*MATI DA ASABE.*
Tafe yake bakin k`ok`arin shi yana jan `yar k`aramar tunkiyar shi daya siyo amma tana ta tittirje masa, cikin fasaha yaci gaba da tafiya da ita tun daga kasuwar har gidan su, akwai nisa sosai amma da hakan ya iso da ita cikin gida.
“Asabe! Asabe!!”
“Naam mai gida, ina ban d`aki gani nan zuwa”.
Wuri ya samu daga gefen tsakar gidan yayi ma tunkiyar tirke, dussa ya dama mata da ruwa ya bata har a lokacin Asabe bata fito ba.
“Gani mai gida”
Ta fad`a tana goge hannun ta a zanin ta.
Cikin murna yace “Asabe kinga tunkiyar dana siyo naira dubu goma sha d`aya da Alhaji Sani ya bani, tayi sauk`i ko?”
Fuskar ta d`aure tace “kar dai kace min da wannan tunkiyar ce zamuyi layya? Yanzu duk yanda nake ji mak`obta sun siyo *RAGON LAYYAH* sai nice zaka nufo da wata `yar tunkiyar wai muyi layya da ita? To wallai bazata sab`u ba! Ko sanda nake gidan mu rago ake yanka mana saboda haka nima dole rago zaka yanka min, idan ba *RAGON LAYYA* tou babu aure” ta k`arasa maganar tana kallon shi cikin raini.
“haba Asabe! Yanzu duk wannan talaucin da ake fama dashi ke bazaki duba hakan ba ki sauk`ak`a min? Wallahi nayi imani da da dama akwai inda bazasu samu yin layya ba, ai kamata yayi ki gode ma Allah da wannan tunkiyar dana siyo”.
“Nidai na fad`a maka kuma wallai sai dai ayi d`aya, ko aure ko *RAGON LAYYAH”.*
*NAINI DA SARATU.*
kwance yake a `yar k`aramar katifar su yayi tagumi daka ganshi zaka gane lallai yana cikin damuwa.
Saratu ce ta shigo cikin ladabi tace “Naini me yake damun ka ne wai kwana biyun nan duk kabi ka fice hayyacin ka? Kuma idan na tambaye ka kace min babu komai”,
Ajiyar zuciya yayi yana kallon ta yace “Saratu damuwar duniya ce kawai tayi min yawa, ga wannan talauci da yake addabar al`ummah, gashi kuma har yanzu ban tanadi ko tsuntsu ba bare *RAGON LAYYAH”.*
Saurin dad`e masa baki tayi tana fad`in “bana son jin haka daga bakin ka fa, me zaisa idan mutun bashi da abu kuma yace lallai sai yayi, dan Allah ka cirewa kanka wannan, ai layya ga wanda yake da halin yinta shine wajibi, kuma Allah yaga zuciyar ka kana da k`udurin yi wadata ce babu”.
“Hakane Saratu, shi yasa nake k`ara sonki a koda yaushe, kina tausayi na sosai, da ace duk mata haka suke da tausayi da maza sunji dad`i” ya k`arasa maganar yana mata murmushin soyayya.
*MATI DA ASABE.*
“Wallahi Mati kazo ka bani takarda ta idan ba haka ba baka ba sauran farin ciki a gidan nan, akan me duk shekara kafin in aure ka gidan mu sai an mana layyah kai kuma ka nufo ni da wata `yar tunkiya wai da ita zamuyi layyah? Wallahi bazata sab`u ba bindiga a ruwa”.
Banza Mati yayi da ita, bai ko tanka taba ya shige d`aki abin shi.
Har d`akin tabi shi tana fad`in “idan har ka haihu ga uwar ka da ubanka tou ka sake ni, wallahi bazan zauna dakai ba matsiyacin banza ka nufo ni da `yar tunkiya wai da sunan layyah, wannan ai abun kunya ne ma”,
Cike da takaici ya kalle ta yace “dole kuwa in nuna miki ni haifaffe ne uwa da uba, kije na sake ki saki D`aya”.
“Tafi nono fari” ta fad`a tare da fara had`a kayakin ta tana wata wak`a k`asa k`asa.
*Gidan su Asabe.*
Cike da kukan munafurci ta shiga gidan, a gaban mamanta ta duk`a, cikin fad`uwar gaba maman ta tace “ke Asabe lafiya dai? Me yasa kike kuka?”
“Mama Mati ne ya sake ni, wai kawai dan na sakar mashi tunkiya ta gudu ba dagangan ba, kuma ma fa ya gano ta a bayan layi, amma duk da haka sai da ya sake ni wai inbar masa gidan sa”.
Cikin b`acin rai maman tace “amma kuwa wannan yaro bai kyau ta ba, lallai kuwa dole zai fuskanci fushin mu”.
Abban ta ne ya fito yana fad`in “kibar shege, zaizo har nan yana neman mu miyar masa da ita amma muk`i”.
Cikin jin dad`in sun goyi bayan ta ta kwashi kayan ta ta nufi d`akin su dasu.
