Ad Code

Ayi Min Adalci Hausa Novel Complete

Ayi Min Adalci Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

AYI MIN ADALCI*

 

*King and Queen writing chamber*

 

 

 

BONUS! BONUS!! BONUS!!!

 

BAYAN WATA SHIDA

 

Abubuwa da dama sun faru ciki har da zamowar mahaifin Barrister Shaheedah sarki, sannan an ɗaura auren Faisal da Barrister Shaheedah. An sha shagali sosai, har sarauta aka yiwa Faisal Sardaunan samarin Muri, arziƙin ya auri ƴar sarki shi yasa aka yi masa sarauta.

Faisal kuwa naira ta zauna masa sosai, idan ka kalle shi ba zaka taɓa cewa shine Faisal ɗin da ka sani a baya ba. Yayi jajur da shi kamar balarabe, ga wani kyau da yake ƙara yi kullum.

Da Ciwo A Zuciya Ta Hausa Novel Complete

A wata unguwar hamshaÆ™an masu kuÉ—i waÉ—anda ake ji da su a Kaduna ya sayi Æ™aton gida. Inda suka zauna shi da amaryarsa Barrister Shaheedah ko kuma na ce Gimbiya Shaheedah tunda yanzu ta zama Æ´ar sarki. A nan kusa da unguwar da suke ya sayawa su Goggo wani danÆ™areren gida ya zuba musu duk wani kayan more rayuwa, da Æ´an aiki da za su rinÆ™a yin komai…Sannan ya bai wa Habibu aiki a babban kamfaninsa na man fetur, dama yayi karatu aikin ne dai Allah bai kawo ba.

 

Haka a É“angaren su Oumar da Auwal su ma Faisal bai manta da su ba, ya samar musu aikin yi a manyan ma’aikatun Gwamnati. Kasancewar Faisal ya san manyan mutane ta hannunsu ya bi ya samowa Oumar aiki a NNPC shi kuma Auwal a CBN, Mudassir kuwa tun daga ranar ya zama abokin su Faisal sosai suka zama kamar da can sun san juna lafiya k’alau suke zaune babu wanda yake Æ™yashi wani.

 

Su Goggo an samu duniya, ta je Umra ta je Hajji. Ga muhalli mai kyau sutura mai kyau ga lafiyayyen abinci, ko aiki Goggo ta yunÆ™ura za ta yi da sauri Æ´an aikinta suke dakatar da ita…Wani lokacin idan Goggo ta zauna tana tunanin rayuwar da suka yi a baya sai ta fashe da kuka ita kaÉ—ai, tunda take a rayuwa ba ta taÉ“a zaton za ta tsinci kanta a irin wannan daular ba, lallai yanzu ta yarda da karin maganar nan dare É—aya Allah ya kan yi bature. Hutu da jin daÉ—i sun zauna a jikin Goggo idan ka kalleta ba za ka taÉ“a zaton tsohuwa ba ce sai an faÉ—a maka…

 

Haka a É“angaren Faisal shi da amaryarsa Gimbiya Shaheedah, soyayya suke zubawa junansu kamar ba gobe. Gimbiya Shaheedah ba ta san tana son Faisal ba har sai da ta aure shi, sannan ta tabbatarwa zuciyarta babu wanda take matuÆ™ar so da kauna kamar shi…Akwai fahimtar juna sosai a tsakaninsu, lafiya kalau suke zaune sai zubawa juna soyayya suke idan ka kalle su dole su burge ka yanda suke matuÆ™ar kulawa da junansu. Duk bayan sati biyu sai Faisal ya É—auki amaryarsa Shaheedah sun je sun gaida mai Martaba wato mahaifin Barrister Shaheedah. Ƙasashen waje kuwa duk bayan wata biyu sai sun je yawon shakatawa sai sun daÉ—e a can suna shan love É—insu kafin su dawo…..

