Ad Code

Yankan Wuka Hausa Novel Complete

Yankan Wuka Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Yankan Wuka Hausa Novel Complete Page 1

Godiya ga Ubangiji madaukakin sarki Wanda da yardar sa ne komai yake tabbata a yau ma ya sake tabbatar Dani akan sabon Aiki Wanda nake fatan ya Zama shiriya gareni da dukkan Al ummar musulmi Allah kar ka bari rubutu na ya zama silar da zai batar da Ni ko na batar da Al umma

 

 

 

Sadaukarwa ne ga iyaye na guda biyu uwa da uba Wanda nake wa fatan Ubangiji yayi musu Rahama da gafara a cikin kowane Hali Rayuwa da mutuwa

 

 

Godiya ga dunbum masoyan rubutun GIDAN IKO na kusa da na nesa Allah Ubangiji ya amfanar damu alherin rubutun kuskuren ciki kuma Ubangiji ya yafe Mana

 

 

 

Ba zan taba mantawa da wadan Nan mutanen ba . Haj binta kassim kaduna . Haj Adama shehu Zaria. Haj Saliha abubakar Abdullahi Zaria tare da anty Jamila yusha u sokoto Ubangiji ya biya ku da alherin sa bani da bakin Gode muku sai dai nace Allah Ubangiji ya biya ku da GIDAN aljannah

 

 

 

 

Da sunan Allah Mai Rahama Mai jinkai salati da aminci Mara’s adadi zuwa ga shugaban mu ANNABI MUHD S A W da ahalin gidan sa madaukaka da masu binsu da kyautatawa har izuwa ranar alkiyama

Duniya Hausa Novel Complete

 

 

 

………. Karfe Sha biyu da minti arba in da biyar na Dare agogon dakin ta nuna min lokacin da nake Kai ganin idona akan ta Don tabbatar da lokacin sai ta nuna min Ashe Dare ya ja sosai kusan dayan dare saura kenan.

 

Gaba na ya kuma faduwa a karo na barkatai saboda tunanin dalilin da ya rike Mai gidan har wannan lokacin bai dawo ba abinda na San baya yi a waje wato Dare irin wannan . Ya jima a waje da yawa karfe takwas zuwa Tara shima zai Kira Ni ya fada min Dalilin da ya tsayar da shi ….

 

Da sauri na kuma jawo waya ta na sake doka mishi Kira Amma shegiyar matar Nan Mai kaifin muryar tsiya ta sake bayyana a dodon kunne na tana Kara maimaita min wai wayar k’atada ba zata samu a yanzu ba sai dai na sake Kira lokaci na Gaba

 

Na kasa hakura da Kiran wayar k’atada itama matar Mai kaifin murya ta kasa hakura da nanata min ba za a same shi yanzu ba sai zuwa lokaci na Gaba.

 

Tsoro da zullumi har da fargaba suka lullube Ni na kasa tsayarwa zuciya ta Dalili guda Daya tal da ya rike k’atada har ya Kai wannan lokacin bai dawo ba kuma wayar shi a kashe

 

Zukata na suka soma yi min canki cakire akan k’atada da abinda yakeyi har ya kama waya ya kashe

A take naji karfafu na suna Shirin Kai gangar jikina kasa saboda yarda da raunin da nake Shirin yarda da shi

Na sake Kiran wayar k’atada Amma dai sammakal a kashe take. Na kuma Kai idona akan agogon dakin wadda take Shirin cike lokaci na karfe Daya na talatainin Dare

Dole na koma na zauna tamkar wacce ake cirewa laka

Tsoro da fargaba suka cika Ni yayin da zufa ta soma yanko min har na warware daurin Dan kwalin da nayiwa dauri irin na Mai gida ga naka. Kwalliyar da na yarfa kuwa damuwa ta bada Tata gudunmuwar wurin Dame ta na koma tamkar wacce Tayi zaman awa biyar a tsakiyar Rana……

 

 

Iska ne ya taso alamar hadari ne ke Shirin tasowa

Na Mike zuwa window na yaye labulen inda nayi karo da hadari ya taso sosai k’ura da iska suka soma Shan sharafin su kan kace me? Yayyafi Mai karfi ya Soma sauka rufin kwano kafin nefa tayi halin duhu ya mamaye Duniya Amma mu sabida invater da ke jone yasa Nepa na daukewa inverter ta kama haske tarwai ….

