Ad Code

An daura Aure a Facebook. Lamarin na son ya kawo hargitsi



'Yan Hisbah a jihar Kano da ke arewacin Najeriya suna neman wasu 'ma'aurata' bayan da suka daura aure a shafin Facebook.

Sanusi Abdullahi mai shekara 29 ya shaida wa BBC cewa wasa kawai yake da yarinyar bai san cewa karamar magana za ta zama babba ba.

"Tattaunawa muke yi a wani zauren Facebook da sauran mutane, kamar wasa sai yarinyar ta ce na aure ta ni kuma na ce to, bayan wani lokaci sai ta sake aiko min da sako ta ce ta samu wanda zai yi mata alwalanci, ni ma sai abokina ya ce zai yi min alwali.

"Sai muka amince da naira 20,000 a matsayin sadaki, daga nan sai abokina da alwalin nata suka gaya mana dukkan abin da ake bukata a aure."

Sanusi ya ce jim kadan da faruwar hakan sai mutane suka fara yada zancen cewa 'Sanusi ya yi aure' daga nan sai ya kira yarinyar ya ce mata wannan auren fa kamar ya dauru, bari mu tambayi malaman musulunci saboda mutane na ta cewa auren ya tabbata.

"Da muka kira sai wasu suka ce ai aure ya dauru tun da akwai shaidu kuma na yi alkawarin biyan sadaki, amma da na tuntubi Sheik Ibrahim Daurawa, wani babban malami sai ya ce aure bai dauru ba tun da iyayen yarinya ba su sani ba.

"Ya ce yaya za a yi aure ba tare da sanin iyayen yarinya ba."

Sanusi ya ce barci ya kauracewa idonsa tsawon kwana biyu tun bayan da labarin ya bayyana.

"Wannan abun na damuna ba kadan ba, yarinyar da nake so ta ce ba ta sona yanzu kuma iyayenta ma sun yi fushi, ita ma waccar yarinyar ta rasa saurayin da za ta aura nan da watanni kadan."

Mai magana da yawun Hukumar Shari'a ta Kano Sanusi Mohammed ya shaida wa BBC cewa tuni sun bai wa Hisbah umarnin kama matasan domin ya zama misali ga masu irin wannan auren wasa a kafafen sada zumunta."

"Abin da suka yi ya sabawa Musulunci, abu na gaba da za a yi bayan Hisbah ta kama su shi ne kai su kotu daga nan kuma alkali zai yanke hukuncin da ya dace da su.

"Shari'a ta tanadi hukunci ga kowane irin laifi."
Babban limamin Masallacin Abdullahi Abbas na Kano, Sheik Nazifi Inuwa ya shaida wa BBC cewa, yaya za a yi aure ya dauru bayan iyayen yarinya ba su sani ba.
"Manzon Allah SAW ya ce mace mai zaman kanta ce kawai za ta iya aurar da kanta, don haka aure tsarkakke irin na musulunci ba haka yake ba."
Sanusi ya ce tuni ya gudu daga gidansu saboda lamarin.

"Na ji labarin cewa Hisbah na nema na don a kama ni amma ina tattaunawa da iyayena kan ko na kai kaina gare su.

"Amma abin da nake so mutane su gane shi ne abun da ya farun kuskure ne kuma na ba da hakuri.

"Ban taba shiga masallaci don halartar daurin aure ba a rayuwata don haka ban san yadda abin yake ba, kuma na yi alkawari ba zan sake aikata irin haka ba."

http://hausar.blogspot.com
Close Menu