 

Haka kawai Barrister Shaheedah ta ji tana sha’awar yin kasuwanci. Ba ta yi wani jinkiri ba ta sanar da mijinta wato Faisal, ba tare da shakkar komai ba kuwa ya ba ta 50million ya ce ta fara da wannan.Idan ya ga kasuwancin ya karÉ“e ta sai ya kara mata wasu kudaÉ—en. Nan take Barrister Shaheedah ta shiga safarar gold and diamond, daga Æ™asar Dubai tana kawowa nan Nigeria ta sayar. Ba iya nan ta tsaya ba har da su rigunan abaya take sayowa ta zo tana sayarwa a nan gida Najeriya. Sosai kasuwancin nata ya karÉ“u nan da nan kuwa kuÉ—i suka fara zauna mata, ganin haka yasa Faisal ya Æ™ara mata wasu 50million din ya ce ta Æ™ara jari.. Cikin Æ™anÆ™anin lokaci Barrister Shaheedah ta zama matashiyar attajira, domin ta iya kasuwancin sosai…Dama tuni ta daÉ—e da ajiye aikinta na Lauya..

 

A cikin masarautar Muri kuwa Umma ta zama matar Sarki, komai sai dai ayi mata. Ba ta da kishiya ko É—aya, shi kansa Sarki Hamza da kansa ya ce, ba zai yiwa Umma kishiya ba saboda ta yi masa halaccin da ba zai taÉ“a mantawa da shi ba. Duk da jama’a suna damunsa sosai akan ya Æ™ara aure bai kamata ba yana babban Sarki ya zauna da mace É—aya ba. Shi kuwa yana ji sai ya share kawai domin gani yake idan ya Æ™ara aure tamkar ya ruguza duk wani farin ciki da yake tsakaninsa da iyalinsa ne, shi yasa ko kaÉ—an ba ya sha’awar Æ™arin auren. Umma tana da kirki sosai, kowa a cikin gidan sarautar idan ya buÉ—e baki sai dai ka ji ya yabe ta.

Wani danƙareren gida ta ba wa mahaifinta Aminu da kakanninta Malam Tijjani da Inna Mairo. Anan suka yi zamansu lafiya cikin kwanciyar hankali sun manta ma da sun yi zaman Nijar sai dai idan sun tuno su yi ta labarin abun..

 

 

*INA LABARIN HAJIYA BILKISU?*

 

Barrister Shaheedah ce a zaune ita da Faisal a kayataccen falonsu wanda ya gaji da haÉ—uwa sai shagwaÉ“a take zuba masa “Baby ka tashi don Allah mu tafi” kallonta yayi ya saki wani murmushi kafin ya ce,

“Yanzu shopping É—in lallai sai da ni za ki je?”

“To, ai idan babu kai ba zan ji daÉ—in tafiyar ba” murmushi kawai yayi tare da miÆ™ewa tsaye ya ce, “Alright tashi mu tafi.”

Da sauri kuwa ta miÆ™e tare da riÆ™e hannunsa ta ce, “Baby mu tafi”

Hannayensu sarÆ™e a cikin na juna suka fito compound É—in gidan, kai tsaye inda ake ajiyar motoci suka nufa…

Da gudu wani dattijo ya zo gabansu ya É—an rusuna kafin ya ce, “Alhaji fita za mu yi ne?” GyaÉ—a kai Faisal yayi ya ce,

“E! Fita za mu yi amma da kaina zan yi driving na hutar da kai”

“To, Alhaji Allah ya kiyaye hanya” yana faÉ—in haka ya juya ya bar wajen da sauri..

 

Wata mota mai ƙirar benz suka shiga, suna ƙoƙarin fita daga gidan suka hango Goggo ta shigo hannunta riƙe da Anwar. Dakatawa Faisal yayi tare da fitowa daga cikin motar, da saurinsa ya nufo su Goggo sai faman sakin murmushi yake, Anwar kuwa da ya hango Abbansa ya nufo inda suke shi ma da gudu ya nufe shi. Suna haɗuwa Faisal ya ɗaga Anwar sama tare da rungume shi tsam a ƙirjinsa, ƙaunar yaron yana jin yanda take mamaye masa duk wani lungu da yake cikin zuciyarsa.

 

Kallon Goggo yayi kafin ya saki murmushi ya ce, “Goggonmu mu shiga daga ciki ko?”

“A’a ba zama na zo yi ba, na ga alamun ma fita za ku yi.” GyaÉ—a kai Faisal yayi ya ce,

“E fita za mu yi yanzun nan Wallahi sai ga shi kun shigo”

Ya ƙarashe maganar yana sakin wani murmshi.

“Dama É—anka ne ya taso ni lallai sai na kawo shi wajenka, to ga shi nan na kawo ka ga sai ku fita tare ko?”

