Ad Code

Dangantakar Zuci Hausa Novel Complete

Dangantakar Zuci Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

Dangantakar Zuci Hausa Novel Complete

BISMILLAHIR RAHMANIRRAHIM_*

 

*_dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah subhanahu wata’ala,tsira da aminci su sake tabbata ga shugaban halitta annabi Muhammad S A W_*

 

*_ina mai farincikin sake haduwa da masoyan rubutu na,sannan ina roqon Allah s w a ya sanya dukkan abinda zan rubuta ya zamo mai amfani mai amfanarwa cikin wannan sabon rubutu nawa_*

 

*_saidai wannan karon masu karatu sai kunyi min afuwa ba kullum ne ranakun da zan rinqa post ba,ranakun posting sune kamar haka in sha Allahu_*

 

*lahadi*

*talata*

*alhamis da juma’a*

 

 

 

*Babi na daya*

 

 

 

 

 

Tun daga cikin kitchen take iya jiyo muryarta cikin ihun kuka tana dosowa tsakar gidan,da sauri ta ajjiye wuqar hannunta ta fito daga kitchen din da nufin taryarsu tun kafin su su iso mata.

 

 

Rayyan ne akan gaba bayansa sabe da school bag dinsa,hannunshi daya riqe da tata school bag din,yayin da daya hannun nashi kuma yake riqe da hannun rumana dake digar jini,Raihana ce ke biye da su a baya itama goye da tata jakar idanunta jage jage da hawaye wanda har ya jiqa medicated glass din dake kan fuskarta.

 

 

Da sauri ummu ta qarasa ta karbi hannun rumana dake cikin na rayyan cike da fargaba take tambayar rayyan din wanda idanunshi suka kada sukayi jawur tamkar wanda aka zazzabgawa mari”garin yaya haka?,dame ta yanke?”ummu ta tambayeshi tana qoqarin tsaida jinin.

 

 

Daga kanshi yayi ya zabgawa raihana harara wanda jikinta yayi laqwas ta lafe a bayan ummu”raihana mana ummu,wai qawarta ce ta bata ajiyar reza ita kuma rumana ta gani ta karba a gunta zata fiqe pencil,garin fiqewar ta yanke hannu”

“Ashsha,ai na hanaku amfani da reza ko?,tunda dukanku kuna da sharpner”

“Ai tana sane wawiyar yarinya data karbi ajiyar kuma har ta bada wai aro” ya fada yana sake hararta duk da ta buya,ji yake kamar ya janyo raihana ya sake mammarinta kamar yadda yayi dazun.

 

 

“To ya isa,rumana kukan ya isa haka mana,dadina dake raaki,kai rayyan maza shiga bedroom dina ka dauko first aid boxs dinku”da sauri ya sabule jakar makarantar tasa ya shige parlour inda daga nan zai sadashi da dakin gadon.

Yar Sadaka Complete Hausa Novel

 

Cikin ‘yan daqiqu ya dawo hannunshi dauke da akwatin ya miqawa ummu,ta sanya ruwa ta fara wanke jinin kafin ta saka spirit ta soma wanke mata,aifa rumana an samu abunyi,bare baki tayi sosai ta dinga sharbar kukanta yayin da rayyan da raihana baki daya suka rasa sukuni suka dinga zuba mata sannu tamkar su maido ciwon jikinsu.

 

 

Raihana ce ta gaza daurewa tace cikin qwalla” ummu da zafi don Allah ki mata a hankali”,da sauri rayyan da ya harde hannayensa a qirji yana kallonsu idanunsa sun kada ya sake zuba mata harara”yi mana shiru,duk bake kika jawo mata ba”,”rayyan ya isheni haka nan”ummun ta tsawata masa,suna tsayen ta kammala gyara matan rayyan ya janye hannunta zuwa falo raihana ta kwashi jakankunansu tabi bayansu,ummun ta bisu da kallo,idan da sabo tuni ta saba,irin wannan damuwa da sukayi da junansu,cikinsu babu wanda keson wani abu ya samu dan uwanshi kada ma rayyan da rumana suji labari,hakan ya sanya cikin makaranta ko unguwa wasu ke musu laqabi da AMINAN JUNA.

 

Ciken tray daya ta shirya musu abincin,don ta sani lokuta irin wadan nan tare suke cin abinci,musamman yau da aka jangwale rumanan sarkin raki.