 

Ruwa ya Soma sauka Ina Shirin sakin labulen in koma ga tunanin dalilin fakuwar k’atada sai kawai naga Hasken fitilar motar Yana doso get din . Duk da ruwan saman da ke sauka da karfi hakan Bai Hana na Gane farar motar k’atada ba ina kallo aka bude mishi kofar get ya shigo da motar Ni kuma na saki labulen Ina sauke AJIYAR ZUCIYA na koma kan kujera na zauna Ina duban kofar shigowa

 

Minti uku naji Yana taba kofar na Mike na nufi kofar ina budewa kamshin turaren shi ne ya Soma dukan hanci na kafin ya bayyana …..

 

Na Kai idona Don ganin yanayin da ya shigo sai kawai idona ya gano min wani abun mamaki…….

 

K’atada ya shigo Yana sallama da wata irin murya Mai sanyi yayin da wata tsaleliyar mace fara tas ke biye dashi a bayan shi tana janye da trolley……

Gaba na yayi wata matsiyaciyar sarawa na amsa sallamar k’atada murya na rawa idona akan wannan kyakkyawar macen da take bakunta ta da tsakar Dare…..

K’atada ya juyo Yana nufo Ni Yana runguma Ni kuma na Zama wata galhoma Ina binsu da kallo…….

 

“Kiyi hakuri my only one nasan hankalin ki na Nan tashe ko ?

Yadda yake magana ne yasa naji Sam ban gamsu da shi ba in ma akwai wani abu Mai kama da Rashin yarda ko aminci to a Nan naji Ina mishi shi….

 

Ita kuwa bakuwar tawa Kanta tsaye naga ta wuce tamkar dai ace ta San ta kan gidan ko kuwa dama Nan take

Ta nufi kujera tana Zama ta jingine trolley din ta fuskar ta a hade ga kuma kyakkyawar rigar ta ta shadda ta jike da ruwa wata kill shine abinda ya Dame ta……

 

“Taimaka ki bawa bakuwar Nan masauki ta sauya kayan ta Kinga ruwa ya jika ta ga sanyi sanyi garin ya dauka said ki dawo nayi miki bayanin ta nasan ranki cike yake da tarin tambayoyi……

 

Ya Isa inda bakuwar take Yana Fadin

“Kuje zata nuna miki masauki sai ki sauya kayan Nan da suka jike akwai toilet a dakin in kina bukatar watsa ruwa kafin a kawo miki abinci..

 

A zatona zanji Tayi godiya sai naga ta Mike tana Kara cin magani tamkar dai ace wacce akayiwa laifi tana Shirin fanshewa

Na kama Jakar ta ta trolley naja Mata har zuwa sifayan dakin na tura muka SHIGA na Kai Mata trolley har kusa da gadon dake kwance a dakin na juyo ina nuna Mata toilet sai kawai naga tana k’arewa dakin kallo a kaskance tana wani ciccin magani abinda yaso fusata Ni da wannan kallon Rainin nata. Amma sai na tuna bakuwa ce kuma ban San wace irin bakunta zatayi ba kuma banji daga inda ta fito ba wata kill daga dangin innar sa ko baban sa Dole na fice na barta tana min wani kallo Mai kama son gano wani Abu a tare Dani….

