Aameenat Bazawara Hausa Novel Complete
AAMEENAT (Bazawara)
Littafin HaÉ—aka ne
Ayeesha Abdulkareem
*INDO*
Daga ELEGANT ONLINE WRITER’S
Tare da
Salma Abdulkareem
*AUTAR JARUMAI*
Daga JARUMAI WRITER’S
PAGE 1
Bismillahirrahmanirrahim
Kaiwa Waccan Tsohuwar Bazawarar Abincinta, Fati ta faɗa Gami da gyatsine Fuska, Umaima ta ƙyalƙyale da dariya sannan ta ɗauki ɗan Abincin ta nufi Ɗaki da shi.
Aameenat Ta na zaune ta zuba Tagumi ta na jiyo su amma ba ta da bakin cewa ƙala.
A can gefe Umaima ta ajiye Abincin Sannan ta ce “Ga shi nan in za ki ci”
rausayar da kai tayi sannan ta taso zata É—auka seda tazo gaf da Abincin Umaima tayi maza ta É—auke tana cewa “Ahayye Æ™walelanki Æ™aramar bazawara”
“da kin zauna a gidan miji ai da kinci” Fati faÉ—a tana ya mutse fuska, dariya suka kwashe da ita suka tafa.
hawayen da suka cika mata Ido ne suka samu damar gangarowa fuskarta wani kallo Umaima ta watsa mata sannan taja Fati suka fice suna waƙe waƙen su na fitsara .
Doctor Nawal Hausa Novel Complete
wani sabon kuka ta fashe dashi tana cewa “kacuceni bazan taÉ“a yafe maka ba azzalumi”
ganin kukan baze amfane ta ba yasa ta tashi ta nufi É—akin wanka ruwa ta watsa ta fito ta shirya cikin doguwar riga Abaya yaluwa taji duwatsu masu sheÆ™i da walwali tayi kyau sosai madubi ta kalla wasu hawaye masu zafi suka fara gangarowa da sauri ta kauda kai tana tauna laÉ“É“an ta kafin ta tashi ta nufi Æ™ofa Mama ce tace ” zawar zawar ce yau tafito kenan” “haba kekuwa Mama ba dole a fita neman bazawari ba”
dariya Su ka sa Kafin Mama ta ce “Allah ya raka taki gona” Aaminat ta murmusa ba tare da ta yi magana ba ta yi hanyar fita, a Æ™ofar gida ta coge ta na leÆ™awa, kasancewar yamma ce ga iska na kaÉ—awa a hankali a hankali ya sa yanayin ya yi mata daÉ—i sosai, yaran layin da su ke Ƙwallo ta ke kalla, a zahiri idanunta su na kansu amma a cikin ranta tunanin Yau da Goben Rayuwarta kawai ta ke yi, “Wace irin Rayuwa ce Ƴan Adam su ka É—orawa kansu??, ba sa tunanin ita Ƙaddara ba kai kake tsarawa kanka ita ba??” tunanin da ya fi yi mata yawo kenan, ta na cikin tunanin ta ji saukar Ƙwallon a Fuskarta, ta yi baya cikin sauri gami da dafe fuskar tata, hawayen azaba ne su ka fara tseren zubowa kan kumatunta, yaran su ka yo yuuu akanta wasu suna “Don Allah ki yi haÆ™uri” wasu kuma su na cewa “Wallahi Walid ne ya jefo miki ita” Goge hawayen ta yi ta É—ago fuskarta ta na kallonsu, murmushi wanda ke Æ™ara nuna zallar haÆ™urinta ta yi kafin ta ce “Na haÆ™ura” Sauran su ka ÆŠauki Ball É—in su ka koma wasa. Abdulkareem ne ya tsaya Ya na Kallonta cike da tausayawa, “Yaya Aamimat!” ya kira sunanta cikin sigar Tambaya, cikin sauri ta zuba masa idanu, sai a lokacin ma ta san ya na gurin domin kuwa a kowacce daÆ™iÆ™a tunani ne tsarin rayuwarta, “Abdulkareem sun ci gaba da wasan ba kai” ta faÉ—a ta na masa É—an murmushi wanda ya ke bala’in sumar da Zinariyar Zuciyarsa “YaYa Aameenat ban ji daÉ—i ba, wallahi dan dai Walid Ƙaninki ne kuma ba’a shiga faÉ—an dangi banda haka da sai kinga yadda zan yi da shi, don ni da a raina ki gwara a mutu har liman, ban damu da rashin kunyar Yayyensa Ƴan Matan nan ba” Ita har ga Allah ya takura mata, don kuwa ganin tsaurin idonsa ta ke yi ta yadda ya ke iya zama ya na tsara mata kalamai kamar irin Namiji ÆŠan 35-37 Years É—innan, ashe nan Bai fi 20 Years zuwa 21 22 ba, yadda ya ke iya jefa Æ™wayar idonsa a cikin nata ya fi komai bata takaici, shi don bai sani bane amma ba Æ™aunar ganinsa take ba. Jin ta yi shiru ya sa shi yin dariya ya ce “YaYa