Ad Code

Matsayin Maniyyi da Makamantansa


Bismillahirrahmanirrahim

MATSAYIN MANIYYI DA MAKAMANTANSA

WADIYYI :
wani irin farin ruwane Mai kauri wanda yake fitowa bayan gama fitsari. Malamai basuyi sabani akan kasancewarsa najasa ba. An ruwaito daga Aisha (r a) tace :

"shi wadiyyi yakan kasancewa ne bayan fitsari, sai mutum ya wanke zakarinsa da 'ya' yan marainansa kuma ya sake yin alwala amma bazaiyi wankan janaba ba. Ibn munzir ya ruwaito

Ankuma ruwaito daga d'an abbas (r a) dangane da lamarin MANIYYI, WADIYYI, WAZIYYI cewa :shi maniyyi anayi masa wankan janaba idan yafito amma maziyyi da wadiyyi ana cika musu tsarki ne "wato a wanke azzakari da sake alwala. Imam asram da baihaqi suka ruwaito.

MAZIYYI :Shi wani ruwane fari wanda yake sulalowa batareda sanin mutum ba a lokacin jima'i ko kuma a lokacin wasanni da mace, kuma yana fitowa maza da mata sai dai yafi yawan sulalowa mata. Malamai sunyi ittifaqi akan zamowarsa najasa, sai dai idan yataba jikin mutum ya wajaba a wanke shi.

Amma idan tufafinsa yataba sai a yayyafa masa ruwa, saboda kasancewar irin wannan najasar tanada wuyar kiyayewa domin yawan saduwarta ga tufafin samari (gwauraye) kuma wannan shi yafi dacewa da a sauqaqa akansa daga fitsarin yara qanana.

An ruwaito daga sayyidina aliyu (r a) yace :nakasance mutum Mai yawan fitarda maziyyi sai na umurci wani mutum ya tambayomin manzon Allah (s a w) ya matsayinsa a wurina? Da ya tambayeshi sai yace :kayi alwala ka wanke azzakarinka. Imam buhari ya ruwaito.

MANIYYI :wadansu daga cikin malamai suna ganin cewa maniyyi najasa ne, sai dai maganar da tafi rinjaye itace :maniyyi abu ne Mai tsarki. A naso a wanke maniyyi idan yana danye kuma a kankareshi idan yabushe.

Aisha (r a) tace :nakasance ina kankare maniyyi a tufafin manzon Allah (s a w), idan ya kasance busashshe, inkuma wanke shi idan yana danye. Imam Darul kudumi, Abu auwana da bazzar suka ruwaito.

An ruwaito daga dan abbas (r a) yace :an tambayi manzon Allah (s a w) dangane da tufafin da yasadu da maniyyi?

Sai yace :"matsayinsa daidai yake da kakin majina da yawun da aka tofar dashi, haqiqa ya isheka ka shafe shi da qyalle ko ganye. Imam Darul kuduni, baihaqi da dahawi suka ruwaito, sai dai anyi sabani acikinsa.
Close Menu