Yar Tsanar Zinari Hausa Novel Complete
YAR TSANAR ZINARI
Story & Writing
By
JIDDARH UMAR
MOONLIGHT WRITER’S ASSOCIATION
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*01*
Ƴan Sanda ne tsaye a bakin babban titin garin wadanda a kalla sun tasar ma mutum goma,
Ko wannen su riƙe yake da makami wato Bindiga,idan nace Bindiga,ina nufin asalin Bindiga lafiyayye,sun riƙe ta da kyau yayin da suka seta wata baƙar mota ƙarama na yayi wanda idan kaji kudin ta sai kayi mamaki,
Jira kawai suke motar ta motsa su bata wuta tamkar yanda sugabansu ya umurce su akan haka,
Babu wani fara’a ko digon imana a tare da waÉ—annan fuskokin kuma basa tunanin zasu sassautawa na cikin motan nan in har basu cika umurnin sun fito daga cikin motar sun mika kai tamkar yanda suka buÆ™ata ba.
Lekawa nayi cikin motar domin na gano wani shahararren mai laifi ne wanda wuyansa ya gawurta aka tare har haka,me yayi,sannan yanzun a wani irin tashin hankali yake ciki a zaune a cikin motar,
Dan haka a hankali na fara lekawa ta cikin tagar,
Sai dai kuma abinda na gani ba karamin mamaki da rikitar dani yayi ba,wanda har saida na kara murza ido na domin son tabbatarwa da gaske abinda nake gani haka ne,sai dai kuma ina kara budawa abinda na gani dai shine zaune ba wani ba,wato dai a takaice wata mace ce na gani zaune a mazaunin direba,wacce daga dukkan alamu ba tada wani girman jiki na azo a gani haka kuma daga zaunen da take zaka fahince ta na da tsayi dai dai gwargodo,bana iya ganin komai nata face ta gefen kunnen ta wanda take fari ne sosai irin tas dinnan,haka kuma suman dake gefen kunnenta yayi wani irin kwanciya mai ban mamaki,sai hannunta wanda sanye yake da bakin safar hannu irin mai kamawa,kamar yanda suman kanta yake a nade an mashi dauren donut sai dai a kwai facing cap a kanta,hancinta sanye yake da wani baƙin Nose mask,sai Jacket din dake jikinta shima baki ne mai dogon hannu,da kuma dogon bakin wando,a takaice dai abin da nake iya gani kenan a jikinta wanda ko kalar fakar ƙafarta baka iya gani,
Halin Kishi Hausa Novel Complete
Itama wacce take zaune a gefen hagunta irin shigar dake jikinta kenan,sai dai abu ɗaya wanda ya bambanta su,ita wacce take zaune a gefen hagu jikinta rawa yake,sannan kuma ga hawaye dake fita a gefen idanunta,wanda yake fitowa kai tsaye daga cikin idanun nata,daga dukkan alamu a mugun tsorace take,saɓanin wacce ke zaune a mazaunin Direba koda ma ace hankalin ta a tashe yake,to bata nuna alamar da zai baiyana hakan ba,dan wata waka ce ma take saurare a rediyo motar,kuma har tana ɗan binshi tana gyaɗa kai,tana kuma kallon manyar ƴan sandar dake gabansu,
ÆŠayar ce a matukar firgice ta kalle ta gefenta tace”BIBA shi kenan mun kawo kanmu duniyar da za’a kashemu,waiyo Allah na,wani tsautsayine ya aikeni biyo ki Kasar Gambia,shi kenan Allah ya jikai na”
Cikin wata iri yar murya mai matukar sanyi da zaki,wacce take fita a hankali ba tare da hayaniya ko tashin hankali a tare da ita ba,tace”me yasa kin cika surutu ne Ummita “ta faÉ—a tana kauda kai,
Kuka ta fashe da shi” Yanzun BIBA har kina da bakin da zaki ce na cika surutu,yanzun ba ki ganin mutuwa a gaban mu,ke fa kika ce ba wani aiki mai wahala bane zai kawo mu,sai gashi yanzun kinsa ina fuskantar mutuwa kiri_kiri,”
Juyowa tayi ta kalleta “karki damu Ummita,dama ita rayuwa hanya biyu ce,kanada damar da zaka zabi duk wacce kake so,ko dai ka dauki hanya mai kyau,ko ka É—auki mara Æ™yau,to ni BIBA na É—auki akasin mai Æ™yau”
Cikin mamaki mai tattare da tsoro tace”kina nufin mara kyau kika É—auka?
Murmushi ta sake wanda duk da ba gani kake ba saboda face mask amma ya baiyana a cikin kwayar idon ta”harda ke,hanyar dana zaÉ“ar maki kenan”tana gama faÉ—in haka ta kunna motar tare da taka burki wanda nan take motar ta bada wani sauti irin na lafiyayyun motoci,
Juyowa ta yi ta kalli inda Ummita ke zaune”kin iya ruwa?
