Ad Code

Wata Mata A KANO Ta Babbaka Mijinta Da Ruwan Zafi

Mallam Aliyu Ibrahim Fayan-fayan malamin Makarantar furamare ne a Dambatta ya tsinci kansa ne Jiya da daddare da misalin karfe Goma da Rabi na dare alhamis Kawai sai ji matarsa ta kwara masa ruwan zafi a jikansa.

Mallam Aliyu Ibrahim ya shaida min cewa ya gayawa Matarsa cewa zai yi aure har ma ya bata kudade domin taje tayi siyayya irin kayan fadar kishiya to tun lokacin da na gaya mata basu sami matsala har take gayamin su zasu je su hado kayanma.

Jiya ma da zan taho Cikin garin Dambatta sai da ta bani siyayya nayo mata, na kaimata kayayyaki.
Ina kwance bayan Nagama jin taskar labarai to har na fita na siyo musu Nama suka ci dama na tarar da ita Tana dafa Ruwan zafi naje na kwanta Kawai sai naji ta kwara min Ruwan zafi. Har a Gabana kana gani Babu Wando ajikina Kuma bama samun sa-in-sa da ita kawai dai dan na ce zan yi ƙarin aure ne shiya sa.

Kuma Duk 'yan uwana sun San Zanyi aure amma har yanzu ban san inda take domin lokacin da abin Yafaru wani makwabci nane ya kawoni asibitin.

Kuma muna da 'Ya 'Ya Goma da ita
yanzu haka yana Asibitin Dambatta a kwance
Close Menu