 

Na fito na dawo falon na same shi zaune ya buga uban tagumi ya zura wa kofar da muka bi ido ……

 

“Taimaka Mata da abinci my only tana cike da yunwa ne na tausaya Mata kema na tabbata Zaki tausaya Mata ……

 

“A hakan zan tausaya Mata ? Wace irin bakuwa ce wannan k’atada ka yayo Mana? Daga Ina take ? Kuma a Ina ka debo ta? Ban ga fa alamar bakunta a matar Nan ba kana kuwa ganin yadda take wani ciccin magani tamkar gidan gidan gyatumin ta? …….

 

“Yi hakuri Kai Mata abincin ki dawo bakon ka fa ANNABIn ka ko? Dama

nasan Dole zakiji babu dadi duk a rasa irin bakon da za a kawo maka sai na mace irin wannan ? ……

 

Na dube shi Yana Kara kwantar da murya abinda ya kuma darsawa ZUCIYA ta zargi kenan na kuma ji Sam ban yarda da k’atada da wannan matar Mai amsa sunan bakuwa ba Amma da yake k’atada ya sani bani da wani kwanji akan sa Dole na Mike na nufi kitchen na kinkimo kayan abincin na fito da su inda na riske shi da waya kare a kunne Amma Ina shigowa yayi maza ya yanke Kiran Yana mikewa ya karbi kayan abincin ya aje a kan center table Yana jera min sannu

 

Mamaki na da wa yake waya a yanzu? Kuma yaushe ya kunna wayar Tashi da nake ta faman Kira ana ce min kashe take?

Jiki a sanyaye dai na hada abincin na dauka na nufi dakin bakuwar inda tun kafin na shiga dakin na soma jiyo maganar ta tana Fadin…

 

“Bafa zan iya ba gaskiya Don bamuyi haka da Kai ba. Ina Dalili da zan mayar da kaina……..

 

Ban tsaya jiran jin cewar ta ba domin kuwa ba labe nazo yi Mata ba Don haka sai na tura kofar na shiga . Itama ganin shiga ta yasa ta ajiye wayar inda na ga ta sauya kaya da na jikin ta zuwa wata rigar bacci night gown dogon gashin Kanta ya sauko har kafadunta yayin da santala santalan cinyoyin ta suka bayyana. ….

 

“Ga abinci ga kuma fridges Nan akwai ruwa akwai lemu in kuma kina bukatar wanka ga toilet Nan

Na K’are magana ta ina Shirin juyawa ita kuma sai yamutsa fuska take babu ko uhum bare godiya. Lallai kuwa bakuwar Nan Bata sanni bane Ni da gidana ? Ai kuwa Rashin jini ne Rashin tsagawa Amma bari naje naji ta yadda ta wanzu da kuma Dalilin da ya kawo ta gidana har take min kallon hadarin kaji……….

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Lallai kuwa nima zan so jin ta yadda wannan bakuwa take da kuma alkiblar da zata kalla🤔🍏🍒……

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Salon wannan zazzafan labarin kenan Mai taken YANKAN WUKA ko waye WUKAR take YANKAN? Mu nutsa a tafiyar labarin ina fatan Ubangiji ya Taya mini yadda na fara lfy ya ci Gaba da Taya mini har na K’are lafiya Don girma da darajar makwancin uban daki na ANNABI.

 

 

 

 

YANKAN WUKA

Hakkin mallakar ma na gidan iko ne kuma abin kiyayewa ne

 

 

 

 

Sadaukarwa ne ga dukkan Al ummar musulmi musamman Wanda suke fama da jinya gida da asibiti birni da karkara Ubangiji yasa ya zamo kaffara

 

 

 

ADDU A ne ga iyaye na guda biyu uwa da uba Wanda nakewa fatan Ubangiji ya yi musu alfarma da Rahama da gafara a Raye da kuma fake

 

 

Gaisuwa ne ga haj Saliha abubakar Abdullahi Zaria tare da haj Adama shehu Zaria tare da haj binta kassim kaduna anty Jamila yusha u sokoto aminci aminci

 

 

 

Gaisuwa ne ga haj binta sale muna Kara mika sakon ta aziyya gareki Allah ya Kara muku juriya da hakuri ya duba marayun Allah