 

 

kan kujera kuwa ta tadda rumana a lafe kamar wadda ke ciwon jiki,yayin da rayyan ke gefanta hannayensa dauke da papers wanda da alama na neco da suke zanawa ne yake sake dubawa,ajjiye tray din tayi wanda ke dauke da shinkafa da miya,gefe kuwa hadin salad ne

“A sauko aci abinci maza kada lokacin islamiya yayi”cewar ummu,ai kuwa sai rumanan ta sake lafewa tana ahirin zubda wasu sabbin qwallan,sarai ummu ta fahimci me take nufi tunda tai hakan,ko dama can kullum da daru rumanan ke tafiya makarantar walau islamiyya ko boko,sauqinta daya rayyan da take shakka,duk da sabon dake tsakaninsu hakan baisa ta rainashi ba.

 

 

Tana shirin neman raihana sai gata ta fito sanye da unifoarm din islamiyar tasu baqar doguwar riga da farin hijabi,yarinyar na da nutsuwa da son makaranta,sau tari takan fahimci abinda ya kamata tun kafin a furta duk da qarancin shekarun nata da basu shige tara da ‘yan watanni ba

 

 

“Oya,sauko muci abinci”rayyan ya fada yana duban rumana,ta kyebe baki don babu damar yin musu haka ta janyo jiki ta sauko qasa inda ta tanqwashe qafarta kamar yadda duk sukayi,hannunta ta kalli kana ta kalli rayyan,shima dubanta yayi ba tare da yace komai ba ya soma diba yana bata a baki,ya juya zai dauki ruwa ya lura raihanan ma ba wani cin kirki tajewa abincin nata ba,sai yaji tausayinta ya kamashi da ya tuna marin da ya mata dazu,hannu yasa ya karbe cokalin hannunta ya hadasu duk su biyun ya dinga basu,ummu dake gefe wadda ta idar da sallar azahar tana kallonsu fuskarta qunshe da murmushi,zuciyarta cike fal da farincikin yadda rayyan din ke kulawa da qannen nasa.

 

 

Sai da suka qoshi su duka kana ya tasa rumana a gaba ta shirya fuskarnan babu digon annuri don kada ta kawo wargin cewa ba zata je ba.

 

 

Hakan bai sanyata tayi shiru ba lokacin da taga ya sanyasu a gaba suna qoqarin ficewa a gidan ba tare da shi ya sanya nashi unifoarm din ba,fuska a narke tace”ya rayyan….yauma mu kadai zamu je kai ba zaka je ba?”dariya ce taso kubce masa ya dan dake”amma da karatu ne wannan rumana yaci kin dade da haddaceshi,wata na nawa da yin sauka aka sallamemu?,ranar saukan ba ke na bawa ajiyar zayyanata ba?”shiru tayi ba tare da tace komai ba tana mai ci gaba da son zubda qwalla,”kinayin kuka ni da raihana ba ruwanmu da ke,ke bakyason kema wataran ace kinyi saukar kamar ni?”,”inaso mana ya rayyan” xto dole ki dage da zuwa makaranta kinji ko?”

“To amma ya rayyan idamukayi sauka shikenan mun daina zuwa ko?”

“Qwarai ma kuwa my angel”da yake wani lokaci haka yake kiranta,murna ta soma yi jin ance sun daina zuwa da sunyi sauka harda rawa da yake ba baya ba wajen son rawa,shi da raihana na gefe na kallonta raihana nata dariya,da haka ya kada kansu suka fice yana jansu da labarai masu dadi dasa dariya don su kuma sakewa har ya kaisu qofar makarantar dake bayan layinsu ya juya ya komo gidan don yayi wanka

 

 

 

*mrs Muhammad ce*

 

 

DANGANTAKAR ZUCI

( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_)

*NA*

 

*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*

 

*watpadd:huguma*

 

© *haske writers asso

(Home of expert and perfect writers)

 

 

 

*_An karbo daga uwar mumunai ummu abdullahi wato nana Aisha R.A tana cewa:Manzan Allah S a w yace “haqiqa dukkan ayyuka basa yiwuwa sai da niyya,kuma kowane mutum akwai abinda ya niyyata”(ma’ana ladan aikinka da sakamakon da zaka samu ya ta’allaqa da irin niyyar dake zuciyarka akan aikinka,irin niyyarka irin sakamakonka agun ubangiji)*

_ruwayar bukhari_

______________________

 

 

*babi na biyu*

 

