Ashe Dangin Juna Muke Hausa Novel Complete
ASHE DANGIN JUNA MUKE?
Written by
Ummusultan….,
ELEGANT ONLINE WRITER’S
Bismillahi rahamani rahim!!!
Page 1-2
Free book
______________Cikin sauri ta ke tafiya, kaman za ta tashi sama har ta na haÉ—awa da gudu, ba ta ankara ba sai ji ta yi an hankaÉ—ata baya tare da dauke ta da wani irin lafiyayyen mari, “wai gaki mara kunya ko? shine jiya har da zagina a dandali kuma har da jifa na har ki ka fasawa saurayi na Ashiru baki ko??”
“Yanzu sai ki gaya min uban da zai karÉ“e ki a hannu na” ita dai Ladidi ba ta ce ma ta komai ba sai ma tunani da ta fara ta ina zata fara kwatar kanta agun wannan mai siffan samudawa.
Dan ta san idan ta rike wallahi sai dai wata ba ita ba, dan ba sa’ar yin ta bace dama irin wannan rikicin idan ta É—akko Baba ke shige mata ya basu hakuri ya ce “kunsan marainiya”. da haka ya ke rufe bakin mutane ga shi yanzu yana kasuwa.
Surkulle Hausa Novel Complete
Ban da Ƙirar samudawan da Allah ya yi mata ga ta baÆ™a kirin ga muni ba’a magana, baÆ™in ta har wani shining ya ke yi, har ta buÉ—e baki za ta bata hakuri, sai wani dabara ya faÉ—o mata tana ja da baya baya sai da suka samu dan ta zara a tsakani su, a hankali ta ware laidan tattasan da ke hannunta, ta watsa ma ta a ido, Larai ta Æ™wala wani uban ihu ta ce “wayyo ido jama’a taimako ido zai fita.”
Ta na samu ta sake ta ta kwashe mata kafa ji kake rub!!!, Larai ta faÉ—i, ta ko samu ta hau ruwan cikinta, duka da yakushi har da cizo, azabar tayi wa Larai yawa ta dinga ihu ta neman taimako, kan kace kwabo guri ya cika da yara sai ihu suke suna cewa sai Ladidi, ita ko sai wani huci ta ke yi kaman wata kububuwa.
Gashi har yanzu babu wanda ya kawowa Larai, dauki saboda tsananin addabar da ta yi wa yara kai har ma da manya ba ta bar su ba.
Ita ko Ladidi, hamdala ta yi ta godewa Allah daya bata nasara a kan Larai, dan ba karfen ta ya kwace ta ba ta san daga yau yara zasu ƙara jin tsoron ta saboda dukkan da ta yi wa Larai, kama hanya ta yi tafiyar ta zuwa gida hankali kwance, ta bar Larai, kwance wajen.
Dama aiken ta Inna yelwa tayi, shi ne Larai ta tare ta a hanya. ta na ciki tafiya taga Hafsi na tallan gyada dafefe, “ke zonan ta ce ma ta bani gyada ta Murtala ki je gidan mu sai ki ce a baki kuÉ—in naci gyadan Murtala”. “kai Ladidi jiya ma fa haka kike min dan Allah kar ki dauka wallahi Innata buguna za ta yi”. “ke ni dallacen kimin shiru kawai da naci gyadan Murtala shine zaki sani gaba ki na min kuka kaman wanda na dake ki”. “Dole nayi kuka kema kisan irin dukkan da Inna ta ke min ko biyar na É“atar balle yau har Murtala, kashe ni za ta yi kawai”. “Ke! ni dallacan rufemin baki kiyiwa mutane shiru akan gyaÉ—an Murtala ce zaki tsaya kina min kukan jin dadin,to kije ni dai bazan biya kudin ba, gyaÉ—an ce dai na ci ta.in yaso in kije gida Innar ta ki,ta kashe ki.”.
Cikin shashaÆ™ar kuka Hafsi ta ce,” ki taimaka kibani kudin wallahi Innata baza ta barni ba,jiya ma sai da dakeni akan gyaÉ—an da kika ci.” tausayin tane ya kama Ladidi ta ce “na ji zan biya ki,amma ba yau ba.” kuka Hafsi ta sake fashewa da shi kamar wace aka ce mata Innarta ta rasu,”ke! tsaya ni ki dai na cika min kunne idan kuma baki tsaya da kukan haka ba, bazan biya ba.”da s’auri ta share hawayenta tana cewa “na daina yi hakuri..” dan tasan halin Ladidi tana iya chanza ra’ayi yanzu nan tunani ta shiga yi ina zata samu kudin biyan gyaÉ—an, can saki wani irin murmushi ta ce” yauwa na samo mafita game da yadda za’a samo gyadar, biyo ni muje ta wajen gidan Babansu Ado, kanensa suna talan gyaÉ—a i’dan mukaje zan ja su faÉ—a i’dan suka yo kaina ke kuma sai kije ki dauki gyaÉ—ar Murtalan ki.ki bar wajen.”