Murmushi mai sauti Faisal yayi kafin ya ce,

“Anwar me yasa ka taso Goggo da ranar nan?” Shiru Anwar yayi tare da sunkuyar da kansa Æ™asa…..

Barrister Shaheedah ce ta gaishe da Goggo da sauri kuwa Goggo ta juya ta fice daga gidan, tare da Anwar su Faisal suka koma motar tasu suka fita daga gidan.

 

Bayan sun gama siyayyarsu sun fito inda suka ajiye motarsu, suna Æ™oÆ™arin shiga motar “Faisal!” Gaba É—ayansu suka waiwaya inda suka jiyo amon muryar wacce ba za su taÉ“a mancewa da ita a rayuwarsu ba.

Ganinta suka yi cikin wani mawuyacin hali, sai tafiya take da kyar tana jan jiki kamar wata macijiya….

Kallo d’aya Faisal yayi mata ya kawar da kai tare da jan wani dogon tsaki.

“Mtssss! Taho mu tafi” ya faÉ—i tare da jan hannun Barrister Shaheedah, Æ™in tafiya Barrister Shaheedah ta yi ta ce, “Faisal Hajiya Bilkisu ce fa ba ka ga a halin da take ciki ba tana buÆ™atar taimako pls mu taimaka mata…”

“Allah ya kiyaye na taimakawa wannan matar Wallahi da na taimaka mata gara a ce zubar da kuÉ—in na yi… Ke yanzu har kina da bakin zuwa ki ce na taimaka miki?”

Hawaye ne ya zubo daga idanun Hajiya Bilkisu ta durƙusa har ƙasa tana roƙon Faisal,

“Don Allah Faisal ka taimaki rayuwata ka daure ka biya min kuÉ—in magani Wallahi idan ba ka biya min ba mutuwa zan yi….”

“Ai Bilkisu mutuwar ita tafi dacewa da ke, gara ki mutu ki je can ki tarar da abinda kika aikata…”

Fashewa da kuka Hajiya Bilkisu ta yi, ta tsugunna har Æ™asa tana roÆ™on Faisal akan ya taimaka amma Faisal yayi kunnen uwar shegu da ita ya Æ™i kulata ballantana ya saurareta. Barrister Shaheedah kuwa ranta ne ya soma É“aci ganin yadda Faisal ya ke wulakanta Hajiya Bilkisu….

Kallon Anwar Hajiya Bilkisu ta yi ta ce, “ÆŠana Anwar taho gare ni, ni ce Ummanka ka ji ko?”

MaÆ™e kafaÉ—a Anwar yayi ya ce, “A’a ni ba ke ce Ummata ba, ni kin ga Ummata” ya faÉ—i yana nuna Barrister Shaheedah..

 

Fashewa da kuka Hajya Bilkisu ta yi cike da gadara Faisal ya ce, “Alhamdulillah! Ko iya wannan abunda ya faru a nan wajen yanzu, ya isa ya zamo miki darasi Bilkisu, ga shi dai É—anki na cikinki gudunki yake duk me ya janyo wannan son duniya da amsa kuwwar shaiÉ—an..Don haka ni yanzu ba ni da lokacinki ki kama gabanki ki san inda dare yayi miki ina gargaÉ—inki karki kuskura ki Æ™ara zuwa inda nake idan kuwa kika Æ™i ji Wallahi sai na ba ki mamaki, sannan ina son ki jira sakamakon da zai biyo bayan abinda kika aikata ba ki ga komai ba Wallahi wasa farin girki….” Yana fadin haka ya juya da sauri ya shige cikin motarsa, cikin sanyin jiki Barrister Shaheedah ta É—auko kuÉ—i a cikin jakarta tana niyyar miÆ™awa Bilkisu…

“Idan kika ba ta ko naira biyar ce Wallahi ban yafe miki ba” Faisal ne ya fadi daga cikin motar yayin da ya ga Barrister Shaheedah tana shiri miÆ™awa Hajiya Bilkisu kuÉ—i…

 

Cike da tsananin É“acin rai Barrister Shaheedah ta zo ta shiga cikin motar zuciyarta duk babu daÉ—i, kallon Hajiya Bilkisu take a tsaye cikin rana jikinta ban da wari babu abinda yake yi. Tun tana kallonta har suka É“acewa ganinta gaba daya, durÆ™ushewa Hajiya Bilkisu ta yi a wajen ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya gami da tsantsar nadamar abinda ta aikata…

A cikin ranta take tunanin yanzu da tuni ita ce a cikin waccan motar, da tuni ita ce cikin kwanciyar hankali da jin daÉ—i…

“Gaskiya na cuci kaina ni Bilkisu ban san ya zan yi ba Allah na tuba ka yafe mini” ta faÉ—i tana rushewa da wani sabon kukan, mutane kuwa zagayeta suka yi wasu tausayi ta ba su duk da basu san abinda ta aikata ba, yayin da wasu kuma suke ta faman faÉ—in Allah ya Æ™ara dama ita duniya ai haka take idan ka bita a sannu ma da ya ka Æ™are balle ka bita da gaggawa….