 

 

 

Hikimar ubangiji ce haduwar jini qauna da shaquwa tsakanin wane da wane,yakan sanya irin wannan jituwar da qaunar juna tsakanin bayinsa,hakan itace ta kasance tsakanin wadan nan bayi nasa guda uku wadanda suka fito daga mabanbantan yare har ma da qabila,wanda daya daga cikinsu ma suka samu banbancin qasar haihuwa a tsakaninsu

 

*Alhj yusufa adamu*

 

Haifaffen jamhuriyar nijer,cikin garin DIFFA,garine dake da qarancin jama’a cikin duka qasar ta nijer,tattalin arziqin yankin ya ta’allaqa ne kan noma da kiwo,mazauna garin sun hada da hausawa,fulani da larabawa.

 

 

alhj yusufa na daga cikin jinsin fulani wadanda a nan mukafi kira da sadakar yalla,duk da yake ruwa biyu ne shi,saboda asali mahaifiyarsa na daya daga cikin larabawan dake zaune cikin yankin wanda auratayya ta hadata da adamu mahaifin alhj yusuf.

 

 

Bai fuskanci wani qalubale wajen samun auren rahinatu ba saboda suna da wani yanki na sarautar garin diffa,mahaifin adamu a lokacin shine wazirin sarkin garin na diffa wanda ko bayan rasuwarshi sarautar bata bar gidansu ba adamu dinne yaci gaba da jan ragamar,kasancewarsa d’a na fari kuma babba a gurin mahaifinsu.

 

 

Yusuf tun yana qaraminsa zuciyarsa da tunaninsa sunfi ta’allaqa ga harkar siye da siyarwa wato kasuwanci,wanda hakan shi ya zama sanadiyyar haduwar jininsu da qanin mahaifinsa muhammadou wanda ke kasuwancin dabino da cukui tsakanin nijeria da niger.

 

 

Yadda ya lura da hazaqar yusuf da qulafucinsa na son kasuwanci yasa ya fara daukarsa rakiya zuwa nijeria tun shekarun yusuf din basu taka kara sun karya ba,cikin qanqanin lokaci sai ga yusuf din ya zama cikakke kuma gogaggen dan kasuwa tsakanin nijeria da nijer.

 

 

Tun zuwan yusuf na farko qasar nijeria ta burgeshi,yanayin garin al’ummarsa wayewarsu da kuma mu’amalarsu da jama’a,musamman da ya soma shiga garin kano ta dabo ci gari jalla babbar hausa,wanda da iyakacinsu sokoto katsina,harkarsa a kano sai tafi garawa ta kuma fi bada armashi kasancewarta cibiyar hada hadar kasuwanci,hakan ya sanya bayan cukui da dabino sai yake hadawa da mazarqwaila da sauran abubuwa da mu bamu da su.

 

 

A lokacin cikin kasuwar kwari suke sauka inda anan ya hadu da alhj *dalhatu attahir* wanda yake da makekiyar rumfa,nan cikin rumfar tasa yake ajjiye kayansa idan yazo kafin ya rarrabawa ‘yan kasuwa da masu sara.

 

Kunsan hali sai yazo daya ake abota,yadda alhj yusuf yake mutum mai matuqar kirki,gaskiya riqon amana taimako da son jama’a haka alhj dalhatu take,nan da nan abota da shaquwa mai qarfi ta shiga tsakaninsu duk da bambancin nau’in kasuwanci dake tsakaninsu,saboda shi alhj dalhatu yana saida atamfofi ne kala daban daban kaama daga qarama mai sauqin kudi zuwa mai tsada,sau tari alhj yusuf kan karbi atamfofin daga hannun alhj dalhatu idan zai koma qasarsa nijer ya tafi da su ya saida,ko kadan alhj attahiru bai karbar kudin atamfofin daga hannunshi har sai ya siyar ya sake dawowa nijeria duk da cewa bawai baida kudin bane babu ma zancan matsalar kudi tattare da shi da kudinsa a hannunsa,tafi tafi sai Allah ya sanuyawa harkar atamfar tasa albarka wanda babu dadewa ya bude babban shago na atamfofi zalla,ba’a dauki wani dogon lokaci ba shagon ya karbu cikin garin diffa da sauran maqwaftan garin,don wani lokaci wasu tun daga dosso tillaberi niamy ko zinder zaga ga sun shigo sari,hakan ya sanya ya sake bude wasu shagunan cikin wadan nan garuruwan,wadansu nashi shi kadai wadansu kuma shi da alhj dalhatu ne.