 

 

 

Da sunan Allah Mai Rahama Mai jinkai salati da aminci Mara’s adadi zuwa ga fiyayyen halitta ANNABI MUHD S A W da ahalin gidan sa madaukaka da masu binsu da kyautatawa har izuwa ranar alkiyama

 

 

 

 

 

🗡️🔪🗡️🔪🔪🗡️🔪🗡️🔪🗡️

 

……… Zuwa wannan lokacin naji na soma gajiya da wannan bakuwa da taci na tankada keyar ta waje saboda samun wurin ta ya wuce makadi da rawa.

 

Mamakin kaina nake ta yadda na iya shanye wannan Dan k’aramin wulakancin nata. A yadda nake babu hakuri dai tamkar tari ko zawayi Amma wai na kyale nake kallon ta tana sharafin ta wata kill hakan baya rasa nasaba da tasirin Wanda ya kawo ta a zuciya ta Wanda nake bawa dukkan yarda da aminci ko da Ni din ba hakan ne Ra ayi na ba.

 

Na turo kofar na shigo inda na samu k’atada da waya a kunne Amma Ina shigowa Yana sauke ta a kunnen shi

 

Fuska ta ba yabo ba fallasa Amma ZUCIYA ta cike take fal da takaici da kuma fargaba Amma sai na yi kamar babu komai a tare Dani Amma kuma shuru na shi ya nunawa k’atada akwai magana wai gawa ta rike Mai wanka………

 

“My only kiyi hakuri Don Allah kin Gane ko?

Na zuba mishi idona ina kallon shi da sauraron shi Yana Fadin kin Gane ko?……

 

“Na Isa batsari da maraice ko gida ban shiga ba labari ya iso cewa akwai matsala kowa ya San abin yi wai barayi sun iso wagini har suna Shirin Karasowa cikin garin batsarin . Ban iya jiran komai ba na SHIGA gida na kwaso su baba na dauko su a mota na kawo su cikin garin katsina inda Inna take Fadin sun baro auta Raliya Dole ta zan zame Ni wai na dauko Mata yarta.

Baba yace kar na koma tunda Allah ya fiddo mu Raliya zata San inda ta fake kuma Allah shi zai zamo Mata tsani. Amma Inna ta fasa kuka tace ita Kam zata koma ta dauko yarta Dole na koma batsarin Don Nemo Raliya Amma Allah da ikon shi sai na yi gamo da motar barayin Nan sun kwaso Mata cike da mota suna ta sakin harsashin bindiga da son suyi kan Mai uwa da wabi…..

Ina lafe karkashin inuwar maina har suka wuce inda wannan matar da muka zo da ita ta Samu gudowa daga motar barayin ta auno a guje shine fa muyi taho mu gama tana kuka tana rokon na taimaka Mata na fidda ita daga yankin Nan shine na tausaya Mata na dauko ta muka bi ta sabuwar hanyar Nan ta dayi har muka samu isowa gida Amma fa tun a mota na kula kamar tana da tabin hankali Don kuka take Tayi tana Fadin an kashe Mata iyaye da yan uwa sai ita kadai Tayi saura ita yanzu ina zata saka Kanta? Shine nace Mata idan zata iya aikatau zan kawo ta gida na Tayi miki aiki tunda kina da tausayi nasan Zaki tausaya Mata Amma sai kawai naga tana kyalkyala dariya wannan shi ya nuna min tana da tabin hankali sai kawai na wuce da ita asibitin masu lalurar aka kuma tabbatar min da ta furgita ne akan abinda ta gani Dole sai dai ayi ta Mata magani har Allah ya Bata sauki Don haka kar ki damu da ganin action din ta ba na Mai hankali bane…….

 

Jikina yayi sanyi kalau naji ina tausaya wa yarinyar Nan shi yasa akace zato zunubi ko da ya zamo gaskiya . ……..

