Garkuwa Ga Mata masu Ciki

 GARKUWA


GA MATA MASU CIKI._*

_Anaso mata masu ciki surika amfani da Alkamah, kwai, ridi, waken soya, karasa,dakuma zait zurra._

_Yana kara masu lafiya, kuma koda mace tana lafiya kalau zata iya amfani dasu zasu gyara mata jiki sosai._

_Ciwan gabbobi namasu ciki sai adinga tafasa Shair anasha damadara._

_Kuma anaso ayawaita cin karas ko shan mansa,daywan cin inabi, da gawasa,dakuma apple._

_Haka idan ana yawan cin yayan baure,da ayaba, tafarnuwa gyada, fasuliyya, to insha Allah idan kanacin wadannan itatuwan koda namiji ko mace to koda tsufa yazoma jikinka bazaiyi irin muguwar lalacewa dinnan ba insha Allah._

_Ko asamo Ganyan Naa Naa dagarin habbatisauda tarika tafasawa tanasha dazuma sau biyu arana, idan matsala tayi yawa sau uku arana._

_Idan Mace tanada karamin ciki kuma tana fama da matsaloli to zata iya tarika tafasa ganyan Naa Naa dakuma Khalil tuffa anasha to yana saukaka laulayin mata masu ciki insha Allah._

_Bayan haka tafasa ganyan Naa Naa dahabba dazuma anasha yana kara ma mata masu ciki lafiya da yayan dasuke acikin nasu insha Allah._

_Ko asamo man zaitun daman habbatisauda kowanne rabin lita ko lita dai dai masu kya sai adinga shan cokali daya tare dazuma kafin akarya haka darana haka dayamma kafin akwata. Zuwa wata shida, cokali bibiyu._

_Idan yakai wata Tara to cokali uku uku dasafe darana dayamma,haka itama zuman insha Allah zaa haihu lafiya._

:

```Allah ta'ala yasa mudace```


Previous Post Next Post