 

*Alhj dalhatu*

 

Haifaffen qasar nijeria ne cikin garin kano qaramar hukumar kano municipal,kowa ya sani cewa ‘yan cikin gari a kano irin unguwannin da suka hada zage,daneji,marmara aisami,qoqi makwarari da sauransu mafi yawancinsu kasuwanci shine babbar sana’arsu,to haka yake ga alhaji dalhatu shima kasuwancin ya gada daga wajen mahaifinsa alhj attahiru,alhj dalhatu shine da na hudu a gidansu a cikinsu su goma da Allah ya bawa mahaifinsu wanda yake da matan aure guda biyu,maza su shida mata hudu,wannan kenan.

 

 

*alh bukar ibrahim*

 

 

Shima haifaffen nijeria ne cikin garin maiduguri qaramar hukumar kwaya kusar,familynsa asalinsu iyali ne ga malam muhammad al’amin elkanemi wanda ake kira da shaihu laminu wanda asalinsu daga yankin larabawa ya fito ya zama kuma ya zauna a kukawa,babban malami ne da ya taimakawa barno tun zamanin da fulani suka zo yaqar bare bari,mutum ne da ya bada gudun mawa mai yawa cikin qasar borno baki daya,daga baya ne da zuri’ar tayi yawa aka samu sauyawar muhalli gun wasu daga cikin zuriyyar tasa.

 

 

Shi din ma kasuwanci ne yake kawoshi kano,yana kusuwancin huluna ne cikin kasuwar kwarin,wanda ya zama tamkar shi dila ne na huluna,yana rabasu ga manya da qananun ‘yan kasuwa,to shi din ma dai karamci da mutuncin alhj dalhatu yasa yake sauke kayansa a rumfar tasa kafin ya gama rabawa wanda zai bawa din,anan tasu tazo daya su ukun baki daya,alhj dalhatu alhj yusuf da kuma alhj bukar.

 

 

Duk alaqar da aka ginata domin Allah to da ikon Allahn kuwa shike riqe da ita,babu wani abu da zai bata ta,hakanne kuwa ya kasance tsakaninsu,aminci mai sunan aminci,shaquwa mai sunan shaquwa da yarda da juna ita ta wanzu tsakaninsu,mutanen da suka sansu daga baya da yawansu sun dauka ‘yan uwane na qut da qut,tunda ba zaka kallesu kace mahaifiyarsu daya ba saboda bambancin harshe da siffa.

 

 

Shi alhj yusuf fari ne tas har yellow yake,sumarsa a kwance take kamar ta larabawa,hakanan harshensa ya dan karye wanda dole idan yana hausa ka fuskanci ba tsantsar bahaushe bane,yayin da alhj bukar ya kasance wankan tarwada,fuskarsa na dauke da tsagu qwaya daya daga hancinsa zuwa goshinsa irin na bare bari,shima alhj dalhatu baqine kamar yadda akasan ainihin kalar fatar bahaushe na usuli.

 

 

A lokacin daga bukar har dalhatu babu wanda yayi aure a tsakaninsu sabanin yusuf da yake da aure a lokacin har matarsa ma na dauke da juna biyu wanda take ‘yar garinsu ce yarensu kuma daya.

 

 

Yau da gobe sai kasuwancinsu dukka yayi qarfi cikin kano,hakanne ya sanya tilas alhj yusuf ya dauko matarsa fatimatou suka dawo nijeria kuma cikin garin kanon tunda shi yafi alhj bukar nisa,alhj dalhatu yaso ya samu gida nan kusa da shi saidai hakan bata samu ba kasancewar yawancin cikin gari a cike yake,babu wani fili da zaka iya siya,saidai kasai gida ka rushe idan kana so kayi irin ginin da kake so,to ko samun gidan ma aiki ne don yawanci basa yarda su siyar din,ba don sansu ba ya samu gida cikin unguwar sharda mai kyau da girma ya ajjiye fatima a ciki.

 

 

Basu cika shekara a nijeria ba fatima ta haihu ta samu yaro namiji,santalelen yaro kuwa wanda ya kwashe kamannin fulanin buzaye da kuma kakarsa rahinatu wadda ta fito cikin jinsin larabawa,jajir da shi suma har goshi,fafin irin murnar da alhj dalhatu da bukar suka nuna bata baki ne,kusan sunfi ma uban dan doki da murna.

