Ad Code

Akan Kudi Hausa Novel Complete

Akan Kudi Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

AKANKUDI

 

(A poor lady story)

 

…. 28th March, 2023

 

sherntee Ghayu

 

 

🅿……… *001*

 

 

*KATSINA*

 

“Ummah Kinga wallahi harna gaji da jiranta ace Idan mutum ya shiga d’aki kamar bokanya” Ummah dake zaune gefen wannan kyakkyawar Budurwar da bazata wuce 17 a shekaru ba tace “hmm Maryam Kenan ai duk Kece kika sangarta ta dayawa ace kullum sekin biyo mata” Ummah ta k’arashe tana tana kallon a gogon y’ar k’aramar keypad din hannunta ta cigaba da cewa “ai gashinan takwas din harta wuce” kyakkyawar Budurwar da aka Kira da Maryam tayi murmushi tace “Ummahmu Kenan ai yanzu zakiga ta fito” ko rufe baki batai ba Sega wata kyakkyawa kuma farar budurwa ta fito fuskarta fayau Babu ko powder natural beautyn ta ya fito tabbas da ace ba’a 9ja naganta ba danace wannan anyi kyakkyawar balarabiya irin quraish dinnan lol.

 

Gidan Marayu Hausa Novel Complete

Tanata kiciniyar saka face mask tace “Maryam taso mu tafi kar muyi latti” Ummah tace ” *SARAUTA* kofa karyawa bakiyi ba” kyakkyawar Budurwar da aka Kira da sarauta tace “Ummah na k’oshi sena dawo, wai meyasa yau bakiyi waina ba” Ummah na mik’amata kud’in makaranta tace “yau sunan y’ar gidan Badiyya inason naje ne shiyasa” sarauta tace “to kijira Idan na dawo sena rakaki zanje mu muntafi ayi mana addua” Maryam ta amshe dacewa “se mun dawo” Ummah tabisu da addua Har suka tafi.

 

Highlights college

Anan suke karatu Sanda sukaje anata taron latti dole suka tsaya suka amshi hukuncinsu sannan suka wuce class.

 

At 10:20am

Gaba d’aya d’aliban suna waje sunata wasansu inka cire wasu Daga cikin SS3 students suna zaune class suna fira, su hud’u ne Akan teburin hira suke sosai suna shewa inka cire sarauta dake gefensu tana zane. Acikin firar tasune d’aya ke cewa “amm Yawwa spincy dan Allah kinsiya wannan littatafin” spincy tace “na siya harma na Gama karantawa” da sauri zeena tace “tsakanin da Allah wayyo dan Allah kiban labari wallahi tunda na gama free pages ban kuma ba” Maryam tace “wai wane littatafin?” meelarge tace “auren wata Tara mana” Maryam tace “Kai Nima inason littafin wallahi marubuciyar tasan sirrin love dana rubutun littafi wai ya aka k’are ne tsakanin MD da XAHRA” meelarge tace “Aini Dama Bana siyan littafi sedai na jira na bati dan Allah spincy Idan kinje gida ki turomin” spincy tayi kicin² da rai tace “Allah ya sawak’e insai littafi infitar dashi kinma ja wallahi tunda na gama gogeshima zanyi” Maryam tace “kudai kuka sani nidai fad’amin complete sunan littafin naje na nema” Zeena tace “gaskiyarki Maryam Nasir” Spincy tace ” *AUREN WATA TARA WRITING BY HAJARA L SADEEQ MISS HAJJO*” Meelarge tace “Aina Allah base k’arewa seme dan baki turomin ba a banza zanga Yana yawo a group” Spincy tace “oho Dai aje aita karanta littafin Allah ya isa” “mttsswww” dogon tsakin dasukaji ne yasasu juyawa su kalleta tsakin ta k’arayi kafin tace “Allah dai ya kyauta muku madadin ku zauna kuyi tunani Akan yanda zakuyi suna ko kuma kunemi na kanku shine zaku zauna kuna firar banza da wofi” Zeena tace “hmm *MARYAM SARAUTA* Kenan ai gwara mu zauna muyi firar banza da wofi Akan mu zauna muyi tunanin dakike magana akai mufa matane harmu mutu rik’on mu ake Daga iyayenmu Zuwa mazajenmu daga mazajenmu Zuwa y’ay’a yenmu to Akan me zamu zauna mu b’ata lokacin mu ” meelarge tace” gaskiyarki yar uwa” Sarauta tace “Aiko kunji haushi niko kunganni nan neman kud’i se inda k’arfina ya k’are kenifa *AKAN KUDI* ba abunda bazan ba raina ne kurum da bazan bayar ba” kafin wani yayi magana sukaji ringing bell alamar andawo aji daga haka kowa ya wuce mazauninshi Haka aka cigaba da darasi har lokacin tashi yayi.

