Ad Code

Bakin Kishi Hausa Novel Complete

Bakin Kishi Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

BAƘIN KISHI

 

”PAID BOOK #200 ONLY*

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

*📝NOTE Ada banyi niyar fara buk ɗinnan yanzu ba gaskiya naso sai march na fara so lura yawan ƙorafin wasu da nuna zallar soyayyarsu ga wannan buk ɗin yasa naɗan duba kuma nayi nazarin wasu Abubuwa haƙiƙa idan nabarshi sai A march zan fara to typing ɗinsa zaijani zuwa Appril, April kuwa watan A zumin ne insha Allah to kunga bazai yuba naja typing harciki Ramadan shiyasa na ƙarɓe ƙorafin ku, kuma nima na nazace wasu Abubuwan to gadai yanan nafara yau SATURDAY 26/2/2022 FE BRUARY DA MISALIN 11:54 p.m ,, kadafa kuce nayi typing dare ina malam so my malam yaɗan yi tafiya ne inacikin kewa hakan yasa naɗan tsaya wannan time ɗin dan baku nishaɗi…… GARGAƊI—-

Zazzafar Kishi Hausa Novel Complete

 

Banyarda wata ko wani ya sauyamun Akalar littafi ba, labarin zainuna tsantsar kishi ne dam illar bijirewa maganar iyaye Allah yasa mu Amfana da darusukan da nakeson koyarwa Aciki kuma Allah yasa marasa kyau masu hali irin hakan sudaina, A koda yaushe burina nakawo Abunda zai Amfanemu bawai dan yabamu nishaɗi ƙaɗaiba, Allah yasa mudace*

 

 

 

 

 

 

 

 

*NASA DAUKAR GA DIKAN MASOYANA*

 

 

 

 

 

 

_TARIN YABO DA JINJINA GAREKI MY SWEET MARYAM INAJI DAKE FA,,,, FATANA CIKIN WATANNAN MUSAMI TWINCE GAREKI

 

 

 

 

 

 

 

JINJINTA GADIKAN ILAHIRIN MEMBERS NA ƘUNGIYAR ROYAL,,,,, DOLE NASAKU MEMBERS NA NOVELS OF MUJAHEEDAH,, INASONKU OVERRR…..

 

 

 

 

 

*TAYAMA ZANYI SUYA NA MANTA DA ALBASA?? AI SAKI MY BESTY QUEEN MARYAM SANUSI WANNAN DOLE NE DOMIN KECE FITILA TA DAKE NAKE RAWAR GABAN HANTSI,, INAMIKI SO NA MUSAMMAN*

 

 

 

 

 

 

 

_BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM_

 

_^DIKAN YABO DA GODIYA SUNTABBATA GA MABUWAYIN SARKI MAIRAYAWA SANDA YASO DAMA ƊAUKA SANDA YASO, INA GODIYA GA ALLAH DAYA SAKE BAN IKON SAKE RUBUTA WANNAN SABON LITTAFIN NAWA MAITAKEN BAKIN KISHI_

 

 

 

 

*MARUBUCIYAR °•° MAIZAMAN KANTA “PAID BOOK” DOCTOR HEESHAM “”PAID BOOK” BARRISTER KHALEEL FREE BOOK– RAUNIN MACCE BAYA HANA ƊAUKAR FANSA, FREE BOOK– SAINA KASHE MIJINA FREE BOOK– FAHAERT HOT LOVE FREE BOOK,,, SO SIRRIN ZUCIYA– AND BAKIN KISHI!!! “”PAID BOOK”” IS LANDING…….. MUJAHEEDAH (MATAR MALM) CE KADA KUMANTA KUMA AMMYN KHAUSAR…*

 

 

 

 

 

 

FREE 🅿️ 1 TO 2..