 

 

Sosai yusuf ya rufe idonsa shi da mai dakinsa fatima suka dinga yi musu gori don suji haushi suyi aure suma,don tace ta gaji itama tana da buqatar qawaye(wato matan da zasu aura din kenan)dariya suka dinga yi suna fadin su sha kuruminsu sun kusa ai.

 

 

Allah bai nufi auren nasu ba sai bayan shekara biyar da haihuwar RAYYAN wanda yaci sunan mahaifin kakansa,kusan tsiran wata guda ne tsakanin auren dalhatu da bukar,dalhatu ya auri rabi’atu bukar ya auri fanna,duk da a maiduguri akayi bikin hakan bai hanasu zuwa ba dukkansu.

 

 

Sai da suka shekara bibbiyu sannan sukayi haihuwar fari,rabi’atu ta samu UMMA RUMANA fanna ta samu RAIHANA,shekarar rumana hudu rabi’ah ta kuma haifa ,yusuf suna kiransa khalifa da abubukar(bukar) suna ce masa amir,fanna ma ta sake haihuwa ta haifi diya mace wadda zainaba,fatima ce tun daga kan rayyan haihuwar bata kuma tsaya mata ba,ta haihu sau hudu maza biyu mata biyu amma dukkansu mutuwa suke,tun tana damuwa har ta miqa lamarinta ga Allah,hakanne ya sanya ta janye umma rumana wanda ya kasance duka weekend din duniyaa gidan takeyi,bata komawa gida sai ran monday,idan aka daukota daga makaranta sai a wuce gida da ita sai kuma wani qarshen makon.

 

Zumunci ne sosai tsakaninsu har ma da matansu da ‘ya’yan nasu,musamman gidan alhj dalhatu da gidan alhj yusuf,kasancewar alhj bukhar sunyi nisa saidai saqon gaisuwa da waya a tsakaninsu.

 

 

Sannu a hankali arziqinsu ke dada yalwata wanda hakan ya sanya tilas alhj bukar ya dawo kano shima kusa da ‘yan uwansa a lokacin raihana da umma rumana na da shekara takwas a duniya rayyan na da sha biyar,unguwarsu daya da alhj yusuf saidai akwai ‘yar tazara tsakaninsu.

 

 

*mrs muhammad ce*

 

DANGANTAKAR ZUCI

( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_)

*NA*

 

*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*

 

*watpadd:huguma*

 

© *haske writers asso

(Home of expert and perfect writers)

 

 

*Manzan Allah S a w yace:duk wanda yayi salati a gareni sau goma da safe sau goma da yamma cetona zai riskeshi ranar qiyama*

 

_duba sahihut targib wat tarhib mujalladi na daya shafi na 372_

____________________________

 

 

*Babi na uku*

 

 

 

 

 

Mai glass shine sunan da rumana ta fara kiran raihana da shi da fari farkon tarewarsu,kasancewar da glass din raihana take zuwa makaranta saboda lalurar rashin ganin abun da ke can nesa da kyau da take fama da shi.

 

 

Lokaci lokaci raihanan na zuwa gidansu rumanan,musamman idan abbansu ya kaisu ko kuma mamansu zata je,hakanne yasa suka dan saba da rumanan duk da rashin son magana irin na raihana,yarinyace da bata qiriniya ko rashin ji ko kadan,hakanan surutu bai dameta ba,iyakacinta da abu kallo sai ko murmushi,sabanin rumana dake da surutu rawar kai tsokana da rashin ji,hakan ya sanya tun a lokacin hajiya yaaya kakarsu rumanan wadda ta haifi alhj dalhatu tasu tafi zuwa daya da raihana,don lokaci lokaci itama suna zuwa mata

 

 

Sam bata damu da zuwa gidan alhj yusuf ba duk da cewa suna kusa,hakanan ko rumana taje weekend bata damu da zuwa gidan ba,haj fatimatou takan alaqanta hakan da ko don bata da ‘yar budurwa ne sai rayyan kadai dake gabanta.

 

 

Yawan zuwan rumana gidan hakan na yiwa rayyan dadi da debe masa kewa,don lokacin ne yake samun abokin hira da wasa kasancewarsa ba mai son yawace yawace ba ya sanya bai da wani aboki,hakanan yanayin unguwar tasu ma bai wani jama’a ta cika ba,jama’ar da take da ita kuwa kowa na qule cikin gidansa ahi da nasa iyalin.