 

Ko da su Faisal suka koma gida, kwata-kwata ya kasa samun nutsuwa a cikin ransa. Wani irin É—aci zuciyarsa ta rinÆ™a yi masa, sakamakon ganin Hajiya Bilkisu ji yayi a ransa inda yana da ikon kasheta da tuni ya kashe ta saboda tsanar da yayi mata….

Yana zaune a falo shi kaɗai yana ta faman tunani, Barrister Shaheedah ce ta kawo masa juice mai sanyi tana lallashinshi da kyar ya ɗan kurɓi juice ɗin sai ya ji zuciyarsa ta ɗan yi sanyi kaɗan, nan take ya shiga ambaton Allah.

A hankali ya ji zuciyarsa ta sanyi sosai, shiru yayi yana ta tunani…

 

Nocking ɗin da ake yi ne a ƙofar falon nasu ya dawo da shi daga duniyar tunanin da ya tafi, a hankali Barrister Shaheedah ta je jikin ƙofar ta leƙa ta jikin ƴar ƙofar nan da take jikin ƙyauren, hankalinta ne ya tashi sakamakon ganin Hajiya Bilkisu jikinta yana ta faman rawa.

Cikin sanyin jiki ta saka hannu ta buɗe ƙyauren.

Faisal da ya ƙurawa ƙofar idanu domin ya ga wanda zai shigo,

Ana gama buɗe ƙyauren ya miƙe tsaye a fusace ya ce,

“Uban waye ya kawo ki gidana? Ki yi saurin fice min daga gida tun kafin ranki ya É“aci”

Barrister Shaheedah ce ta tako ta zo har inda yake ta kama hannayensa ta riƙe

“Please Habiby ka yi haÆ™uri don Allah ka saurareta please my horny”

ÆŠan rusunawa Faisal yayi ya dubi Bilkisu a wulaÆ™ance ya ce, “Ina sauraronki”

Wani yawun baƙin ciki Hajiya Bilkisu ta hadiye,

yanzu wai ita ce sai wata ta saka baki sannan mijinta zai saurareta? “Gaskiya ni BILKISU na cuci kaina” durÆ™usawa ta yi a gaban Faisal ta dafa kafafunsa cikin raunin murya irin mai cike da tsantsar nadama ta ce,

“Don Allah Faisal ka yafe min laifin da na yi maka, ka yafe min don Allah ko zan samu sassauci a cikin halin da nake ciki. Na san duk alhakinka ne yake bibiyata, idan ba ka yafe min ba Wallahi ban san yanda zan yi ba…”

Zaunawa Faisal yayi akan kujera ya dafe kansa, yayi shiru…

 

Ganin haka yasa Barrister Shaheedah ta zo kusa da shi ta zauna tare da dafa kafaÉ—arsa ta ce, “Haba my Habiby ka yafe mata mana, ka san Allah yana son masu afuwa daga cikin bayinsa” wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauke ya dubi Bilkisu ya ce,

“Tunda matata ta saka baki na ji na yafe miki duniya da lahira, amma batun igiyar auren da take tsakanina da ke babu ita na tsinke ta gaba É—aya ukun kar ki Æ™ara yin tunanin sake zama inuwa É—aya da ni…”

ÆŠora hannu a kai Bilkisu ta yi, kafin ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya gami da tsantsar nadama..

“Ke Bilkisu ya ishe ki haka, kiyi saurin fitar min daga gida yanzun nan tunda na yafe miki, kuma na daÆ™ile igiyar auren da yake tsakanina da ke…” Faisal ne ya faÉ—i yana nuna Bilkisu da hannu cikin tsananin É“acin rai.

