki da ake kiranta da yar lukuta saboda shi, ba kuma ta tunanin bata je neman alfarmar wani wani ba zai wulakantata ba, idan sun kula zumunci ne da zamani yazo da shi tsakanin namiji da mace na abotaka, nata kawancen bai kaucewa tsarin adininta ba domin akida gareta shi kuma yana da addini, layin rayuwarsu ba daya bane dan shi yana zuwa makaranta ne dan yaki da jahilci , dauke kewa, jin dadin mu’amala da jama’a, inda ita kuma take karatu dan samun abin sakawa a baka gobe idan Allah ya nufa!, Ita karatu ne take yi da dukkan karfinta dan bata da madafar da ta wuce bin abinda ya dace dan ta samu rabauta itama da nutsuwar zuciya, shi kuwa wadinnann ya dade a cikinsu domin ya
*DA CIWO A ZUCIYATA*
_MALLAKIN_
*SAJIDA NIJAR*
*FREE BOOK NE* 2️⃣
LITATAFAN MARUBUCIYAR
Duk karyar kada
Yar mahaukaciya
Neman na kaina
Bani da zabi
Bak’a ce
Kutkale
Makauniya ce
Mage
Duk nisan jifa
Idan ka raina inda kake
Dutse
Alkalamin kadarata
Bani da zabi
Dakika Biyar
Now
*Da CIWO A ZUCIYATA*
*Tallah, tallah, tallah*
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_
Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicé
Lait de nuit
Parfums désodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*WaÉ—annan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al’ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes
*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata
Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan number 97 82 44 94
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata💃💃💃💃💃
A lokacin da ta shigo gidan kowa yana nan
Bata tsaya tsaye tsaye ba alwallah ta daura kawai ta shige dakinsu ta zauna ta bude litafinta tana yi tana kallon yan uwanta dake hira da makociyarsu wace ta shigo su kuwa sunna tsakar gida da mamansu sunna tataunawa kan shirye shiryen auren y’arta budurwa
Aisha ce ta kula da yannayinta domin sosai yannayin nata ke nuni da ranta a bace yake, dan haka da kula ta ce” Hajia sister wai waye ya tabo ki haka?”
Kallonta *KAUSAR* ta yi a hankali , sai kuma ta kalli inda mamansu ke fadin maza Rukaya ta fito ta zuba masu abinci su ci
Dan sa’ida ta ji a ranta, domin har ga Allah tafiyar da ta yi dambun nan gaba daya kamar bata ci komai ba take ji, du ya yi kasa, dan haka ta kasa ba Aisha amsa har Rukaya ta zubo abincin ta shigo da shi dakin lokaci daya kuma suka mike sunna fita dan Maman ce ta shiga fadan kar su kumkume daki su ci abinci
Du a tsakar gidan suka zauna saman tabarma da kwanon da Aisha ta janyo masu ruwan rijiyar ta ajiye sula shiga cin abincin a cikin kwano daya gaba dayansu cikin nutsuwa
Ajiyar zuciya makociyar Mama watau maman Naïma ta sauke a ranta tana jin tausayin Maman da Æ´aÆ´anta……., Har ga Allah abin a tausaya ne idan aka yi dubi da yan matan sun fa kai sun kawo ama shiru ko daya ba’a aurar ba, su jira suke yi KAUSAR ta samu miji, wace idan har rayuwarta za’a zauna a duba babu wannan tsarin a cikin tsarin rayuwarta……., Babu wanda zai ce yau ya taba gannin saurayi a matsayin na KAUSAR, yarinyar kamar wata mai bakin aljani ita din da kantama bata da alamun ta damu da wata magana ta d’a namiji a rayuwarta, wani fannin kuwa har ga Allah ana yi mata duba ne na wace bata bada wani dan motsin da zai nuna cewa ta dan itama mace ce tana cikin layin mata a rayuwa ba, ko me yasa ta zabi gabatar da rayuwarta haka? Allah masani
Sunna nan zaune har yan matan suka gama cin abincin, cikin gagawa ta shirya ta daura alwallah ta dauki salaya ta saka a jakarta ta kuma daukan hanya domin safe da yama ne jarabawar kwana uku
Ta yamar ma bai zo ba haka ta sake shako wani takaicin harda yiwa kanta fadan in sha Allah ba ita babu shi, tunda a zamantakewarsu ba zata iya fada masa magana ya dauka ba, tunda bata isa ta nuna masa mahinmancin karatunsa ya gane me take nufi ba, ita har yanzu ta kasa gane ina ya dosa , in karatun ne baya so ai ba dole ya yi zamansa mana a gidansu? Ama sai ya wani dauko kafa ya zo makaranta ya koma har gashi yanzu ana cikin lokaci mai mahimmanci wanda idan baka samu abin kirki ba to fa ka san me ka shekare kana yi shi bama zai zauna ya yi ba? Tana matukar jin takaicin rashin maida hankalinsa a kan karatu kamar yadda zata iya ji a kan yan kannenta A’isha da Rukaya, bale dai shi da yake biyan makarantar nan mai masifar tsada, ita kanta da ta samu shiga saboda kyan sakamakon jarabawar shigar da takardunta suka yi bata wasa sai shine zai yi wasa?