 

 

Wannan shine musabbabin shaquwa mai qarfi da ta shiga tsakanin rayyan da rumanan,wanda har takai ta kawo odan bata zoba shi yana zuwa gidansu yayi weekend dinsa hankalinsa kwance kasancewar gidansu rumanan akwai yara ba kamar nasu gidan ba da yake shi daya qwal

 

 

*dukkan mai rai mamaci ne*

 

 

Wannan haka yake kuwa,domin alhj bukar bai wuce shekara daya da zuwa dawowa garin kano ba Allah ua yi masa rasuwa,a lokacin duka duka shekarun raihana tara a duniya.

 

 

Hakan ya faru ne sakamakon hadarin mota da ya samu daga hanyar mai duguri zuwa kano,wanda dama yakan je garin nasu lokaci lokaci yaga dangi kuma ya karbo huluna gurin mutunen da yake siya a gurinsu,basu kai ga qarasowa ma cikin garin kanon ba lamarin ya afku,wanda sai gawarsu aka qarasa da ita asibitin koyarwa na malam aminu kano.

 

 

Mutuwar ba qaramin girgiza zuriyar uku tayi ba baki daya,kada ma mai dakinsa alhj dalhatu da alhj yusuf suji labari,kai kace mahaifansu ne suka rasu,sunyi matuqar gigita,to amma ya aka iya da lamarin ubangiji tilas suka haqura suka rungumi qaddarar ubangiji.

 

 

Bayan share makoki ne ‘yan uwan fanna sukayi niyyar tafiya da ita amma alhj yusuf da alhj dalhatu suka kafe kai da fata kan cewa a barta a dakinta tayi takaba kamar yadda addinin musulunci yafiso,tunda dai gida na bukar ne mallakinsa ne,sanin irin alaqar da take tsakani suka janye qudurinsu ba haufi suka barta a gidanta tayi takaba,sun barta da ‘yan uwa mutum biyu masu tayata zama.

 

 

Cikin zaman takabar ta ta qara yadda da jadda da girman abota dake tsakanin wadannan mutane guda uku,don babu wani abu da wani cikinsu zai siya bai hada da gidan bukar ba,ficika basu bari an taba cikin dukiyar bukar din ba da nufin a ciyar da iyalinsa,babu abinda suka rasa bangaren ci sha sutura da buqatun rayuwa na yau da kullum,haka matansu ma kullum suna tafe,banda rashin mai gidan da sukayi babu wani rashi da suka dandana.

 

 

Tana kammala idda kuwa suka dawo don tafiya da ita din,a nan ne su alhj dalhatu suka gabatar musu da buqatarsu na a bar musu raihana da zainaba zasu kula da su,mutanen nada qima da daraja a idonsu babu abinda zasu tambaya su kasa basu kamar yadda suka san ko bukar na raye bazai iya hanasu komai ba,sun amince zasu bada daya amma dayar saidai suyi haquri don dangin mahaifin bukar ma sun matsa suna son riqon.

 

 

Ba yadda suka iya haka suka amshi raihanan don a son ransu a basu duka kowa ya dauki dai dai,alhj dalhatu shi yaso karbeta alhj yusuf yace haba ba za’ayi haka ba,kai da gidanka ke cike da yara,ni kuwa da muke mu uku daga ni sai fatima sai rayyan,ai a tausaya mana ko?,bai ja ba alhj dalhatun yace ba komai ya riqe din don da gaskiyarsa,amma fa shima ba za’a samu ladan babu shi ba,shi zai dauki nauyin karatun raihanan kamar yadda ya dauke na yaransa da rayyan ma baki daya,baice komai ba bayan godiya don yasan abotarsu tafi gaban haka don daga Allah take.

 

 

Komawar raihana gidan alhj yusuf ita ta kawo komawar rumana ma baki daya ta bar yin weekends kawai ta koma ta din din din,hakan ba qaramin dadi ya yiwa raihana na don jininsu ya hadu sosai da rumana,tanason surutunta iyayinta da rawar kanta,sai ta sata gaba ta yita kallo tana bata dariya,haka ma hajiya fatima ba qaramin dadi taji ba,ganin an share mata hawayen yara da bata samu ba,ta kamasu qam ta riqesu,duk qwaqwqwafinka baka isa kace ba ita ta haifesu ba,tana matuqar ji da su.