Durƙushewa Hajiya Bilkisu ta yi a wurin, ta dubi Faisal cikin muryar ban tausayi ta ce,

“Faisal na sani ka daÆ™ile duk wata alaÆ™a tsakanina da kai, na san na É“ata maka kuma na cancanci duk wani hukunci daga gare ka amma don Allah ina neman wata alfarma a gare ka..”

A wulaÆ™ace Faisal ya dube ta ya ce, “Ina jin ki Allah yasa zan iya”

“Don Allah ka daure ka siya min magani Wallahi idan ban samu maganin ba nan da kwana uku mutuwa zan yi” ta faÉ—i hade da fashewa da wani irin kuka mai ban tausayi…

 

A wulaÆ™ance Faisal ya dube ta ya ce, “Bilkisu kenan! Ina tarin dukiyar da kika samu a wajen marigayi Alhaji Hashim? Kar dai ki ce min yanzu duk babu ita?”

Girgiza kai Bilkisu ta yi ta ce,

“Tun lokacin da aka raba gado aka bani nawa, sai na haÉ—u da wani mutum mai suna Alhaji Kamilu, shine ya ce min na kawo kuÉ—in nawa shi ma ya kawo na sa mu fara business a Dubai..Na yarda da shi sosai, na É—auki gaba É—ayan dukiyata har da kadarorina muka haÉ—a ni da shi muka tafi Dubai domin mu fara kasuwanci tare..

Yayin da muka je can, ni ban san komai ba kuma ban san kowa ba ban da shi, sai ya rinÆ™a amfani da wannan damar yana cutar da ni. Kullum idan zai fita waje sai ya kulle ni a gida, sai bayan magriba yake dawowa idan na yi masa maganar kasuwancin namu sai yi min masifa yana cewa ba ni da haÆ™uri ko kuma ya ce ina zarginshi zai cinÆ´e min kuÉ—i…A Æ™arshe da ya gaji da takurawar da nake yi masa, sai ya fara nuna min ainihin kalarsa. Sai ya shiga nemana tun ba na amincewa ina guduwa har ta kai yana zuwa har É—akin da nake ko ba na so sai yayi min ta Æ™arfi da yaji, sosai ya mayar da ni matarsa duk lokacin da ya so amfani da ni zai zo ya biya buÆ™atarsa ba tare da tunanin halin da zan kasance a ciki ba…

Tun ina damuwa har na zo na daina na rinÆ™a ba shi hadin kai yana yin yadda ya ga dama da ni…

Kwatsam! Wata rana ya ce min na shirya zai tura ni can Germany tare da wani abokinsa na fara saro mana kaya domin mu fara kasuwancin namu, da murnata kuwa na shirya ya haÉ—a ni da abokin nasa wai shi Joseph Æ™arfe 11 na safe muka shirya muka hau jirgi, ashe ban sani ba duk shirinsa ne a jirgin Najeriya ya sako ni ba a cikin jirgin Germany ba, ashe yaudarata yayi shi da abokinsa tunda muka sauka a aiport É—in Malam Aminu Kano ban kara ganin Joseph ba, kuma nan take na fahimci Najeriya aka dawo da ni..Nan take kuwa na shiga cikin rudani domin gaba É—aya dukiyata tana hannun Alhaji Kamilu, da kyar na samu wani mai taxi ya kai ni unguwa uku na ba shi Æ´an sauran canjin da suka rage mini, sauran kuma na kama gida haya anan unguwar..Kullum tunanina shine ya zan yi na koma Dubai domin na haÉ—u da Alhaji Kamilu haka ne yasa shiga neman kuÉ—i a lallai sai na tara kuÉ—in komawa Dubai É—in na karÉ“o kuÉ—ina a wajen Alhaji Kamilu. Sana’a na ke yi da kyar wani Alhaji ya ara min bashin dubu É—ari biyar na kama shago na fara sana’ar sayar da abinci kala-kala, sosai kasuwar tawa ta karÉ“u nan take kuwa na fara tara kuÉ—in komawa Dubai wajen Alhaji Kamilu…

Kwatsam wata rana na tashi da wani matsanancin ciwon kai, da zazzaɓi mai zafin gaske, da kyar da siɗin goshi na kai kaina asibiti. Anan likita yake shaida min ina ɗauke da cuta mai karya garkuwar jiki wato (H.I.V AIDS) kuma ta fara yin ƙarfi a jikina. Hankalina ya tashi sosai, karo na farko da naji nadama ta shige ni akan abinda na aikata a rayuwata..