 

“Kai Amma na tausaya Mata my only Dole Kam take ciccin magani Ashe rarrashi take bukata……

 

“Wallahi kuwa Ni na San Zaki tausaya Mata don Allah ga Amanar ta Nan na kawo miki amana ce garemu Ni da ke nayi alkawarin nema Mata magani in Sha Allah……

 

“Babu komai in Sha Allah nima zan Taya ka Allah ya bamu ikon fita hakkin ta…….

Ban rufe baki ba sai ga kofar an turo inda bakuwar mu ta bayyana tana Rike da kayan abincin da na Kai mata ta kawo su Gaban mu ta dire irin a tunzure din Nan irin an Bata haushi ko an Bata Mata Rai…..

 

Muka bita da kallo Ni da k’atada Wanda ya saki baki Yana kallon ta ita kuma tana duban shi tana Fadin

“K’atada me zanyi da wannan abincin kamar wata zomo? Farar shinkafa da wani ganye biya biya ? Ni ? Allah ya sauwake wallahi ba zan iya cin wannan abincin ba ya shake min wuya kamar wata yar bursuna kafi kowa sanin bana cin irin wannan abincin……

 

“To yi hakuri Mai kike so kici yanzu?

Ya Fadi maganar Yana kwantar da murya cike da kulawa……

“Alkubus nake so sai rufaida yougurt Amma bana bukatar wata shinkafa can gatse gatse ….

Ta juya abinta muka bita da kallo Ni da k’atada Wanda yake Fadin …..

 

“Yi hakuri my only kin San Abu in akace ba na hankali bane sai hakuri bari na Tashi na samo Mata Rufaidan nasan kema Zaki bukata ko?…..

 

Na Mike ina duban agogon falon kafin na dube shi ina Fadin

 

“Dubi lokaci fa k’atada? Biyu saura zaka fita? Su masu siyar da Rufaidan Kai kadai suke jira? Kuma a wannan lokacin za a sama Mata Alkubus din? To bari na fada maka gaskiya matukar haukan yarinyar Nan irin wannan ne to ba zan yaudare ka ba wallahi Bata da muhalli a gidan nan Don Ni Kam akan hakan Rashin jini ne Rashin tsagawa ba haukan aljani daya ba in na aljanun da suke bangon Duniya ne zata Gane akwai inda haukan ma yake tsoron bayyana kanshi . Don haka idan har tana da zabin abinda zata ci to kwashe ta yanzu yanzun Nan ka mayar ta can batsarin gidan ubanta ko kuma ka mayarwa bandit din da suka dauko ta wata kill dama Allah ne ya zana bandit din sune daidai da haukan ta Amma ba Nan . Waye uban ta da har take Kiran wannan girkin da shinkafa getse gatse? Nifa na zage nayi maka shi ba talatu ba. Ko talatu Tayi ai yafi karfin gatse gatse……

 

Jikin k’atada yayi sanyi kalau ya koma ya zauna Yana Fadin

“Sai kinyi hakuri my only yaushe Zaki biyewa mahaukaciya? Bata da hankali duk abinda Tayi ita a ganin ta daidai ne ……

“Dole na biyewa mahaukaciya k’atada Don na takawa haukan ta burki don kar Nan Gaba haukan ta ya Raya Mata kwana a kan kirjin ka kaga Dole nice da ya jiki? To Amma gara tun yanzu ta Gane Nan ba gidan gyatumin ta bane ba kuma inda zata uhum ace Mata meye ba? Taimako kayi niya nima kuma har ga Allah nayi niya to tunda iskanci ne a cikin haukan gara kawai ka biya kudi a kula da ita can yar kutungu( gidan mahaukata) Amma nan gidan Kam tunda har ta iya wannan aikin na hankali wai Bata cin shinkafa getse gatse sai Alkubus to Ni ban yarda mahaukaciya bace in ma haukan ne to na iskanci ne……

K’atada yayi shiru Bai kuma tankawa ba na Mike ina Fadin

 