Da sauri ta girgiza kai tana ɗan leƙen babban rafin dake zagaye dasu,domin a saman titi suke wanda ya kasance kasan shi tafkeken rafi ne,
“Ki daura Ballet da kyau”
Kara cukuikuye Ballet din dake jikinta tayi, wanda dama tun fara tseren su da Æ´an sanda a cikin gari ta daura dakyau dan tasan in dai tukin Biba ne tana iya fita ta windo,
Wani irin kara motar ke fitowa dashi mai tattare da hayaƙi wanda tuni ya turnike wurin,karan harbi suka fara ji wanda ya fara sauka a kan mota,
Kafin Yan sanda su fara gama tantace shin cikin su zata yi kome zata yi kawai cikin ƙwarewa da iya sarrafa sitiyarin mota ta daki wasu dakali da akayi ta gefen titi da karfin gaske wanda ya haddasa ma wurin fashewa kamar yanda gaban motar ta tarwase,sai dai wannan ba damuwar ta bace,kara dawowa baya tayi a ƙaro na biyu,ta fisge motar wanda nan take suke sunduma a cikin wannan tafkeken Rafin daga ita har motar,
Duk jami’an daje wurin da gudu suka nufe rafen suna lekawa domin kuwa ba kamin shammatarsu tayi ba,basu taba tsammanin zata iya faÉ—awa acikin wannan ruwan ba,
Wanda ya kasance Oga a wurin ne yayi Æ™wallo da wani block dake gefen shi yana faÉ—in “ohh shet,”
Daya daga cikin su ne yace”oga yanzun me abinyi domin daga dukkan alamu ta mutu domin motar ta nitse a cikin ruwa”
Cikin matsifa yace”koda ace ta mutu ina bukatar gawarta,ina bukatar gawar wannan yarinyar,”
“Oga tunda ta mutu me zai hana mu bar ma kifaye su cinye”
Wani irin lafiyayyen mari ya zuba mai yana cakumo kwalar rigar shi “kasan kuwa me ta sata,kasan me a hannun ta kuwa,to bari kaji,abinda ke hannun ta yafi kuÉ—i daraja,yafi zinari daraja,dole koda gawarta ne a nemo a cikin wannan ruwan ina bukatar ta” Ya faÉ—a da ihun takaici yana wurgi dashi gefe,domin yasan idan har ya kama wannan Hatsabibiyar Yar Tsanar to ba karamin warkewa yayi ba daga shi har dangin shi,matsayi kuwa a gwamnati sai wanda ya zaÉ“a.
Kallon sauran yaran shi dake tsaye yayi “aje a dauko injin mai tsamo mota a ruwa a ciro su”
Cikin girmamawa suka Sara mai…..
YAR TSANAR ZINARI
Story & Writing
By
JIDDARH UM
*”’We are the moonlight writers we shine all over the world.”
بِسم الله الرØمن الرØيم
*Ban yarda wani ko wata su saka min littafi a shafin su ko su mai da min littafi Audio ba tare da izini na ba*
*02*
A cikin ruwa kuwa cikin kwarewa ta cire Ballet din dake jikinta sannan ta buɗe wani karamin jakka data ɗauko daga bayan motar,da sauri ta buɗe ta dauko wasu abubuwa guda biyu na zukar numfashi a cikin ruwa mai dauke da wani ɗan ƙaramin contenar na gas,sai glass na ido, shima wanda ke hana ruwa shiga ido,
Jawo Ummita tayi ta cire mata bellet wacce ke ƙoƙarin suna saboda ruwan da take shaka,
Saka mata abin tayi a hanci,ta goya mata karamin tukunyar,ita ma abinda tayi kenan,sannan ta tallabi Ummita ta fara iyo da ita ta kasan wannan rafin,wanda a Æ™alla sai da tayi iyo da ita a wannan ruwan na tsayin mintina Arba’in tsakanin su da inda suka faÉ—a,sannan suka fito,
Zuwa lokacin ita kam Ummita da kyar take numfashi koda ta yi wurgi da abin hancinta,ta cire gilashin daya taimaka mata wanda ya hana ruwa shiga idonta,
Kwantawa tayi kawai tana maida numfashi,tare da jira taga kuma me zai faru,
Jin motsin tafiya ne yasa ta daga kai tana bin Biba da kallo,wacce taga ta nufi wata Blue mota mai kama da tazi,hannu tasa ta bude bayan motar ta dauko wani lede babba ta daura saman motar,