Sosai likitan ya kwantar min da hankali tare da É—ora ni akan magani, duk Æ´an kudaÉ—en da na tara domin na koma Dubai sai da suka k’are gaba É—aya a wajen sayan magani, na dawo kan jarin da nake juyawa su ma ba su daÉ—e ba suka kaf na dawo abincin da zan ci ma yana bani wahala. Ga Alhajin da ya ara min kuÉ—in nake juyawa ya saka ni a gaba a lallai sai na biya shi kuÉ—insa, ga gidan da nake haya su ma sun saka ni a gaba ban biya kuÉ—in haya ba. Ga maganina ya kare gaba É—aya kuma babu kuÉ—in sayan wani, haka ne yasa na tashi na dawo nan Kaduna na miÆ™a Æ™oÆ™on barata a wani masallaci ana nema min taimako, da kyar wata mata ta taimaka min da wani dan Æ™aramin d’aki a gidanta nake kwana, idan ka kalli É—akin ba zaka taÉ“a cewa mutum zai iya kwanciya a cikinsa ba. Ranar da na ganku na zo wucewa ne na hango Shaheedah ta shiga mota shi yasa na Æ™araso wajenku domin na nemi yafiyarku ko zan samu sassauci daga rayuwar da nake fuskanta mai cike da Æ™unci da baÆ™in ciki fiye da wanda na jefa ka a ciki….”

 

Tana kai wa nan a zancenta sai ta sake fashewa da kuka mai har da sheshsheƙa, Barrister Shaheedah ma hawaye sai faman kwaranya yake a kan fuskarta kamar da ita abin ya faru,

A hankali Faisal ya sauke nannauyar ajiyar zuciya ya dubi Hajiya Bilkisu ya ce,

“HaÆ™iÆ™a Bilkisu kin ga karshen maci amana tun anan duniya ko? To ina ga an je can Lahira? Ki godewa Allah ma da kika same mu har kika nemi yafiyarmu amma ya zaki yi da alhakin marigayi Alhaji Hashim?”

Sake fashewa da kuka Hajiya Bilkisu ta yi ta ce, “Wallahi ban sani ba na yi nadamar abunda na aikata a rayuwata don Allah Faisal ka taimaka min”

 

A nutse Faisal ya dubeta ya ce, “Na ji zan saya miki magani in sha Allah ba zaki sake yin rashinsa ba, zan hada ki da wani Likitana da zai rinÆ™a duba ki kullum, sannan zan baki gida ki zauna iya tsawon rayuwarki ba zaki rasa ci da sha ba…” DurÆ™usawa Hajiya Bilkisu ta yi tana ta faman zubawa Faisal godiya domin jita yi kamar kyautar Aljanna ya bata..

Numfasawa Faisal yayi ya ce,

“A dalilin kaza Æ™adangare ke shan ruwan kasko saboda haka ina son ki sani duk wannan abinda na yi miki saboda kin ci darajar É—an da yake tsakaninmu wanda kika gudu kika bar shi a lokacin da yafi kowa buÆ™atark…”

Shiru yayi sakamakon buga Æ™ofar da ake yi da karfi kamar za’a karyata,

 

Ba tare da tambayar ko waye ba Faisal ya buɗe ƙofar, ƴan sanda ne wajen su goma a tsaitsaye. Cike mamaki Faisal ya dubi ogansu ya ce,

“YallaÉ“ai lafiya kuwa?”

Murmushi dan sandan yayi ya ce,

“Kayi haÆ™uri Faisal mun zo tafiya da Hajiya Bilkisu ne”

Shiru Faisal yayi na dan wani lokaci kafin ya dubi É—an sandan ya ce,

“YallaÉ“ai indai don ni za ku kama Bilkisu na riga na yafe mata ku yi haÆ™uri ku koma”

“Faisal kenan! Idan kai ka yafe mata su Æ´an’uwan marigayi Alhaji Hashim sun yafe mata? Kuma hukumar Æ´an sanda ma ai ba su yafe mata ba”

“Amma yallaÉ“ai….”

“Ka ga dakata Faisal duk abinda za ka faÉ—i ka bari aje can station É—in muma Æ´an aike ne”

Ganin haka yasa Faisal ya buÉ—e musu Æ™ofar ya ce, su shigo, nan take kuwa suka shiga suka kama Hajiya Bilkisu tare da saka mata ankwa a hannu suka tusa Æ™eyarta tana kuka tana komai amma ko tausayinta babu a tare da su kawai ingiza ta suke yi kamar za su cinÆ´eta É—anye…..