Haka ta yi karatunta bayan sun ci abinci ta shige da wuri ta yi sallah ta yi kwonciyarta domin yau ko abanta ba zai sameta ido biyu ba, haka take idan ana jarabawa bata da lokacin kowa sai an gama
Bayan an yi sallar asubahi mamansu na zaune tana jan carbi abansu ya dawo daga masalaci
Datijo mai mutunci da daraja, mutun mai karamin hali ama mai wadatar zuci, mutun mai daraja iyali da iyawa talaucinsa a kan muradin iyalinsa na yau da kulun, Abansu mutun ne mai zuciyar nema , yana siyar da turare ne kama daga na feshe har zuwa na haki, yana hi kasuwanni da ma’aikatu da kayan tallarsa ya rabawa masu siya kama daga masu daukan bashi masu biya har zuwa zuwa masu dauka na bakin hanya ciniki yanzu biya yanzu
Ya kasance mai saka riba kadan ya saka albarka shi yasa rana ba zata fito dare ya yi bai samu abinda iyalinsa suka ci suka yi yan bukatun yau da gobe na rayuwa,
Tukunya dai ukun nan ana dorata a gidansa kofa kuwa ruwan koko za’a dora a yi kari sai an yi shi , basu da mandar abinci bale na ruwa ko na sabulun wanke dati……, Sai kuma Allah ya taimakeshi matarsa macece da ta iyawa talaucinsu
Bata da kwatamniyar fade faden abubuwan da suka fi karfinsu bale har ya dawo neme nemen abinda ya fi karfinsa, ta kasance mai talafa masa ce da dukkan hanyar da Allah ya bata dan su ji saukin rayuwa, domin tun daga kan awon masara, hatsi, ko yar shinkafa zuwa sabulun wanka, omo , clean da dai sauransu idan ya kawo ya ajiye har sai ya karro wani da tunanin na gidan ya kai karewa sai ya ga da saura….., Bai taba zuwa gidansa ya tarar da tari tarin abinci banzace a yashe kamar ba nema ake yi ba, bai taba gannin guntatakin sabulai na yawo a cikin gidansa a zubde ba, komai a kilace komai a adane daidai karfinsa, hakan ya sa tafiyarsu cikin rufin asiri da taimakon junna ne, zamansu kuwa bayan Adu’ar gamawa da duniya lafiya sai fatan a je a samu baban rabo gobe kiyama…….
Shi dai Abansu bashi da kiba ko kadan, domin lange lange yake kamar zai rabe biyu, mamansu ce mai jiki sosai, dan ifan har jerawa zasu yi ba zaka taba hango abansu ba in ta yi tsaye……a haka tafiyarsu take tafe cikin aminci da tsarin addinin islama, inda Allah ya azurtasu da ya’ya hudu , mata uku dai auta namiji
Da salama ya shige dakin ya karasa ya shiga fitar da kwalayan turarukansa yana ajiyewa gefe , ga dakin Mamansu ta kunna dan turaran haki ya gama dakin da kanshi masha Allah
Shafa fatihar ta yi sannan ta ciciba ta mike ta karasa wajen kayan da ya zo da su jiya ta dauko ledar da bai mata bayaninta ba ta kawo ta ajiye sannan ta duka tana gaishe shi kamar yadda al’adun malan bahaushe mai nagarta yake
Da kula yake amsata da yi mata yan tambayoyin gidan da yaren, itama ta amsa shi sannan ta ce” Aban KAUSAR ledar nan baka min bayani a kanta ba”
Ledar ya dan Æ™alla yana cirewa yaren turarukan daidaya masu kyau da tsada ya ce” Au na manta, na KAUSAR ne”
Dan murmushi ta yi tana kuncewa ta ce” Bara mu ga me yar gatan Abanta ta samu ne?”
