Kungiyar Kwallon Kafa Ta Manchester United Ta Sayi Dan Wasa Casemiro Daga RealMadrid

 

Kungiyar Kwallon Kafa Ta Manchester United Ta Sayi Dan Wasa Casemiro Daga RealMadrid

CASEMIRO

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta amince da daukar dan wasan tsakiyar Real Madrid, Casemiro akan kudi fam miliyan 60, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 70.

Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Erik ten Hag ya dade yana neman samun dan wasan tsakiya tun lokacin da ya karbi ragamar horar da kungiyar, inda ya koma taya dan wasa  Casemiro bayan  da ya kasa siyan Frenkie de Jong na Barcelona.

An yi wa Casemiro tayin kwantiragin shekaru hudu tare da zabin karin shekara daya a yarjejeniyar da aka kulla.

Previous Post Next Post