Aaminat haÆ™urinki ya na bala’in TaÉ“a Zuciyata!” ya Æ™arasa maganar gami da É—ora É—an yatsansa akan Ƙirjinsa saitin Zuciyar tashi, haÉ—a hannunta ta yi guri É—aya alamar roÆ™o, cikin sassanyar muryarta ta ce “Abdulkareem don Allah ka koma ku ci gaba da Æ™wallonku Me yasa sai ka dame ni ne???” “Ba na gajiya da kallonki ne” lokacin da ya yi maganar ya juya mata baya har ya É—anyi tazara da inda take, ta saki baki ta na kallon bayansa, É—an Æ™aramin tsaki ta ja kafin ta juya ta koma ciki aranta ta na cewa “Ciki ba daÉ—i waje ba daÉ—i Abdulkareem ka fiya shiga rayuwata, Mara kunya da tsayayyun idanunka”
Ta na shiga Mama dake shara ta ce “A’ah Zawar me mu ka samu ne naga kin shigo baki na motsi??, ko mun yi sabon kamu ne??” Girgiza kai ta yi alamar “a’a” ta ratse ta shiga É—aki, Mayafinta ta fizge ta jefar sannan ta shiga gyara É—akin, daga fitarta har Su Fati sun yi abinda su ka saba, sun yi wa É—akin batsa batsa, ta na aikin ta na Tunanin Kamal wanda ta kasa mantawa dashi, zuwa yanzu ita kanta shaida ce WATA TSIYAR A Jinin ÆŠan Adam take, Ba ta taÉ“a tunanin haka za ta gindaya tsakanin Rayuwarta da Kamal ba.
hawayene suka fara sunturi a kuncinta sosai take sheshshekar kuka tana girgiza kai, jiri ne ya fara ɗibarta tayi saurin dafa bango ta na ambaton Allah, a daddafe ta iya ƙarasa sharar dan ta zamar mata dole, fita tayi tsakar gidan ta fara haɗa kwanuka domin wanke su ba tare da ɓata lokaci ba ta kammala wanke wanken ta shiga ɗaki ta saki labule domin bata son yin kaciɓus da samarin gidan dan kuwa basason ganinta guri tanema ta zauna tana jen carbi.
dariyar da taji ce tasa ta ɗagowa Umaima ce da ƙawarsu Nafisa da Fati suke mata dariya
“Oni Æ´asu dama haka zawarci kebsa bawa ladabi”? Nafisa faÉ—a tana riÆ™e haÉ“arta wani murmushi Fati tayi sannan tace “to zawara se a bawa Æ´an mata waje ko, ta baro gidan miji ta zo ta dami mutane”
bata musa ba ta tashi ta nufi É—akin Umma, duk da ta san balalle ta barta ta shigar mata É—aki ba kai a Æ™asa ta Æ™arasa kofar É—akin, Umma ta watso mata harara gami da cewa “Sannu Aameena karki shigo min É—aki, ki É“ata min, É—akin naku aikin me yake yi??” “Su Fati ne a ciki” Umma ta ce “Ai ba Æ™arfinki su ka fi ba, ni dai ba a É—akina ba, yanzu na gama share shi” jiki a sanyaye taja Æ™afafuwan ta tanufi kicin, karo taci da Umar ya shigo ta sunkuya tace “Ya Umar ina wuni” be ko kalleta ba ya wuce abin shi hakan yayi mata ciwo sosai Amma inda sabo ta saba haka ta tura Æ™ofar kicin É—in ta shiga ta zauna tare da saukar da wata ajiyar zuciya yunwa takeji gashi babu da mar dafa abinci domin in mutan gidan suka sani baza taji da daÉ—i ba. rabonta da abinci tun karin safe ta galabaita sosai dankuwa duhu duhu take gani..
Rai a É“ace ya shiga gidan bebi ta kan kowa ba ya nufi É—akin su “Abdulkareem”! tafaÉ—a cikin kwantar da kai batare da ya juyo ba ya tsaya cak bece ko mai ba a hankali ta Æ™arasa inda yake ta É—an shafi gefen fuskar shi tare da hura mai iska da bakin ta batare da ya É—agoba yace “Ummi ina jin bacci” “maza kaje in katashi ka sanar min da wuri don rabonka da abinci ka daÉ—e, ka fi ganewa tsalle tsalle” be ce komai ba ya cigaba da tafiya murmushi tayi tare da bin É—an na ta da kallo tana sa musu Albarka tare da addu’ar Allah ya Æ™ara haÉ—a mata kan su mazan da mata ya tsaresu daga sharin magauta.
É—akin wanka ya shiga yawatsa ruwa ya na fitowa ya nufi firji gorar ruwa ya É—auka ya sha sannan ya sauke ajiyar zuciya gami da dafa Æ™irjinsa….
CommenT
Shere FisabilillaH
© INDO CE & AUTAR JARUMAI