Shima murmushin ya yi ya dan dakata da aikin da yake yi yana kallonta yana kuma jiyo kiciyar ya’yan nasa a tsakar gida ya san abin kari suke shiryawa da kuma shirin school ya ce” Kayan kwaliya ne jiya a shagin elhaji na ga wata mata na siyawa y’arta, y’ar yadda kika ga Kausar dina ana ta siya mata su nima nace a bani abinda aka basu kin ga takalmin nan mai dan tsayi kuwa? Zai yiwa KAUSAR kyau , harda wata shada nacewa Elhaji a yanka min yafi goma sha takwas karshen wata zan kai kufin mu ci sallah da ita in sha Allah”
Mama fuskarta bata gushe da murmurshi kawace a kai ba tana ta dagawa duda abinda take sakawa daban a zuciyarta shine addu’a da fatan gannin wata rana KHAUSARma ta fara gabatar da rayuwa irin ta yan mata, irin yadda mahaifinta ke kokarin nan yana son lalle lalle shima babar yarsa sai ta zamo kamar yan uwantan nan ta san burinsa daya ne Allah ya nuna masa ta samu miji ya aurar da ita ko ya fuskanci kannenta da suke da manema tuntuntuni…., A yanzu dai a kasar hausa shekara ashirin da hudu zuwa da shida ai an kai a shiga dakin miji, sai dai halin rayuwa da kadarar bawa idan har Allah ya yi mijin bai samu ba dole a yi hakuri a yi ta addu’a
Tana murmushin ta ce” Allah ya karra budi, ya karra rufa asiri, to ina na yan matana kayan kwaliyar ?”
Murmushin ya yi shima ya ce” yan matanki rasawa suke, inace ba’afi sati biyu da suka ce hodarsu ta kare ba har nace da Aisha ni indo hodar nan ko barci za’a shiga fai badata ake yi kau?”
Mama na daria ta ce” Kai, ai Æ´aÆ´an nan sunna son kwaliya nu har mamakinsu nake yi, koda yake kwaliyar ai da ranarta gashi du sun samu manema , ama ita hajiar ba ga kwaliyar ba , ba ga dandasa gayun ba, ita dai barta da takarda da byro abinta”
Murmushi kawai ya yi , hakan ya sa ta sake tausasar da muryarta, domin abinda ta kwana da shi har ya saka ta kwana tana juyi kennan, maganar ya’yan nasu
A tausashe sosai ta ce” Abansu ina so mu tatauna wata magana ni kam”
Ajiyewa ya yi ya fuskanceta ya ce” Ai tunda na ga an ki fita a kamawa yayana aiki an bar min yan muleka da shara da wanke wanken asubahi na san da magana, yi bayaninki kai tsaye mamansu”
Murmushi ta yi , harshenta na yi mata nauyi kan maganar, a sanyaye ainun ta ce” Baban Muhamadu, kan maganar ya’yan nan ne yan mata…., Abansu dan Allah ina so ka dan duba lamarin nan mu samu mafita, ka ga Aisha da Rukaya sunna da masu so dan manemin auren Aisha yace idanma da hali yana so bayan babar sallah a yi bikinsu dan ya gama ginninsa…., Haka Rukaya a yadfa KAUSAR ta dabar min itama manemin aurenta ya shirya dama yake jira…..”
Ta dan tsagaita tana sake sada kanta ta ce” Abansu na san menene damuwarka, ama idan har haka Allah ya yi gwara mu fuskanci lamarin a aurar da Wa’inda suka samu malamuncin nasu, kar a tsaya jiran har sai KAUSAR ta samu miji a hade aje Allah ya kiyaye suma su zo ana kame kame…., Ka fa san menene rayuwar y’a mace, gashi KAUSAR bata yin wani kokarin da zai nuna tana son ta samu itama mijin nan ta je ta kilace kanta, yanzu dogon karatun nan na likita dai bana an ga karshensa in sha Allah koda sakamako bai yi kyau ba ba za’a kuma zaman bence ba sai dai a yi jiran wata jarabawar….., Ka ga sai ta zo mu girka sana’a ginaniya mu yi dan karra talafa maka a cikin gidan”
Da kyar ta iya kai karshen zancen, domin ta sani ne abinda ke daga masa hankali Kennan a rayuwa irin maganar nan
Ya jima yana kallonta , shiru yana tunani
