Gardamar aure kan cin amanar juna ta kai wasu ma'aurata kotu inda suka nemi a kashe aurensu.
Matar mai suna Misis Edith Obieme ta roki wata kotu a birnin Legas na Najeriya ta kashe aurenta na shekara biyu da Mista Kingsley inda ta ce ta sha kama shi yana kwanciya da mata da dama a gadonta na aure.
Tun farko mijin ne ya shigar da kara inda ya bukaci kotun ta kashe aurensu saboda acewarsa matar ta sha barazanar halaka shi, zargin da ta musanta.
Matar ta nemi kotun ta kashe auren domin yadda mijin ke kwanciya da mata a gaban idonta.
"Ya taba kwanciya da 'yar aiki, ban taba cewa ina bukatar 'yar aiki ba, amma a ranar da na kama shi yana kwanciya da ita, a ranar ta kwashe kayanta ta bar gidan."
"Kingsley talaka ne, ba shi da ko kwabo, babu ribar da zan ci idan ma na kashe shi," kamar yadda kamfanin dillancin labaran kasar NAN, ya rawaito tana fada a kotu.
"Kawai na taba barazanar zan yi wa farkarsa wanka da ruwan guba (acid) idan har na sake kama shi yana lalata da matan banza, in ji Edith wacce 'yar kasuwa ce mai goyon yaro dan wata hudu.