 

 

Hakanan rayyan sai yake jin shima yanzu gidansu akwai mutane ba kamar da ba da yake shi daya qwal,suka zama abokansa musamman rumana da shaquwarsu dama tafi qarfi kasancewar sun dade tare.

 

 

Wannan shine tarihin wadan nan iyalai guda uku,gidansu RUMANA RAIHANA da kuma RAYYAN

 

 

*mrs muhammad ce*

 

📚📚📚✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼

🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊

💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔

( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_)

*NA*

 

*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*

 

*watpadd:huguma*

 

© *haske writers asso*💡

(Home of expert and perfect writers)

 

 

 

*An karbo daga usman dan affan R.A yace:manzan Allah S A W yace”duk wanda ya sallaci isha’i acikin jam’i tamkar yayi tsaiwar dare ne ta rabin dare,wanda kima ya sallaci sallar asuba cikin jam’i tamkar ya raya daren ne baki dayansa”*

 

_muslim ne ya rawaito_

________________________

 

*babi na hudu*

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tafe yake da ‘yar sassarfa har ya qaraso bakin get din gidan nasu,bai wani saurari a bude masa qofa ba ya tura ‘yar qaramar qofar dake maqale da madaidaicin get din nasu,ba bata lokaci ya bayyana cikin ‘yar madaidaiciyar harabar gidan nasu dake shimfide da interlock,wadda motoci uku kawai take iya dauka,duk da ba girma ne da ita mai yawan gaske ba amma sai ta baka sha’awa,don qawace take da shuke shuke da kuma wadatar tsafta.

 

 

Tsaye suke cirko cirko bakin motar,daga raihana har rumana uniform ne a jikinsu,raihana na goye da jakar makarantarta daya hannun nata kuma riqe da lunch boxs dinta,yayin da daya hannun nata take riqe da lunch boxs din rumanan.

 

 

Ita kuma rigimammiyar na sabe da tata jakar makarantar,kai maqale kan kafadarta tana sharbe qwalla.

 

 

A hankali dariya ta subucewa rayyan,tabbas mai hali baya fasa halinshi,babu ko shakka yau ma darun tafiya makarantar akeyi da rumana.

 

 

Ya qarasa inda suke tsaitsaye su da auwal wanda abba yusif ya daukeshi don kaisu makaranta duk sanda baya gari ko ya fita kasuwa da wuri,don yace rayyan yayi qanqata da driving tunda duka duka shekarunsa basu wuce goma sha shida ba.

 

 

Tun kan ya qarasa ta hangoshi da gudu ta ratsa ta gefan motar ta nufeshi,ba bata lokaci ta maqalqaleshi tare da sakin kukanta baki daya

“To ya isa?,me kuma aka yi miki rigimammiya?”

“To yaya ba kaine ba,kayi tafiyarka bayan kasan da makaranta,kuma gashi ummu tace mu biyu yau zamu”,”amma dai rumana kinsan exams ke kaini makaranta kuma na gama nayi candy?,me kuma zanje nayi?”ta sake barkewa da kuka tana fadin” “Nima yaya na daina zuwa tunda ka gama,muyi zamanmu a gida”fuska ya dan hade don uasan darun mutuniyar tasa sarai,indai ba haka yayi mata ba ba za’a daidaita ba”a’ah,kina so muyi fada kenan?”kai ta girgiza tana kebe baki”good,me yasa kullum ke ke qin makaranta?,kin taba ganin rumana na kukan zuwa makaranta?”nan ma ta girgiza kai”kina son mu bata na daina yi miki magana?”da sauri ta sake sakin kuka tana bubbuga qafa tare da fadin”a’ah…a’ah”murmushi yayi a boye don yasan abinda tafi tsana ya fada kenan zai daina kulata.

 

 

“Ok to daga yau kada ki sake cewa ba zaki je makaranta kina jina ko?”tace “to”

“Promise?”

Kai ta gyada kana yace “da kyau”ya miqe yana amsar lunch boxs dinta daga hannun raihana ya damqa mata,ya yiwa auwal magana ya bude motar ya kaisu,sai ta ja ta sake cogewa tana narai narai da ido.

 

 

“Rumanaaaa…ya kuma akayi?”

“Nidai yaya ka rakamu..makarantar babu dadi yaya”

“Rumana baki ganin….”

DA sauri ta katseshi ta hanyar bubbuga qafa da shirin wani sabon kukan”don Allah yaya”.