Cen ya iya budar bakinsa ya ce” In sha Allah, itama zata samu malamuncinta….., Lamarin rayuwa kowa da irin tsarin da Allah ya yiwa rayuwarsa……, Maganar ta kama sana’a aa ban lamunta ba, tunda dai da sauran karfina kuma ina yin daidai gwargwado bi izinillah zan ci gaba , ba zaku ringa fita sana’a ba, ta cikin gidanama da kike yi dan kar na hanna a ga na so kaina da yawa ne Mamansu, maganar shekarunta kuwa ni baya gabana , ko dan ni na haifa? Lalle yana damuna ama ba shi yake nufin yana gabana ba, abinda yake gabana bara ki ji , dama jira nake yi ta gama, in sha Allah dukkan hanyar da zata dan daidaita rayuwarta zan sake nema na rike, zan kaita a dan kokoya mata dan gyara irin na yan mata, ni bana yiwa y’ata kwadayin auren wane sai dan mutunci ko wanene komai tsufansa, kar ki manta a lokacin da na ganki bakida ko digon kwali a idannuwanki, ina yiwa y’ata fatan miji na gari baki dayansu, dan Allah mamansu ki daina yin magana da sarewa a ciki kin ji? Na san abu ne mai matukar hanna zuciya sukuni, ama idan har ke kika fara haka zaki yi gagawar cin mini kin ji?……, Yaran nan kuwa zan duba maganar auren Allah ya doramu a kan hanya madaidaiciya”
Ajiyar zuciya ta sauke tana amsawa da amen sannan ta ciciba ta tashi dan ya ci gana da aikinsa haka kuma yannayinsa baya mata dadi dan walwalar tasa ta ragu, ama ba zata saka damuwar haka a ranta ba, fatanta ya gane ya kuma rike wannan dama, dan idan har suka rayu da jiran babar yarsu in Allah bai yi zata samu da wurin ba sai a zauna a tauye kowa da kowa?, Su Aisha kansu yanzun sun fara gandamewa ai
Da wannan ya’yan du suka shirya, ita zata fara fita bayan ta gaisar da Abanta tana ta doka murmushin tambayoyin da yake yi mata tana bashi amsa sannan ya salameta yau har dari uku ya wanka mata hakan ya sa ta fito kanta a sama kamar sarauniya ta zo ta duka ta yiwa Mamanta salama sannan ta mikowa Maman nata watsetsiyar wayar TAUFEEK wace ta saka su Aisha zaro ido sunna kallon wayar domin su sun san cewa ba karamar waya bace, ita dai ce da ba komai ya dameta ba ba wani sannin kudin wayar ta yi bama bale har ta ji tsoron rikewa ta ce” Mama wannan wayar adanawa TAUFEEK ita kar aje ta fashe ina hadeta da kaya a jakar nan”
Maman nata ta amsa tana kallonta ta ce” KAUSAR me yasa kika amshi wayarsa har ki je ki yar bakya tsoro? Da gani wayar nan ba karama bace ba fa?”
Aisha da ta rafka tagumi ta ce” Mama, wayar nan ai sai ta sayi aunty Kausar tsaf harma a nemi kari, Aunty Kausar da wayar nan kika kwana a gidan nan a san tana nan a shigo a yi kidmashin dinmu?”
Rukaya ta yi dariya tana dungure kan Aisha ta ce” Ke haba dai wayar zata wani sayi mutun, ama fa Mama wayar nan ba karamin kudi ne da ita ba gaskiya, koda yake su a gidansu yar autarsuma mai shekara goma sha uku iphone ce a hannunta ranar da muka je din nan amsar books din aunty kamar na kifa kallonsu kawai nake yi, Mamansu wata yar gayu da ita bakinta turanci ya amshe hausar”
KAUSAR ta girgiza kai ta ce” Ku dai kula sani, Mama wayar yau kwananta biyu a wajena, ba kin ga irin fadan da na masa da wayar Aba kan karatu ba? To Mama za’a shiga aji na amshe wayar dan karma ya zauna yana dane dane, har an shiga aji kawai ya tashi ya tafi har yau dai da ban ganshi ba, gatanan wayar a hannunki idan ya ga dama ya zo ya amsa, ni ba ni ba shi ko a hanya ya ganni ba zan nuna na sanshi ba, tunda haka ya zabarwa kansa sai ya yi”
Ta gama fada da takaici ta mike ta tafi tana fadin ta tafi
Aisha a a sake tafa hannu tana rakata da ido kafin ta dawo dubanta kan mamansu ta ce” Iko sai Allah, ni wani lokacin sai su rikitani da tunani, wani lokacin kuma sai kawai in ga kawancen ne kawai, ama yanzun kamar wata budurwarsa????”
Rukaya ta ja numfashi ta ce” Ke da ke kadai ce sai a maki maganin haka, ama kuma idan har kika yi duba da yannayin abin nan bayan zumuncin babu komai, aunty fa babu wannan maganar tsakaninta da shi, shima haka, inaga fa shekara hudu ce kawai ya batama, kuma bayan wannan yarinyar da zai aura fa in fada maki komai a hannun Aunty yake, kawai haÉ—uwar jinni ce mai wuyar fasara, ni abinda ke bani dariya da Aunty idan suka yi fadansu ta ringa rantse rantsen ba ita ba shi, ita dole sai ta sa ya mayar da hankali kan karatun da ya je ko bai je ba takardunsa tuni a hannunsa, kuma ya yi ko bai yi ba sunnansa mai kudi, ama haka ta yi ta fushi shima ya biye mata”
Mamansu dai da ta kai wayar ta boye dan ita tsoroma wayar ke bata ta dawo tana fadin” kai maza ku tashi ku yi da jiki ku kama hanyar makaranta ba sai kun yi lati ba ku ce sai an baku na sahu!”