Kallon Sarauta Maryam tayi tace “yakamata mu tsaida napep mu tai ko” Sarauta tace “haba Maryam nan da d’aki Tara shine Zaki wani ce muhau napep Dan Allah ki koyi economizing rayuwa haba ni band nawa kud’in inyaso kekin hau napep din Ohk” ta k’arashe tana mik’ama Maryam hannu Maryam tace “yanzu Sarauta abunda kikeyi kin kyauta Kenan ke kullum bakida abunda ke faranta Miki se kud’i kin fifita kud’i Akan kowa kin maidani kamar ba k’awarki ba wallahi kiji tsoron Allah kud’i fa halaka ne ashe duk fad’an da Ummahmu take Miki a banza” Sarauta tayi murmushi tace “hmm Maryam Kenan kud’i ba halaka bane kyauta ce kuma baiwace tadaban da Allah keyiwa bayinshi ni bance Miki keba k’awata bace kuma bance fad’an Ummah yatashi abanza ba but am sorry to say gaskiya kud’i sunfimin komai kizo mutafi” ta k’arashe tana tafiya wannan ba sabon Abu bane agurin Maryam Tasha sanar da ita kud’i sun fita a gurinta so bazatayi mamaki ba shiyasa kawai tabita suka tafi.

A gajiye taje gida, ta tarar da Ummah harta shirya sedai me cemata tayi taje kurum ita tagaji Babu inda zata, dama Ummah ta tsammaci hakan shiyasa kurum tayi tafiyar ta.

 

 

 

*JIDDA*

 

*The emir palace*

 

 

Ajere motocin suka shigo masarautar a hankali suke tafiya harsu kayi parking da sauri escorts din suka fito tare da bud’emai k’ofar a hankali yasoma fitowa daga motar kafin kuma gaba d’aya ya bayyana (hasbunallahu wani’emal wakeel tsarki ya tabbata GA mahaliccin wannan halintar) saurayine da baze wuce 29 a shekaru ba Yana sanye cikin k’ananan kaya inda ya d’ora alkyabbarshi me adon zinari a sama gashin kanshi ya sauko har gurin wuya ta b’angaren Dama kyawawan red lips dinshi su suka k’ara k’awata fuskarshi eyesbolls dinshi bak’i wuluk yariman nan dai ya had’u ta ko Ina ga kyakkyawar k’ira da rabbi yayi mishi tafiya yake in a classic way harya k’arasa wani kyakkyawan building daya gama haduwa tundaga yanayin building d’in kasan cikinshi zeyi kyau da dad’in kallo Haka kuwa akai Kai tsaye yashiga cikin k’ayataccen palourn komai yaji ba’a magana a hankali yasoma hawa upstairs d’in d’aki d’aya ya bud’ e Acikin jerin d’akunan wani kyakkyawa kuma farin dattijo nagani Wanda daka kalli fuskarsa zaka hango dattijon taka da mutuntawa *SARKI LADTEEF* Kenan sarki masarautar jidda murmushi yayi tare da mik’ewa cikin nuna murna da k’auna yace “you’re welcome my darling son” shima rungumeshi yayi tare da shagwab’e fuska kamar k’aramin yaro cikin lafiyayyen larabcinshi yace “ai Nayi fushi bakaje d’aukoni Airport ba koma murnar zuwana bakuyi ba” kyakkyawar matar dake tsaye gaban mirror tana murmushi tace “my baby boy Kadai k’i girma ko” kallonta yayi yace “Ummi Kenan aina gode hardake ko” kusa dashi ta dawo tana zama tace “Tohm munji we’re sorry Ohk koba Haka ba JARUMINA” ta k’arashe tana kallon sarki murmushi sarkin yayi yace “hakane mana ayi mana afuwa” saman kafad’arta ya kwantar da kanshi tare dacewa “badan halinku ba anyafe” duk dariya sukayi Ummi ta mik’e tasama me martaba alkyabbarshi tare da fesheshi da turare “Abieyna seka dawo” Abiey yace “Tohm Abiey’s boy sena dawo” harya fita yadawo yace ” *MUHAMMAD SHUREIM*” dasauri ya juyo yace “Na’ammmm” Abiey yace “kome kakeyi karka bari yau ta wuce bakaje Ka gaida su Neenah ba kaji ko” Muhammad Shureim yace “in sha Allah Abiey” daga Haka Abiey ya fice kallon Umminshi yayi yace “meyasa Abieyna yake hakane Sarai fa yasan halin mutanen nan amma shi yafi son ayita wulak’antani” Ummi tazauna gefenshi tare da d’ora hannunta a saman kafad’aeshi tace “kayi hak’uri my son mahak’urci nawadaci wata rana se labari kaje kugaisa kaji Aidai bazasu cinye namanka d’anye ba ko” Kai ya d’aga mata tace “good boy Shureim” murmushi yayi yace “Humm Ummi Bari naje b’angaren *SHUBAI’A* tun kafin tasamu labarin dawowata tad’au fushi me dogon zango dani” Ummi murmushi kurum tayi tace “gaskiya Kam gwara kaje nasan dishes nasan an shirya maka” murmushi yake harya fice daga d’akin cike da shauk’i da d’okin ganin k’anwar tashi…………

 

 

Kar ku manta labarin *AKAN KUDI* k’irk’ irarren labarine danayishi domin nishad’antarwa dakuma fad’akarwa nice taku me nishad’antar daku a kullum da ko yaushe

 

@ *sherntee ghayu* 🥰🥰

 

Sak’on godeeya ta Zuwa gareku a bin alfaharina

~Miss hajjo

~mom Islam

~Daddy’s little girl

~zaituna

 

 

07064706167

Close Menu