 

 

 

 

 

 

Wani kyakykyawan gaye nagaban kwatance na hanga yana Zaune kan resting chair gefen sa ƙaramin stoll ne ɗauke da drinks na kwali sai kofin glass, lokaci lokaci yakan ɗauka ya kurɓi lemon dika hankalinsa nakan jaridar dake hannunsa, Sanye yake cikin t.shourt baƙa da gajeren wando trozer baki,

 

 

 

Idanuwansa farare sol kamar madara da zara zaran giran idanuwa, bazaka kirashi baƙi ba, haka kuma ba zaka kirashi fari ba, baida tsawo kuma baida gajarta gayanan dai dai dai misali,

 

 

 

Lips ɗinsa pink ne bakinsa ɗan karami kamar Antsaga da reza,

 

 

 

Hunmmmmm bari dai nabar mukushi hakan readers dan harna ga su o.o Ana haɗiye yawo to wannan mallakar wata ne watar ma wadda keda baƙin kishi!!! idan ko dakwai wadda zata iya to bismillah badai ruwan Mujaheedah ɗauko rahoto ne kawai nawa……..

 

 

 

 

Lunshe idanuwa kawai yake wadikan Alamu yanajin daɗin ya nayin,

 

 

 

 

 

_•••LABARI YAKORO AMMA SAIDAI KASH BACCI YACI ƘARFIN IDONA YANZU 12:26 p.m SO KUMUN AFUWA SAI ZUWA SAFIYA DANJIN NEXT PAGE MUJAHEEDAH TAURARUWAR ROYAL_°°°°°

 

 

 

 

 

 

 

_BASEERATA ITACE ARZIKINA

 

 

 

 

 

 

WhatsApp number 07064904617 or call number 07031012948

 

 

 

 

 

 

*BAƘIN KISHI!! “PAID BOOK #200 ONLY*

 

 

FREE 🅿️ 3/4

 

 

 

 

 

 

 

A fusace ta shigo gidan har tana tuntuɓe idan ta sunrufe saboda tsabar fushi…

 

 

 

Ɗagowa Za’i’d yayi harya buɗe baki zai kirata Amma ina harta shige cikin gidan bakan bakan,

 

Girgiza kai yayi A fili ya furta “Anur Zafin fushi ga Zuciya ko dawa take A yau ɗin kuma,”?

 

 

 

 

 

 

Shigowa su Najwa da Amal da Afan sai salman dake ta faman faɗa yana kunfar baki, Sukuwa dik sunwani sumi sumi suna tafiya,

 

 

 

 

 

Girgiza kai Za’i’d ya sakeyi Yace,” Wannan gidan namu Akwai gwara cikin sa”,

Ɗaga musu hannu yayi batare da yayi magana ba Alamar dikansu suzo nan,

 

 

 

 

Najwa Tace,” Shikenan munshiga uku wllh Anur halinta A kwai gyara mukam munshiga ukunmu ga wannan baƙin mugun bayan mu gawani gaban mu,” kamar tayi kuka take maganar…

 

 

 

 

 

 

Amal Tace,” baku ne kuke wani biyeta ba ni wllh daidai nake da ita,”

 

 

 

 

 

 

 

Ƙarasowa wurinshi sukayi suka ɗan duƙa ƙasa,

 

 

Salman ya zauna kusa dashi,

 

 

 

Za’i’d Yace,” me kuma ke faruwa yau ma faɗan suka sakeyi ko,”?

 

 

 

 

 

 

Salman Yace,” ni inama nasani koda naje ɗauko su ita waccan mai *BAƘIN KISHI!!!* Harta tako ƙasa fa tadawo,”

 

 

 

 

 

Saida yaɗan ƙurɓa lemunsa hankalinsa kwance still idanuwan sa nakan jaridar Yace,” Ni Abunda yafaru nake son sani,”

 

 

 

 

 

 

Salman Yace,” Affan faɗama yaya Abunda Akayi,”

 

 

 

 

Affan ƙarami ne dika shekarunsa 11 ne Amma yanada shegen wayo ga surutu hakan yasa Za’i’d ya dage Akan saidai A kaisu makaranta ɗaya dan shine ƙaɗai zai riƙa bashi rahoto Abunda suke..

 

 

 

 

Affan Yace,” Uncle wai da Aunty baba da ƙarama sukayi faɗa da wata, Aunty Annur Tace ita bazata haɗa ƙawa da kowa ba shine ƙawar tace wai Aunty Amal takeso to sai sukayi faɗa har jiwa Aunty Annur sukayi ga Hannu jini yafito Uncle maths ne yada keta yace wai ita *BAƘIN KISHI!!* ne da ita,”

 

 

 

 

 

 

 

Salman Yace,” kagani ko wllh ina tsoron halin *BAƘI KISHIN NAN NA ANNUR* Kowa yasa narma da Abu ɗaya A kan me,”?