Gaba É—aya Faisal sai ya ji jikinsa ya mutu ya rasa mai yake yi masa daÉ—i, domin har yanzu akwai sauran rububin son Hajiya Bilkisu a cikin ransa duk da tsantsar butulcin da ta yi masa a rayuwa…

 

 

BAYAN KWANA UKU

 

Faisal ne da Barrister Shaheedah a zaune a falonsu suna kallon tv, BBC HAUSA ne suke labarai gaba É—aya hankalinsu yana kan tv din. Ji suka yi É—an jaridar yana cewa

“Kotu ta yankewa matar marigayi Alhaji Hashim mai dala hukuncin kisa ta hanyar rataya, bisa zarginta da kashe shi har lah…” Bai kai ga Æ™arshen labarin ba Faisal ya kashe tv É—in yana dafe kansa da ya sara masa ciwo lokaci guda, Barrister Shaheedah kuwa fashewa da kuka ta yi ta tashi ta shige cikin dakinta.Gaba É—aya yinin ranar su Faisal ba su yi shi a cikin walwala ba, har su Goggo sai da suka jinjina abin tausayin Bilkisu gaba daya ya kama su, ba ta da kowa a Najeriya da ya wuce su Faisal shi yasa suka shiga tsananin damuwa bisa hukuncin da aka zartar mata, haÆ™iÆ™a Faisal da yana da halin da zai ceci Hajiya Bilkisu da tuni ya ceceta sai dai babu hali idanu ne kawai nasa….

 

 

BAYAN WATA ÆŠAYA

 

Barrister Shaheedah ce ta tashi jikinta duk babu daÉ—i, ga kasala da tashin zuciya da suke damunta. Ganin haka yasa Faisal ya kirawo likitansa domin ya duba ta, gwajin farko ya tabbatarwa da Faisal tana É—auke da ciki wata biyu…

Sosai Faisal yayi murna tare da yiwa Allah godiya, zai samu zuri’a tare da matar da ya fi so a cikin mata, Anwar ma da aka faÉ—a masa an kusa haifa masa sabon baby kullum murna yake tare da É—okin yaushe Ummarsa za ta haifo masa babyn sai dai ta kwantar da hankali amma duk da haka kullum sai ya tambaya.

Sosai Faisal yake tarairayar Barrister Shaheedah tare da bata kulawa ta musamman, har cikin nata ya cika wata tara…

Ranar Juma’a da safe nak’uda ta taso mata, nan da nan kuwa Faisal ya É—auke ta sai asibiti, ba ta daÉ—e tana naÆ™udar ba Allah ya sauke ta lafiya ta haifo kyawawan Æ´aÆ´anta su biyu…

Identical twins kamar su É—aya sak kamar an tsaga kara, mace da namiji ne.

Murna a wajen Faisal da sauran Æ´an uwa da abokan arziÆ™i ba a cewa komai, da ranar suna ta kewayo aka raÉ—awa yaran suna…

Namijin aka saka masa sunan mahaifin Faisal wato Muhammad Sani amma ana kiransa da Halim ita kuma macen aka raÉ—a mata sunan Umma mahaifiyar Barrister Shaheedah SALMA amma ana kiranta ana kiranta Ummi…Mai martaba ma sosai ya ji daÉ—in samun jikokin da yayi ya rinÆ™a murna tare da yiwa iyayensu kyaututtuka na musamman…….

 

Haka rayuwar wannan ahali ta cigaba da gudana cikin tsafta da kwanciyar hankali, Faisal ya zama Daddy Barrister Shaheedah ta zama Umma……

 

 

*Tammat bihamdillah*

 

Alhamdulillah anan na kawo karshen wannan littafin nawa mai suna AYI MIN ADALCI BOOK 2 abinda muka karanta dai-dai Allah ya bamu ladan abinda muka yi kuskure Allah ya yafe mana gaba É—aya…….

 

 

Duk mai bukatar complt BOOK 2 kai tsaye yayi magana ta cikin wannan number 07069475482 É—ari uku ne #300 babu tsada sai na ji daga gare ku…..

 

 

*HUSSAIN YUSUF*

2347069475482

Close Menu