*Bayan sati d`aya.*
Zaune suke duka gidan suna hira ban da Abbah daya fita, sallamah yayi suka amsa cike da jin dad`i, bayan ya zauna mamah ta kawo masa ruwa yasha yace “tou bana dai babu kyau, abun babu dad`i wallahi”,
Asabe ce tayi saurin katse sa tace “Abbah inji dai ko lafiya?”
“Lafiya k`alau, amma fa babu kanta, duk inda nake sa ran zan samo kud`in *RAGON LAYYAH* naje amma ban samu ba, hasali ma kowa ta kan sa yake, bana sai dai mu dangana mu barwa Allah komai, dan sai dai kuji kamshin soye daga mak`ofta”.
Saurin mik`ewa Asabe tayi tace “na shiga uku! Anyi gudun gara an fad`a gidan zago, na guji tunkiya na dawo ma babu”,
Cikin rashin fahimta iyayen ta sukace “me kike nufi Asabe?”
Cikin kuka ta labarta masu komai, cike da nadama take kuka sosai, kuma tasan yanzu duk nacin ta Mati bazai mayar da ita ba, saboda zagin shi da tayi akan sai ya sake ta, wannan shi hausawa ke kira da biyu babu.
*Naini da Saratu.*
Kwance yake kamar kullun yana tunanin abunda zasu ci, Saratu nata kwakkwafar shi akan ya kwantar da hankalin shi ita batta jin yunwa. Sallamar da sukaji ce tasa Naini mik`ewa tare da zira jallabiyar shi, hanyar k`ofa ya nufa yana amsa sallamar.
“Ahh yallabai sannu da zuwa, kaine a gidan namu? Bismillah mu shiga daga ciki”
Har ciki suka shiga, bayan Saratu ta gaishe shi ta basu guri, “wato Naini ina nan rik`e da hallacin da kayi min a baya, shine nazo maka da `yar kyauta ta ina fatan zakaji dad`in ta”
Cike da farin ciki yace “Allah sarki! Wlh alhaji daka barshi ma, ni dan Allah na maka komai”,
“Nasani ai Naini, shi yasa nima nake son faranta maka kamar yanda kaima ka faranta min, *RAGON LAYYAH* ne nazo maka dashi da `yan kayan abinci”,
Sosai Naini yayi godiya, Alhajin ya bashi dubu goma sannan sukayi sallamah, bayan sun fita waje ya karb`i ragon da buhun shinkafa, taliya da sauran kayan abinci, har da yara suka taya shi kwasar su, cike da murna ya shigo yana jan shi yana kiran Saratu, sun sha farin ciki sosai Saratu tace “kaga irin ta ko Naini? Shi yasa idan kana damuwa nake nunar maka da Allah shine yake bayarwa, kuma shi zai wadata mu dashi dan shi kadai yasan halin da muke ciki, gashi kuwa lokaci d`aya mun samu *RAGON LAYYAH”*
*GIDAN SU ASABE.*
Abban Asabe ya aika an kira masa Mati, nan ya rok`e shi akan ya mayar da matar shi d`akin ta amma sam Mati yace bazai mayar da ita ba, saboda zagin sa da tayi.
The end!!!.
Ina fatan sak`on da nake son isarwa ya isa, inda nayi kuskure Allah gafarta min, inda nayi daidai kuma Allah ya bani ladar.
Duk kan yabo da godiya sun tabbata ga Allah mad`aukakin sarki, tsira da aminci su k`ara tabbata ga shugaban mu annabi muhammadu tare da alayen sa. Godiya ga d`aukacin masoyana maza da mata a duk inda kuke, nagode k`warai da nuna kulawar ku a gare ni, bani da abun saka maku face addu`ah. Kuyi hak`uri da rashin jin posting d`in *UMMU HAYDAR* kwana biyu, abubuwan ne sunyi yawa.
Jinjina ga k`ungiya mai albarka *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* Allah ya had`a kawunan mu ya kauda fitina a tsakanin mu,
*Ban manta daku ba,*
*Fikra writers association,*
*Excellent writers,*
*Clever writers,*
*Marubuta zallah,*
*Duniyar marubuta,*
*Galaxies hausa writers,*
*Writers world association*
*Best writers group*
*And other writer’s groups.*
*Nafee and Amrah novellas,*
*Amrah nd Rerbee’art sk novels,*
*Mu farka mata,*
*Amrah’s kitchen,*
*Saha’s novels,*
*General joint,*
*Aneelurv fans,*
*House of novella na kdeey,*
*Novels novella na Hanny,*
*Zarah bb fans,*
*Sadiya nd zarah bb novels,*
*Futuhatul khair novels,*
*Runbun Asiya Basheer,*
*Dandalin Lubee mai tafsir,*
*Taskar munay,*
*Queen mimi novels*
Da sauran wanda ban fad`a ba suna raina.
*Rabiatu sk msh and Zarah bb* bazan rufe ba dole sai na ambace ku, wo hohoooo my sisters, ina k`aunar ku forever and ever