 

 

 

 

 

Ɗaure fuska Za’i’d Yace,” wato harkuna ƙarfin faɗa ko,? to tinda hakane kai Affan jeka kira Annur kace tazo yanzu kona sameta can natatta kata,”

 

 

 

Dagudu Affan yayi ciki…… …..

 

 

 

 

 

 

 

00 ONLY*

 

 

FREE 🅿️ 7/8

 

 

 

 

 

 

 

*WACECE ANNUR?*

 

 

 

Annur kyakykyawa ce ta gaban kwatacce tana da yalwataccen gashi har gadon bayanta ya sauka, baƙi ne silik tsantsi tsawo.

 

Tanada ƙaramin baki lips ɗinta jane kamar tashafa janbaki tana da manyan ido wato golding eye’s da zara zaran eyelashes, Farace sol Amma farin maija ne, duguwa ce baso sai ba,

 

Tintana ƙaramar yarinya kyanta yake A bayyane,.

 

 

 

Annur tana da wani masifaffen kishi wanda idan ya motsa ita kanta bata iya controlling kanta , Su biyu ne kawai ƙaɗai ƴaƴan Alhaji Salisu Annur itace Babba sai ƙanenta Affan…

 

 

 

 

 

Tin tana shekara 5 Iyayensu sukayi hatsari A take suka rasu saka makon ƙatuwar motar da tabin kan motarsu,

 

 

 

 

Annur taci kuka sosai kamar bazata daina har kwanci A hosbital tayi A lokacin Affan baifi shekara 1 ɗaya,

Abban Za’i’d ya maidasu gurinshi dan shine babban yayan Mahaifinsu. Tinda tazo gidan bata wani sakewa kullum cikin kuka take Najwa ce ma take rarrashinta dan tana mugun tausayinta,

A lokacin Za’i’d baya 9jar yana Estan bool gurin karatunsa na lafiya.

 

 

 

 

 

*WAYE ZA’I’D?????*

 

 

 

Za’i’d Shine ɗan yayan Mahaifin Annur, mutum ne shi mai matiƙar haƙuri da tausayi wannan dalilin yasa ya fara karatun lafiya, Tinkan yaje yake masifar son Annur dan yarinya ce maishiga rai gashi tana ƴar Mahaifinsa, Baban ta yasan da hakan tinkan yaje Yace,” ko bayan ransa Yabawa Za’i’d Annur, Sunada shaƙuwa sosai da ita, Daya sami labarin mutuwar Iyayenta baƙaramin tashin hankali yashiga ba, tinda lokacin yaƙara sawa ransa shine kawai zai iya Auran Annur batare da tayi maraiciba, Alhaji Misbah yana da mata ɗaya hajiya Maryam macce mai matuƙar haƙuri da kawaici wanda halinta ne ɗanta Za’i’d yaɗauka Sunada yara 3.. Za’i’d Shine babba ya nada ƙanne 3 Amal salman Husna, Sunsami tarbiya sosai dai dai iyawar iyayen nasu….

 

 

 

 

 

 

*MUNDAWO LABARIN*

 

 

 

 

 

Da ƙyar Najwa tasamu Annur ta haƙuri,

 

 

 

Shiga ɗakin Mamy tayi tasa meta kwance kan cinyar Najwa tana lallashi,

 

 

 

Mamy Tace,” Haba my Annur? saboda salim yamiki maganar kishiya shine zaki shiga damuwa haka? Kinga barshi Wasa yake miki kece kawai Mijinki zai Aura bawata kishiya da zai miki, Ai kesan Uncle ɗinki Za’i’d baya da ra’ayin mata 2 ko,”?

 

 

 

 

 

 

Jinjina kai tayi Alamar eh

 

 

 

 

” to meye Abun damuwa maza tashi kishare hawayenki kafin Uncle ɗinki yazo tinɗa Yake jiranki kuje shopping kinsan saura bikin naku yakusa ko,”?

 

 

 

 

 

 

 

Rufe idanta tayi wai taji kunyar mamy..

 

 

 

 

 

Mamy dariya take tabar palourn Amma Aranta tana fatan Allah yasa idan suka gaggauta ɗaura Auran tadaina wannan *BAƘIN KISHIN* nata.

 

 

 

Close Menu