Abu na farko data fara yi shine cire wannan facing cap din dake kanta ta yar a kasa,wanda hakan yasa saida na kusa kwarewa saboda ganin irin zubin hallitar fuskarta,wanda yake fuska ne mai É—an faÉ—i,dan ba zaka kira shi da mai tsayi ba,mai dauke wasu irin dara_daran zagayayyun idanu masu matukar haske da girma,cikin kwayar idon kuwa baki ne wuluk yayin da farin yake tamkar tsaftaccen madara,tsabar fari wanda ba karamin kyau yama idanunba,giran idanunta razo_zaro ne tamkar yanda giranta yake a cike mai tattare da wani irin shape yanda kasan an mata kabin gashi baki kirin,
Hancinta ba shida irin tsayin nan sosai,sai dai ba zaka kirashi da mara tsayi ba ko gajere,ya dai zauna sosai kamar yanda ya dace da fuskar, sai kuma labbanta masu matukar taushi da tsantsi ma dai-daita,masu matsakaicin faɗi,haka kuma tana da haƙora fari tas wadanda suke ƴan madaidaita yanda kasan na yara,masu matukar jan hankali,kuskar Biba kadai can iya jan hankalin mutum ya shagala ga kallon ta,
Jacket din saman jikinta ta cire ba tare da tunanin komai ba ta daga rigar dake kasan jaketa din wanda yake fari ne,
Kai jama’a tsarki ya tabbata ga Allah wanda yake makagin dukkakn hilittu,
Idan ka kalli tsarin halitar kirjinta wanda yake a cike a cikin Pink din Bireziya ka gangaro zuwa shafaffen cikinta wanda ya haɗe da baya,idanunka suka sauka a saman ɗan ƙaramin ramin Cibiyar ta wanda ya shige canciki, yayin da aka makala wani ɗan ƙarfe mai matukar jan hankali a wurin wanda na tabbatar na zinari ne saboda yanda wurin ke daukar ido,maranta a shafe yake sosai babu alamun tudu ko wani abu,
Takalmin Æ™afarta ta cire sannan ta cire dogon wandon dake jikinta,ya rage daga ita sai pant,jama’a ba zan iya cewa komai ba sai dai ku kwatanta yanda tsarin halittar kugun Biba yake,sai dai abun da zan iya faÉ—a shine ba tada mugun Hips madaidaicine mai matukar jan hankali,kamar yanda fatar jikinta yake sumul yanda kasan na tarwada tsabar tsamtsi,babu wani tamurewa ko tattarewa a tare da fatan kamar yanda babu nankarwa ko rakainuwa ne oho,babu shi dai a jikinta,
Juyowa tayi ta kalli Ummita wacce ta taso ganin yanda take tube kaya,
Jawo ledan tayi ta ciro wasu kaya ta mika mata”kiyi sauri ki saka mubar nan wurin domin nan da minti ishirin jirginmu zai tashi zuwa NIGERIA”
Amsar kayan tayi ta warware tana kallon ta”Biba ina kika samu kaya”
Ba tare data juyo ba tace”ba nida lokacin amsa maki wannan tambayar kawai kiyi abinda nace in kina buÆ™atar kasancewa a raye”
Bakinta taja ta kulle yayin data hadiye dukkan tambayar da take dashi,idan sunje gida ta jero mata su.
Dukansu riga da siket ne na atamfa sai jallabiya irin wacce ake ma lakabi bi After dressing,shi suka saka,sai kuma Sun glass na ido babba wanda ya kusan cinye rabin fuskar tasu,
Kayansu ba iri É—aya bane kowa da irin nashi,
Kayan da suka cire ta kwashe ta maida cikin leda,harta daure ledan sai kuma ta sance da sauri ta ciro wandon data cire,hannun ta saka a aljihum wandon ta ciro wani karamin leda,ta buɗe,sai ga wani ɗan ƙaramin Memory Card,
Maida wandon tayi cikin ledar sannan ta wurga ledan cikin wannan katon rafin,
Motar suka shiga yanzun ma itace a mazaunin direba,kafin ta tayar da motar ne ta mika hannunta ta dauko wani karamin jakkanta wanda yake É—an madaidaici ne irin na Æ´an matan yanzun,buÉ—ewa tayi ta duba passport dinsu,sannan ta ciro wata Android phone ta saka wannan Memory a ciki,ta maida cikin jakkan,
Sai da tayi Ribas sannan ta ja motar da karfi suka bar wurin,wanda tafiyar minti goma ya kai su Airport,
Lafiya aka gama caje su kafin a basu damar shiga cikin jirgi,wanda gaba ɗayan su a lokacin da suka ji jirgin ya lula sararin samaniya dasu suka sauke ƙaƙƙarfan ajiyar zuciya,yayin da ita kuma take ƙara damke jakkan dake rike a hannun ta,tana mai fatan saukarsu lafiya..