“Kai Ladidi i’dan wani ya ganmu fa?.”
“Yo! shikenan sai ki je ki gaya wa Innarki naci gyadar dan bani da kuÉ—in biya.”
Da s’auri Hafsi ta ce “a’a wallahi zanyi muje toh.” “kin taimaki kanki.”
Suna zuwa ta jasu da faÉ—a su kayo kanta, gabaki-daya ita ko Hafsi da take gefe take ta dau gyaÉ—ar Murtalan ta tabar wajen cikin Sa’a kuwa ba wanda ya ganta ta yi tafiyar ta gida kai wa Inna Abu gyadarta ita ko Ladidi ta gani ta É—auka ta fi ita ta kama hanyar gida dan kai wa Inna Yelwa saÆ™onta. su kuma abokan fadan nata cewa suke tsoro ta ji ta gudu,ba su san É—anyan aikin data musu ba.
*********** ******* *********
Zaune ya ke a wani katafaren Office dake hawa na Uku a cikin Company. kai da ka ga tsarin wajen zaka san ba Æ™aramin Company ba ne, wanda suke aikin gine-gine dan ba Æ™aramin contract suke samu ba shiyasa indai kana son aiki da su, to dole sai ka zama jajirtacce dan shugaban kamfanin ba ya son wasa ko kaÉ—an. daga nan har China ya na aiki da su, sometime ma su zana maka kawai zasu yi In yaso sai ka ne masu yi maka aikin, musamman idan suna aikin gomnati.sun samu lambobin yabo da dama dan sun yi fice har akwai kasashe da suke Æ™oÆ™arin buÉ—e rashin su a nan ma. baturai da larabawa duk ba’a bar su baya ba suna hulÉ—a da ARMAN CONSTRUCTION COMPANY.
rubutu yayi a yan Æ™aramar takarda sannan ya mikawa messenger da ke tsaye a gun, karban yayi sannan ya duba me Oga ya rubuta ciki. bayan ya duba ya ce”okay Sir.”domin yasan ba bayani zai masa ba. ganin an rubuta sactetary daga saman t’note din yasa ya fahimci shi za’a kaiwa t’note din.
Zuwa messenger yayi ya miÆ™a wa Sactetary karÉ“a yayi tare da dubawa “bana son damuwa.”shine abin da aka rubuta, a jiyewa yayi sannan ya É—ana wani bottom wani slide doors mai É—an duhu ya rufe glass door É—in gaba-daya.wata irin Æ™ofar ce wanda kai da kake ciki zaka ga duk abinda ke faruwa a waje, amma na waje shi baya i’ya gani sai dai ya yi ta kallon zane zane Gidaje,Asibitoci, da kuma Wanda zai sa ka shagala wajen kallon wannan zane zane.
Tashi yayi daga kujerar da yake z’aune ya koma resting room na shi dake cikin Office din,É—akin ya tsaru i’ya tsaruwa sosai ba zama ka ce a cikin Office din ya ke ba samun guri ya yi a É—aya daga cikin kujerun da ke gefen wani makeken table wace ke É—auke da computer guda 24 an yi connecting É—in su da Cctv Camera da ke gaba-ki-daya Company.
Gefen table É—in manya manyan takardun zane-zane bayan ya zauna ya dauki Coffee da ya haÉ—o wa kansa ya fara sha a hankali ya ke sipping din i’danunsa a kan Cctv potage É—in ya kallon duk abubuwan da ke gudana a cikin Company.
Kiran wayan da aka yi hakan ya sa ya maida hankalisa kan neman wayar tare da neman inda ya ajiye ta har ta katse bai ɗauka ba a karo na biyu aka sake kira bai kula ba balle a saran zai ɗauka har ta katse, sai da aka masa wajen kira biyar sannan a na karshen ya juya zai ɗauka sai ya tuna a she ma bai shigo da wayar ba.hakan yasa shi jan dan ƙaramin tsaki,ya tashi ya fara tafiya cike da izza da nu na isa, hakan na nuna allamun lafiya a tatare da shi.
Ya bude kofar ya shiga cikin Office, Masha Allah ba karamin tsaruwa ya yi ba, sannan ga shi babban da shi, komai na ciki kuma baki da fari ne. ya na mai ɗauke da manya manyan zane wanda a ka yi frame na su aka maƙale su jikin garun (Bango) Office ɗin.