 

 

Baya son kukan da take tayi,kuma yasan halin rumanan da kafiya,hakanan kayan motsa jiki ne a jikinsa riga armless da boxer,idan yace zaya koma ciki kuma canzo kaya zasu makara ne kawai,don haka baice komai ba ya bude qofar motar yace raihana ta shiga,ta fara shiga rumanan ta shiga,yana shirin rufe murfin motar ta qiya dole shima bayan ya shiga,kafin sukai makaranta sai gashi baki ya bude tana ta zuba masa hira shi kuma yana biye mata tamkar ba ita ke faman sharar hawaye ba dazun.

 

 

Bata yarda ta barsu sun koma ba sai da ya dauki alqawarin tare da shi za’a zo daukarsu,cikin motar ya dinga murmushi shi kadai yana tuna rigima irin ta rumana,shi kansa yana jinjina shaquwa irin tasu,shi yasa ko gidansu baya yadda ta tafi da zummar kwana saidai su tafi tare ko su yini su dawo

 

*************

 

shigowarsa ta uku kenan yana tambayar ummu su rumanan basu dawo ba?,dubarsa tayi tana saka jug na lemon zobo da ta hadawa abba cikin freezer

“Basu dawo ba,ina zaton kwana fa zasuyi,ka dauki abincinka kawai kaci,don ko sun dawo dare ya riga yayi,qila ma sunyi bacci”

“Kwana ummu?”

“Eh,da matsala ne?”,ba mai yawan son jan zance bane sai kawai ya girgiza kai yace ba komai ya juya ya sake ficewa

 

 

Tana zaune ita daya a falon, itama gidan ya mata shiru da yawa saijin sallamarsu tayi,rayyan ne a gaba riqe da hannun rumana wadda dankwalin after dress dinta ke hannu,kitson da suka tafi a yi musu acan gidansu gashinan rangadau a kanta,saidai idon nan yayi jazur da alamu kuka ta sha,raihana na binsu a baya saidai jikinta ba qwari ko bacci ta fara ya tattagosu?.

 

 

Riqe baki ummu tayi tana duban rayyan tare da fadin “daga ina?”

“Daukosu mukaje mukayi,lawan ya rakani”ido ta zare kana ta rufeshi da fada akan saboda me zaiyi haka?,tana cewa can ma gida ne kamar nan,kuma yau juma’a gone da jibi duka ba makaranta?

“Kiyi haquri ummu,gobe da jibin ne kawai naga muke zama tare,ragiwan kwanakin duka suna makaranta”abinda ya iya fadi kenan ya zube saman kujera

“Sai kace ba gid daya kuke kwana ba?ko weekend din cewa akayi ta qare ne,to naga yadda zakayi idan lokacin tafiyarka yayi”ta fada tana janyo wayarta ta nemo lambar hajiya rabi’ah maman rumanan ta kirata

 

 

 

lumshe ido yayi, yayi shiru don ko maganar tafiyar baiso,idan banda baba muhammadou da ya matsa a gida zai qarasa karatunsa shikam.

 

 

Gaisawa suka fara yi da haj rabi’ah kana tayi mata qorafin barin rayyan ya taho da su raihana

“Daina bata bakinki hajiya,ko rayyan baizo ba dama komai dare nayi niyyar dawo miki da yaranki,nikam bazan iya da su ba,kuka ta zauna dirshan tanayi tana kiran sunansa qatuwa da ita kamar wata yayayya,taqi cin abinci ganin haka yasa raihanan ma ta kasa ci,a haka yazo ya taddasu nace su tafi Allah ya raka taki gona”

Murmushi haijya fatima tayi”to ai shikenan,a gaida sauran yaran da abbansu”

“Zasuji in sha Allahu,Allah ya bamu alkhairi”

“Ameen sai da safe”

 

 

Ta ajjiye wayar tana dubansu,wuni daya tak duk sunyi wani fiqi fiqi dasu su ukun baki daya,damuwar ayyan da rumana ta hada har raihanan duka,duk sai suka bata tausayi don tasan nan da dan qanqanin lokaci zasuyi mai dalili.

 

 

Ba abinda ta kuma cewa da su illa kitchen da ta shiga kai tsaye raihana ta bita a baya ta tayata daukar plate ta hado musu abincin ta ajjiye musu,tana gefe tana kallonsu har suka kammala

 

Close Menu