“Ruwan wanka fa a bandaki

Ya Mike ya wuce na bi bayan shi Ina karantar yanayin shi tamkar Mai shiga zuzzurfan tunani

 

Ina zaune bakin gado ya fito Yana sauya rigar bacci ya hau gado ya kwanta

Gamin babu wani abu da ya kuma waiwaya a gareni yasa nima na gitta bayan shi na kwanta

Na jima banyi bacci ba ina tunanin bakuwar mu inda na kula kadan kadan zai leko fuska ta. Hakan ya sa na rufe idanu na ba Don nayi baccin ba

 

Mintuna Sha biyar zuwa ashirin naji Yana magana a waya duk da ban iya fahimtar me yake fada ba

Ya gama wayar kafin ya Mike cike da sand’a tamkar wani barawo ko marar gaskiya ya Soma tafiyar Yana waigo baya da son ganin ko ana ganin shi?

 

Ya fice Yana Jan kofar a hankali Don kar Tayi karar da zata tayar Dani Bai sani ba yayi shuka Akan idon makwarwa…..

 

Yana fita nima na Mike nabi bayan shi can na hango shi Yana sauri Yana haska wayar shi abinda yayi matukar bani mamaki shine ganin Yana nufar dakin da bakuwar mu take . Nima sai na bi bayan shi har zuwa lokacin da ya tura kofar dakin ya shiga da sauri . Wannan shine Abu na farko da na Rike Wanda ya tabbatar min da abinda mijina k’atada ya fada min ba gaskiya bane . Domin kuwa inda gaskiya ne meye abun satar hanya? Kuma meye abin damuwa da matar da ta zamo mahaukaciya a talatainin Dare irin wannan? Shin me ya kawo shi dakin ta a yanzu? Ko kuwa Alkubus din da ta bukata zai girka Mata? Anya kuwa lamarin Nan babu lauje a cikin Nadi? Na iso bakin kofar zan tura na SHIGA sai na jiyo maganar da ta kusa saka Ni mutywa Don haka sai na tsaya cik na kasa motsawa Amma kuma jiki na ne ya kasa motsawa kunnuwa na suna cikin dakin bakuwar Nan suna nado min maganganun da suke watsywa tsakanin ta da k’atada duk dai Akan yadda ta shigo gidana da kuma shi Wanda ya kawo ta. Sai kawai naji ZUCIYA ta na tambaya ta wai yaushe ne maza zasu daina yaudara? Yaushe ne maza zasu kalli gaskiya suce gaskiya ce ba tare da sunyi Mata kwaskwarima da gyaran sunan ta na gaskiya ba? Abinda k’atada yake fadawa bakuwar Nan shi ya sa na mayar da hankali na kan sauraren su inda sai a yanzu naji sunan bakuwar a bakin shi yana Kiran ta da suna Deena. Mamaki na haduwar su yau kuma haduwar Tashin hankali har ya hardace sunan ta na Deena itama duk da haukan nata ta iya kiyaye sunan shi na k’atada har take iya fadar wai yasan cimar ta ? Wannan lullubin birin yau zan kware shi wallahi Ashe duk son da mace zata nunawa namiji baya Hana ya yaudare ta? Baya Hana ya ha ince ta? Baya Hana ya ci Amanar ta? Sai kawai naji hawaye Yana zarya a gurbin idona kafin na share ma naji maganar bakuwa Deena tana Fadin………..

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Lallai Kam an gaida maza masu kokari kan kokari Amma dai bari muji Don har yanzu a duhu muke tariya da sannu in Sha Sha Allah zamu zo ga warwara ……..

 

 

 

 

YANKAN WUKA wani murdadden Al Amari ne da labarin yazo a cure kuma a kulle Amma da sannu zamu baje komai kan faifai Allah ya bamu yarda da aminci da kuma lokacin da komai zai nuna Kansa.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

GIDAN IKO na ke cewa saduwar alheri

Close Menu